Wanda Ya Jagoranci Kafa APC Ya Kawo Yadda za a Ruguza Jam'iyyar a 2027
- Jagoran jam’iyyar ADC a Najeriya, John Odigie-Oyegun, ya ce hadin gwiwar ADC da Obidient Movement zai kawo sauyin mulki a zaben 2027
- Rahotanni sun nuna cewa ya bayyana hakan ne a Benin yayin shigowar dimbin mambobin Obidient Movement cikin ADC a Jihar Edo
- Cif John Odigie-Oyegun na cikin wadanda suka suka jagoranci kafa jam'iyyar APC a lokacin hadaka da marigayi shugaba Muhammadu Buhari
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo – Wani babban jigo a jam’iyyar ADC, Cif John Odigie-Oyegun, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa hadin gwiwar jam’iyyarsa da Obidient Movement zai kawar da jam’iyyar APC daga mulki a zaben shekarar 2027.
Odigie-Oyegun, wanda ya taba rike mukamin shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya fadi hakan ne yayin da dubban mambobin Obidient Movement suka fice daga tsohuwar jam’iyyarsu suka shiga ADC a Jihar Edo.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa lamarin na zuwa ne makonni kadan bayan tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya sanar da shiga jam’iyyar ADC.
John Oyegun ya ce za a ruguza APC
Da yake maraba da mambobin Obidient Movement, Odigie-Oyegun ya ce shigowarsu jam’iyyar na nuni da cewa ‘yan Najeriya, musamman matasa, sun shirya daukar nauyin fafutukar kawo sabon shugabanci a kasar nan.
Odigie-Oyegun ya ce karfin matasa da kishin kasa da yake gani tattare da 'yan Obidient Movement ya bambanta da duk abin da ya taba gani a baya a harkar siyasa.
A kan haka ya ce hada karfi da karfe tsakanin ADC da 'yan Obidient Movement zai taimaka wajen fatattakar APC mai mulki a Najeriya.
Rawar matasa a sauyin siyasar Najeriya
A cewarsa, wannan ne karon farko da yake ganin matasa masu cike da kudurin gina kasa ba tare da dogaro da tsofaffin dabarun siyasa ba.
Vanguard ta rahoto ya ce shigowar Obidient Movement cikin ADC ba kuskure ba ne, ya ce hakan mataki na karbar ragamar fafutukar sauyi da kansu.

Source: Facebook
Odigie-Oyegun ya kara da cewa tun daga ranar da aka kafa hadakar 'yan adawa, ya tabbatar a zuciyarsa cewa ADC na tafiya a kan sahihiyar hanya.
Oyegun ya ce za a ceto kasa daga APC
Jagoran ADC ya jaddada cewa halin da Najeriya da Jihar Edo ke ciki a yanzu ya kamata ya zama abin da zai hada kan jama’a wajen daukar matakin ceto kasa.
Ya ce burinsu daya ne kawai, wato ceton Najeriya daga halin da take ciki na mulkin APC, tare da tabbatar da cewa ta hanyar ADC, za samar da sabuwar Najeriya.
A nasa bangaren, shugaban Obidient Movement a Jihar Edo, Asemota Idiogbe, ya ce ADC ce jam’iyyar da ta fi dacewa wajen kalubalantar APC a Edo da kuma a matakin kasa.
'APC za ta fadi a 2027,' Olawepo-Hashim
A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon mai neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Gbenga Olawepo-Hashim ya ce APC za ta fadi a 2027.
Olawepo-Hashim ya ce duk dabarun da gwamnatin APC ke yi na raunana 'yan adawa ba za su yi nasara ba lura da tarihin siyasar Najeriya.
'Dan siyasar ya yi kira ga 'yan Najeriya da sauran 'yan kasashen waje da su saka ido kan yadda zaben kasar zai kasance domin tabbatar da adalci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


