Amaechi Ya Dora Laifin Gaza Sauya Gwamnati kan 'Yan Adawa, Ya Fadi Kuskurensu
- Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi tsokaci kan siyasar Najeriya da matsalar da ke sa 'yan adawa gaza yin katabus
- Rotimi Amaechi ya bayyana cewa bai yi wa Mai girma Bola Tinubu kallon mutumin da ba za a iya kayarwa ba a zabe
- Sai dai, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya bayyana cewa jam'iyyun adawa su ne matsalar saboda kuskuren da suke yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Ministan sufuri kuma jigo a jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa 'yan adawa sun kasa yin abin da ya dace.
Rotimi Amaechi ya bayyana cewa matsalolin zaɓe da Najeriya ke fuskanta ba wai saboda rinjayen masu mulki ba ne, illa gazawar jam’iyyun adawa.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Amaechi ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wani taron jama’a a ranar Juma’a, 16 ga watan Janairun 2026.
Amaechi ya ce za a iya kifar da Tinubu
Amaechi ya ce Shugaba Bola Tinubu “ba wanda ba a iya kayarwa ba ne,” yana mai jaddada cewa jam’iyyun adawa ne babban matsalar siyasar kasar.
Jawabinsa na zuwa ne a daidai lokacin da rikice-rikicen cikin gida ke girgiza jam’iyyun adawa, inda suka rabu kashi-kashi, lamarin da ya raunana karfinsu na kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki.
Yayin da rikicin ke kara ta’azzara, wasu ’yan siyasar adawa sun zargi Tinubu da APC da hura wutar rikicin ta hanyar ɗaukar nauyin sauya sheka daga jam’iyyunsu.
Amaechi ya fadi kuskuren 'yan adawa
Sai dai Amaechi ya yi watsi da wannan zargi, yana ɗora alhakin matsalolin siyasar ƙasar kan jam’iyyun adawa.
“Tinubu ba wanda ba za a iya kayarwa ba ne; jam’iyyar adawa ce matsala. Ban ɗauke shi a matsayin wanda ba za a iya doke shi ba. Matsalar ita ce jam’iyyar adawa."
- Rotimi Amaechi
Ya ce jam’iyyun adawa sun shagaltu da lissafin kabilanci da na yankuna wajen rabon mulki, maimakon tattaunawa kan kyakkyawan shugabanci da farfaɗo da ƙasa.
“Ina faɗa wa jam’iyyun adawa cewa ku ne matsalar. Babu wanda ke cewa, ‘To, abubuwa sun lalace. Ta yaya za mu sauya ɗan takara? Za ku yi wa’adi ɗaya ne ko ba za ku yi ba?’ Wannan kaɗai ake tattaunawa. Ba wani abu daban ba."
“Yayin da masu hannu da shuni ke ta tattaunawa kan yadda za su samu mulki, masu jefa ƙuri’a, wato ’yan ƙasa, suna taimaka musu wajen cimma wannan buri.”
- Rotimi Amaechi

Source: Twitter
Amaechi na ganawa da 'yan siyasa
Amaechi ya kuma bayyana cewa yana ganawa da ’yan siyasa daban-daban gabanin zaɓen 2027.
“Idan ka tambayi waɗanda ke ganawa da ni, za su faɗa maka cewa ina ta ganawa da su, ina tattaunawa kan yiwuwar samun nasara a zaɓen 2027."
- Rotimi Amaechi
Amaechi ya ba gwamnati shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya ba gwamnati shawara kan matsalar rashin tsaro.
Rotimi Amaechi ya ce yaki da rashin tsaro ba zai haifar da sakamako mai kyau ba muddin gwamnati ba ta magance matsalar yunwa a tsakanin ‘yan kasa ba.
Ya ce dogaro kawai da karfin soja ko ‘yan sanda wajen yaki da rashin tsaro ba tare da magance talauci da yunwa ba, ba zai samar da abin da ake so ba.
Asali: Legit.ng

