Tazarce: Gwamna Ya Jero Dalilan da Za Su Sanya Ƴan Kaduna Su Zabi Tinubu a 2027

Tazarce: Gwamna Ya Jero Dalilan da Za Su Sanya Ƴan Kaduna Su Zabi Tinubu a 2027

  • Gwamna Uba Sani ya sanar da goyon bayan Kaduna ga tazarcen Shugaba Bola Tinubu a 2027 saboda wasu dalilai da ya lissafo
  • Gwamnan jihar na Kaduna ya ce Tinubu ya yi wa Kaduna duk wani gata da ake bukata, ciki har da gina layin dogo na zamani
  • A cewar Uba Sani, APC za ta samu akalla mabiya miliyan uku a yayin da take rajistar mambobi a intanet, gabanin zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce al'ummar jiharsa za su goyi bayan tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda romon dimokuradiyya da ya kawo.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin taron masu ruwa da tsaki kan aikin rajistar mambobin jam'iyyar APC na intanet da ake gudanarwa.

Kara karanta wannan

Bashir Ahmad ya soki Abba Kabir kan tsawaita maganar zuwa APC, ya fadi illar dambarwar

Gwamna Uba Sani ya ce Tinubu ya yi wa Kaduna sha tara ta arziki kuma za su zabe shi a 2027
Gwamna Uba Sani tare da Shugaba Bola Tinubu a Aso Rock Villa, Abuja. Hoto: @ubasanius
Source: Twitter

Ayyukan raya kasa da karuwar karfin APC

Uba Sani ya ce Kaduna tana sa ran samun mambobi miliyan 2.5 a wannan aiki, domin a cewarsa, APC ce yanzu take da rinjaye a jihar baki daya, in ji rahoton Daily Trust.

Gwamnan ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya tallafa wa aikin samar da jirgin kasa na "Light Rail" a Kaduna da kudi Naira biliyan daya.

Ya bayyana cewa babu wata jiha a Najeriya da ta samu irin wannan tallafin ban da Jihar Legas, wanda hakan ke nuna fifikon da aka ba Kaduna.

Gwamnan ya kara da cewa salon mulkinsa na tafiya da kowa ya sanya mambobin jam'iyyun hamayya da dama komawa APC domin gina jihar cikin hadin kai da fahimtar juna.

Sabon aikin dala miliyan 200 a Kaduna

A yayin jawabin nasa, Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa nan da makonni uku za a kaddamar da babban aikin gidan kiwon tsuntsaye na hadin gwiwa da kasar Sin a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

ADC ta samo hanyar ceto Najeriya daga hannun Shugaba Tinubu

The Nation ta rahoto Gwamna Uba Sani ya ce:

"Shugaba Tinubu ya amince da kashe dala miliyan 200 domin wannan aikin kiwon tsuntsaye wanda zai samar da ayyukan yi akalla 350,000."

Ya kara da cewa:

"Wannan zai zama shirin kiwon tsuntsaye mafi girma a yankin kudu da hamadar Sahara, kuma zai tallafa wa kananan 'yan kasuwa akalla 10,000."
Gwamna Uba Sani ya ce Tinubu ya kaddamar da muhimman ayyuka a Kaduna da ya cancanci tazarce
Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya na jawabi a yayin bude wata kasuwa da aka rufe a yankin Birnin Gwari. Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Gina hanyoyin Mando da Birnin Gwari

Haka kuma, gwamnan ya mika godiya ga Shugaba Tinubu kan amincewa da gina hanyar Mando zuwa Birnin Gwari da kuma sake gina hanyar Kwoi zuwa Jama'a.

Ya nuna cewa Kaduna tana da sa a sakamakon samun mutane a gwamnatin tarayya, kamar shugaban majalisar wakilai Tajuddeen Abbas da ministan muhalli Balarabe Abbas Lawal.

A cewarsa, hadin gwiwa da ministan muhalli zai kawo aikin magance zaizayar kasa (ACReSAL) a yankunan Zaria da Rigasa wanda darajarsa ta kai kusan Naira biliyan 53.

Gwamna Uba Sani ya cewa da wadannan nasarori, Kaduna za ta zama a sahun gaba wajen nuna goyon baya ga Shugaba Tinubu a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Kano da wasu jihohin Najeriya 4 da siyasarsu ke ɗaukar zafi gabanin zaɓen 2027

An fara yakin nemawa Tinubu tazarce

A wani labari, mun ruwaito cewa, yayin da ake tunkarar 2027, wasu jiga-jigan APC sun fara kokarin tabbatar da sake zaben Shugaba Bola Tinubu.

Duk da cewa ba a fara yakin neman zabe ba a hukumance, shugabannin APC irin su Abdullahi Ganduje da George Akume sun bukaci ‘yan takarar Arewa su dakata har zuwa 2031.

Ganduje ya jagoranta a hedikwatar APC ya bukaci ‘yan siyasar Arewa da ke da burin shugabancin kasa su hakura har sai bayan Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com