Tsohon Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisa Ya Sauya Sheka daga PDP zuwa APC
- Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta samu karuwa bayan wani tsohon jigo a PDP ya sauya sheka zuwa cikinta a jihar Plateau
- Sanata Simon Mwadkwon wanda ya kasance tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, ya raba gari da jam'iyyar PDP
- Tsohon sanatam ya sanar da dattawan APC a Plateau ta Arewa kujerar da yake son nema a zaben shekarar 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Simon Mwadkwon, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Mwadkwon ya wakilci Plateau a majalisar dattawa ta 10, kuma ya yi aiki na ɗan lokaci a matsayin shugaban marasa rinjaye na majalisar a shekarar 2023.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta ce ya sanar da sauya shekarsa ne yayin wata ziyara da ya kai wa dattawan jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta jihar Plateau, a ranar Alhamis, 15 ga watan Janairun 2026.
Simon Mwadkwon ya koma APC daga PDP
Simon Mwadkwon ya bayyana cewa ya kai musu ziyarar ne domin sanar da su shigarsa jam'iyyar APC.
“Na zo nan ne domin sanar da shigata jam’iyyar APC a hukumance, tare da neman shawarwari daga dattawan jam’iyya da ke kusa da jama'a."
- Simon Mwadkwon
Mwadkwon ya ce ya yanke wannan shawara ne bayan shawarwari masu zurfi da ya yi da al’ummar mazabarsa, masu ruwa da tsaki a siyasa, ’yan uwa da abokan hulɗa a duk faɗin yankin Plateau ta Arewa.
Yankin Plateau ta Arewa ya haɗa da kananan hukumomin Barkin Ladi, Riyom, Jos ta Arewa, Jos ta Kudu, Jos ta Gabas da Bassa.
Me ya ce kan sauya shekarsa
Ya bayyana sauya shekar ta sa a matsayin wani tsari na sake daidaita siyasa domin karfafa haɗin gwiwar siyasa da kuma tabbatar da wakilci mai inganci ga al’ummarsa.
“Wannan shawara ta samo asali ne daga burin yin aiki tare da shugabanni masu kishin inganta shugabanci da tabbatar da cewa muryar jama’armu na isa wuraren da ya kamata."
- Simon Mwadkwon

Source: Facebook
Rahoton Premium Times ya nuna cewa Mwadkwon ya shaida wa shugabannin jam’iyyar cewa sauya shekarsa ba wai surutu ba ne, illa wani ɓangare na babban yunkuri na ginawa da karfafa APC a jihar Plateau gabanin zaɓen 2027.
Har ila yau, ya sanar da dattawan jam’iyyar aniyarsa ta sake tsayawa takarar kujerar Sanata a zaɓen 2027.
Mwadkwon ya taa zuwa majalisa
Mwadkwon ya lashe zaɓen Sanatan Plateau ta Arewa a shekarar 2023 a karkashin jam’iyyar PDP. Sai dai dotun daukaka kara ta soke nasarar da ya samu tare da bayar da umarnin a sake zaɓe.
Zaɓen cike gurbin da aka gudanar daga bisani ya haifar da Sanata mai ci yanzu, Dachungyang Mwadkon, wanda ya yi nasara a ƙarƙashin jam’iyyar ADP.
Dan Atiku ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Abubakar Atiku Abubar wanda yake da ne a wajen tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ne, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan
Ana jita-jitar barin Abba NNPP, Ganduje ya dawo Najeriya, zai bazama harkar siyasa
Abubakar Atiku Abubakar ya samu tarba daga wajen manyan jiga-jigan jam'iyyar APC bayan sauya shekarsa.
Ya bayyana cewa shirye yake ya mara baya ga tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

