APC Ta Fito Karara Ta Yaba wa Atiku duk da Adawar da Ya ke da Tinubu

APC Ta Fito Karara Ta Yaba wa Atiku duk da Adawar da Ya ke da Tinubu

  • Jam’iyyar APC ta ce shigowar Abba Atiku Abubakar cikinta ba zai iya girgiza ta ba, tana mai bayyana kanta a matsayin jam’iyya mai tsari da ladabi da biyayya
  • APC ta yaba wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, bisa yadda ya ware kansa daga siyasar dansa tare da nuna girmamawa ga ka’idar dimokuradiyya
  • Jam’iyyar ta ce rade-radin cewa Abba Atiku na iya shigowa APC da wata manufa ta boye ba su da tushe, tana mai jaddada cewa tsarinta ya fi karfin mutum daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jam’iyyar APC ta yi watsi da rade-radin da ke cewa shigowar Abba Atiku Abubakar daga jam’iyyar PDP zuwa cikinta na iya haddasa rikici ko girgizata.

A cewar jam’iyyar, APC ta ginu ne a kan tsari, ladabi da ka’idoji masu karfi da ba za su bar mutum guda ya kawo rudani ba kwata-kwata.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda Lawal ya mika wasikar komawa APC? Jam'iyyar ta yi karin haske

Atiku Abubakar da shugaba Bola Tinubu
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|Paul Ibe
Source: Getty Images

Punch ta wallafa cewa APC ta kuma yabawa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, bisa yadda ya bayyana matsayinsa cikin natsuwa kan matakin da dansa ya dauka.

APC ta yaba wa Atiku Abubakar

Mataimakin sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC na kasa, Nze Chidi Duru, ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman, yana mai cewa jam’iyyar ta girmama kalaman Atiku da yadda ya bi ka’idar dimokuradiyya.

Nze Chidi Duru ya ce APC na maraba da kowane dan kasa da ya yanke shawarar shigowa jam’iyyar bisa yardar ransa. Ya ce batun uba da da abu ne mai sarkakiya, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne girmama ra’ayin kowa.

A cewarsa, Atiku Abubakar ya fito fili ya bayyana cewa ba ya tilasta wa ‘ya’yansa ko wani dan kasa ra’ayi a harkar siyasa. APC ta ce wannan matsaya ta nuna mutunta tsarin dimokuradiyya.

Duru ya ce ya dace a mutunta ra’ayin Atiku da kuma na dansa, wanda ya zabi shigowa APC maimakon wasu jam’iyyu. Ya kara da cewa jam’iyyar ta yaba wa tsohon mataimakin shugaban kasa bisa yadda ya dauki lamarin cikin kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Sauya sheka: Wasu 'yan APC na maganar hana Abba takara a 2027

Martani kan zargin rusa jam'iyyar APC

Dangane da rade-radin da wasu ke yadawa cewa Abba Atiku na iya shigowa APC da wata manufa ta boye, Duru ya ce hakan ba zai yiwu ba. Ya bayyana cewa APC jam’iyya ce da ke da ginshikai masu yawa da suka hada da ladabi, tsari da bin umarni.

A cewarsa, ba zai yiwu mutum daya ya shigo jam’iyyar ya tarwatsa tsarin da aka gina tsawon shekaru ba. Ya ce APC ta saba karbar ra’ayoyi daban-daban, amma duk wanda ya shigo dole ne ya bi dokoki da tsarin jam’iyyar.

Abba Atiku Abubakar da ya shiga APC
Sanata Barau Jibrin yayin karbar Abba Atiku Abubakar zuwa APC.
Source: Facebook

Duru ya jaddada cewa jam’iyyar ta mayar da hankali ne wajen samar da shugabanci nagari da kuma zama abin alfahari ga ‘yan Najeriya.

Maganar da Atiku Abubakar ya yi

A wani rahoton, kun ji cewa Atiku Abubakar ya bayyana matsayarsa bayan shigar dansa APC, inda ya ce matakin lamari ne na karan kansa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce shi mai kishin dimokuradiyya ne, kuma ba ya tilasta wa ‘ya’yansa ko al’umma ra’ayi a harkar siyasa.

Sai dai ya sake jaddada sukar gwamnatocin APC, yana alakanta hakan da kalubalen tattalin arziki da zamantakewa da kasar ke fuskanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng