Shigar Abba APC: Kwankwaso Ya Fitar da Sanarwa ga 'Yan Kwankwasiyya

Shigar Abba APC: Kwankwaso Ya Fitar da Sanarwa ga 'Yan Kwankwasiyya

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana jin dadinsa ga masu kare akidar Kwankwasiyya a kafafen sada-zumunta a daidai lokacin da ake rade-radin rikicin siyasa
  • Kwankwaso ya yaba da jajircewar matasa da magoya bayansa a kafafen sada zumunta na Facebook da X yayin da ake maganar sauya shekar Abba Kabir Yusuf
  • Wannan yabo na zuwa ne bayan tashin muhawarar siyasa da ke gudana, inda bangarori ke kare magoya bayansu kan makomar jam’iyyar NNPP a Kano da Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano — Jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yabawa matasan da ke fafutukar kare akidar Kwankwasiyya a kafafen sada-zumunta.

A sakon da ya fitar, ya bayyana cewa goyon bayansu na taka muhimmiyar rawa wajen gina makomar tafiyar siyasar da ya assasa.

Kara karanta wannan

Shiga APC: Kwankwaso ya fadi yadda Abba zai buga rikici da Ganduje

Rabiu Musa Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso tare da wasu 'yan Kwankwasiyya a Kano. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Wannan yabo ya zo ne a wani sako da ya fitar a X, inda ya nuna godiya ga masu tsayawa tsayin daka wajen kare manufofi da akidar tafiyar Kwankwasiyya.

Yabon Rabi'u Kwankwaso ga 'yan Kwankwasiyya

A cikin sakonsa, Kwankwaso ya ce yana mika godiya ta musamman ga dakarun kafafen sada-zumunta na Kwankwasiyya, magoya baya da dukkan masu yi musu fatan alheri.

Ya ce jajircewarsu da biyayyarsu ga akidar Kwankwasiyya— wadda ta kunshi hidima, gaskiya da cigaban da ya shafi al’umma — ita ce ginshikin da ake gina kyakkyawar makomar tafiyar a kai.

Kwankwaso ya kara da cewa hakuri da juriyar da magoya bayan ke nunawa a lokutan jarabawa da kalubale na siyasa na kara tabbatar da cewa Kwankwasiyya tafiya ce mai tushe da manufa.

Yadda ake muhawarar siyasa a Kano

Yabon Kwankwaso na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta muhawara mai zafi a kafafen sada-zumunta, musamman Facebook da X, biyo bayan rade-radin cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Kara karanta wannan

Abokin takarar Kwankwaso ya fito ya yi magana ana batun shirin Abba na komawa APC

Wannan batu ya raba ra’ayin magoya bayan NNPP da Kwankwasiyya, inda kowane bangare ke kare bangaren da ya ke yi wa biyayya.

A wannan yanayi, magoya bayan Kwankwaso sun fito fili suna kare tafiyar Kwankwasiyya da matsayinsa, suna martani ga masu sukar sa ko kuma masu goyon bayan yiwuwar sauya shekar gwamnan.

Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso
Sanata Rabiu Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf a Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Wannan ne ya sa Kwankwaso ya ga dacewar yabawa da karfafa gwiwar wadanda ke tsayawa a bangarensa suna cewa har yanzu suna tare da shi.

A halin da ake ciki, Gwamna Abba Kabir Yusuf bai fitar da irin wannan sakon yabo ga magoya bayansa a kafafen sada-zumunta ba.

Maganar takarar Abba Kabir a APC

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu mazauna Kano sun fito karara sun yi magana kan rade-radin sauya shekar Abba Kabir Yusuf zuwa APC.

Wasu 'yan APC kamar Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda sun bayyana cewa ba za su ba Abba Kabir takarar gwamna kai tsaye ba ko ya koma cikinsu.

Dan Bilki Kwamanda ya jaddada cewa jam'iyyar APC ta ginu ne a kan tsari na musamman kuma duk wanda ya shiga cikinta dole ya bi tsarinta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng