Waiwaye: Yadda Ɗan Obasanjo ya goyi bayan Buhari Shekaru kafin Abba Atiku ya Koma APC

Waiwaye: Yadda Ɗan Obasanjo ya goyi bayan Buhari Shekaru kafin Abba Atiku ya Koma APC

  • A daren Juma'a, 15 ga watan Janairu, 2026 ne aka samu bullar labarin cewa 'dan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya sauya sheka
  • 'Dan tsohon 'dan takarar Shugaban kasar, ya ɗauki matakin da da yawa ke ganin abin mamaki ne, inda ya nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu
  • Amma ba a kan Atiku iyalai su ka fara wannan ba, an gano yadda 'dan tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya goyi bayan Muhammadu Buhari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – A daren Juma'a, 15 ga watan Janairu, 2026 ne aka samu labarin cewa ɗan Atiku Abubakar, wanda aka fi sani da Abba, ya sanar da shiga APC daga tsohuwar jam’iyarsa.

Bayan koma wa APC ne kuma Abba ya sanar da goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu yayin da mahaifinsa, Atiku Abubakar ke neman kujerarsa a 2027.

Kara karanta wannan

Kusa a APC ya sha alwashin cin amanarta idan aka ba Abba tikitin takara a Kano

Dan Atiku ya yi abin da 'dan Obasanjo ya yi a baya
Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Mataimakinsa Atiku Abubakar Hoto: @Rasheethe
Source: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Abubakar Atiku Abubakar ya tabbatar da cewa zai yi aiki tukuru wajen ganin Tinubu ya lashe zaben.

Abba ya yi fatali da mahaifinsa, Atiku

Daily Trust ta ruwaito cewa bai tsaya nan ba, ya sanar da cewa ya juyar da duk kayan yakin da ya tanadar wa mahaifinsa Atiku a zaɓen baya ga Tinubu.

Ya ce:

“Sunana Abubakar Atiku Abubakar, amma kowa yana kirana Abba. A yau na zo ne in sanar da barina tsohuwar jam’iyya da muka yi aiki a 2023, tare da yanke shawarar shiga APC. Bisa haka, zan yi aiki don ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu wa’adin shugabanci na biyu a 2027.”

Lamarin Abba ya yi kama da abin da Olujonwo Obasanjo, ɗan tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, ya yi a lokacin zaɓen 2019.

Abba Atiku ya bi sawun 'dan Olusegun Obasanjo

Kara karanta wannan

ADC: Momodu ya kare Atiku kan zargin shirin amfani da kuɗi wajen sayen takara

A wancan lokaci, duk da rashin jituwa tsakanin Obasanjo da Buhari, Olujonwo ya rubuta wata sanarwa mai shafi biyu yana goyon bayan Shugaba Buhari.

A cikin sanarwar, ya lissafa nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu kamar: samar da tushe mai ƙarfi ga matasa da ƙarni na gaba, tallafawa manoma, ‘yan kasuwa, mata da masana’antu.

'Dan Obasanjo, Olujonwo ya goyi bayan Buhari a lokacin da ya ke neman zabe a baya
Tsohon Shugaban Najeriya, Marigayi Muhammadu Buhari Hoto: Bashir Ahmad
Source: Twitter

Ya kara da bayyana goyon bayansa saboda a ganinsa, gwamnatin Buhari ta sake farfado da masana’antar ƙarfe ta Ajaokuta da tashoshin ruwa na Baro da Lokoja.

Olujonwo ya yi kira ga matasa da su haɗa kai wajen tallafawa ci gaban Buhari, yana mai cewa:

“Muna kan hanya madaidaiciya, amma bai kamata mu koma zaman bauta ba. Mu matasa, mu haɗa kai don mayar da Buhari kan mulki a 2019.”

Jam'iyyar APC ta yi wa Atiku shagube

A wani labarin, kun ji cewa APC reshen jihar Legas ta bayyana matakin ɗan Atiku Abubakar na shiga cikinta da goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a matsayin babban koma-baya ga amincin siyasar mahaifinsa.

Kakakin APC a jihar Legas, Seye Oladejo, ya ce barin tsarin ADC da ɗan Atiku ya yi, ya bayyana rashin gamsuwa da siyasar mahaifinsa, inda ya koma AOC domin neman mafita mai kyau.

APC ta yi tir da salon siyasar Atiku na sauya jam’iyya sau da dama, tare da bayyana shi a matsayin mai neman kujerar shugaban ƙasa fiye da tsaya wa a kan akidar siyasarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng