APC Ta Sace Gwiwar Gwamnonin da ke Tururuwar Sauye Sheka gabanin Zaben 2027

APC Ta Sace Gwiwar Gwamnonin da ke Tururuwar Sauye Sheka gabanin Zaben 2027

  • APC ta bayyana cewa sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ba ya nufin za a bayar da tikitin takara kai tsaye ga gwamnonin da suka shigo
  • Jam’iyyar ta jaddada cewa tsarin APC na dimokuraɗiyya ne, inda kowa zai fafata domin samun tikitin tsaya wa takarar kowacce kujera
  • Wannan na zuwa ne a lokacin da gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP da wasu gwamnonin adawa ke tururuwar koma wa APC mai mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Manyan shugabannin jam’iyyar APC sun bayyana cewa ba za a ba gwamnonin da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar tikitin takara kai tsaye ba, duk da matsayinsu.

Wannan ya shafi gwamnonin da suka shiga APC kwanan nan kamar Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno; Gwamnan Taraba, Agbu Kefas; da Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An ji abin da ya jawo jinkiri game da zuwan Abba Kabir APC

APC za ta hana gwamnonin da ke sauya sheka takara kai tsaye
Shugaban APC na kasa, Yilwatda Nentawe Hoto: Prof Yilwatda Nentaw
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa haka kuma, an ce Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ake sa ran zai sauya sheƙa zuwa APC nan ba da jimawa ba, ba zai samu wata dama ta musamman ba.

Jam'iyyar APC ta tsaya da kafarta

Jaridar Punch ta wallafa cewa wani 'dan kwamitin ayyuka na 'kasa (NWC) na APC, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce sauya sheƙa daga wata jam’iyya zuwa APC ba ya nufin mutum zai samu tikitin takara kai tsaye.

A cewarsa, tsarin jam’iyyar ya tanadi adalci ta a fafata ga kowa, ba tare da la’akari da matsayin mutum ba, kuma a tabbatar da cewa an bi tsarin dimokuriadiyya.

Daraktan Yaɗa Labarai na APC, Bala Ibrahim, ya goyi bayan wannan matsayi a wata hira ta musamman da ya yi da kafar, inda ya bayyana APC a matsayin jam’iyya mai bin tafarkin dimokuraɗiyya sau da kafa.

Kara karanta wannan

Sauya sheka: Wasu 'yan APC na maganar hana Abba takara a 2027

Ya tabbatar da cewa dukkanin 'yan jam'iyya za su samu damar yin amfani da ‘yancinsu gaba ɗaya. Ya ce babu wanda za a fifita saboda sauya sheƙa ko mukami da yake kai.

APC: Martanin jam’iyyun adawa kan sauya sheka

A nasu martani, Sakatarorin Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyun adawa, wato Ini Ememobong na PDP da Oladipo Johnson na NNPP, sun ce sa rai da faruwar hakan.

Sun ƙara da cewa gwamnonin da suka bar jam’iyyunsu sun yi kuskuren siyasa, kuma lokaci ne kaɗai zai nuna sakamakon hakan.

Daga cikin gwamnonin PDP da suka sauya sheƙa zuwa APC akwai Umo Eno na Akwa Ibom, Sheriff Oborevwori na Delta, Peter Mbah na Enugu, Agbu Kefas na Taraba, da kuma Siminalayi Fubara na Rivers.

Ana hasashen Abba ba zai samu tikitin takara tai tsaye ba ko ya koma APC
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Shin Gwamnan Kano zai koma APC?

Shugabannin APC a Kano sun fara nuna alamun gwamna Abba Kabir Yusuf zai sauya sheka a jihar, kuma akwai alamun lamarin rashin tikitin takara zai shafe shi.

Baya ga gwamnonin, ‘yan majalisun tarayya da na jihohi, tsofaffin gwamnonin jihohi, tsofaffin ministoci da sauran manyan ‘yan siyasa da dama sun bar PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan

Sauya shekar Abba: NNPP ta ce lokaci bai ƙure ba, tana fatan Gwamna zai hakura

Zuwa yanzu dai Abba bai taba magana dangane da rade-radin sauya-sheka zuwa APC mai mulkin kasa ba sai dai Rabiu Kwankwaso ya nuna akwai alamun hakan.

Abba Atiku ya sauya sheka zuwa APC

A wani labarin, kun ji cewa Abubakar Atiku Abubakar, ɗan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar kuma tsohon dan takarar kujera lamba daya a Najeriya, ya fice daga PDP zuwa APC.

Ya kuma bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya sha alwashin yin aiki tukuru domin tabbatar da sake zaɓensa a zaɓen shekarar 2027 duk da yiwuwar mahaifinsa zai nemi kujerar.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, tare da shugabannin APC daga shiyyar Arewa maso Gabas, ne suka tarbi dan Atiku Abubakar tare da yi masa maraba zuwa jam’iyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng