An Gama Magana: Shugaba Tinubu Ya Sharewa Gwamnan Kano Fagen Shiga APC
- Bayanai na kara fitowa kan abubuwan da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tattauna da Gwamna Abba Kabur Yusuf na jihar Kano
- Da yammacin jiya Litinin ne, Gwamna Abba ya gana da Shugaba Tinubu yayin da ake tsaka da rade-radin zai sauya sheka zuwa APC
- Rahotanni daga fadar shugaban kasa sun ce Tinubu ya karfafawa Abba gwiwa, kuma ya warware duk matsalolin da suka jawo jinkirin shigarsa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Alamu sun nuna cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shirya tsaf domin sauya sheka daga NNPP zuwa APC bayan ganawarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wannan ganawa ta zo ne a daidai lokacin da jita-jitar sauya shekar Abba ta mamaye siyasar Kano, lamarin da ya janyo rashin jituwa tsakaninsa da ubangidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Source: Twitter
Tinubu ya sharewa Abba fagen shiga APC
Majiyoyi da dama da ke da masaniya kan ganawar sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa, tattaunawar ta warware muhimman matsalolin siyasa da suka dakatar da shirin sauya shekar gwamnan a baya.
Sun ce Shugaba Tinubu ya sharewa Gwamna Abba fagen shiga APC a hukumance nan da yan kwanaki kadan.
A cewar majiyoyin, gwamnan ya 'dan jinkirta ne saboda rashin tabbas kan makomar siyasarsa a APC, musamman batun takara a 2027, makomar tsarin siyasarsa, da kuma magoya bayansa a cikin sabuwar jam’iyyar.
Abin da Tinubu ya tattauna da Abba
Wadannan batutuwa, a cewar majiyar, an tattauna su kuma an shawo kansu a ganawar da Gwamna Abba ya yi da Shugaba Tinubu ranar Litinin, 19 ga watan Janairu, 2026, in ji The Nation.
Wata majiya ta ce:
“Yana iya sanar da komawarsa a hukumance gobe (Talata) ko jibi domin an riga an gama komai. Shugaban kasa yana son ganinsa a APC, shi ma gwamnan yana son tafiya tare da shugaban kasar.”
Kalmar da Abba ya fada a Aso Rock
Bayanai sun nuna cewa Gwamna Aba Kabir Yusuf ya ki yarda ya yi magana da manema labarai bayan fitowa daga ofishin shugaban kasa, inda kawai ya ce, “zan dawo.”
Rahotanni sun nuna cewa ganawar ta dauki tsawon kusan sa’o’i uku, inda aka ce Abba ya isa ne da misalin karfe 4:10 na yamma, sanye da babbar riga fara da jan hula, sannan ya bar wurin mintuna kadan bayan karfe 7:00 na dare.

Source: Twitter
Majiyoyi sun ce shugaban kasa ya tabbatar wa Abba Gida-Gida da kansa cewa za a daraja shi a APC, musamman a Kano da kuma yankin Arewa maso Yamma, inda jam'iyyar ta rasa kujeru da dama a zaben 2023.
Abubuwan da Abba ya fadawa Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi ganawar sirri da Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin tattauna muhimman batutuwan tsaro da ci gaban jiharsa.
Ganawar ta mayar da hankali ne kan kalubalen tsaro, manyan ayyukan more rayuwa da kuma yadda Kano za ta kara amfana daga shirye-shiryen gwamnatin tarayya.
A yayin ganawar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar wa Shugaba Tinubu da cikakken bayani kan halin tsaro a wasu sassan Jihar Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


