Sauya Shekar Abba: NNPP Ta Ce Lokaci bai Ƙure ba, Tana Fatan Gwamna Zai Hakura
- Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa har yanzu tana fatan Gwamna Abba Kabir Yusuf zai dakatar da shirin sauya sheka zuwa APC
- Kakakin jam’iyyar ya ce gudanar da tattaunawa da shawarwari a kan matsalar, kuma lokaci bai kure ba kan batun yanke hukunci
- Ladipo Johnson ya bukaci ‘yan Kwankwasiyya su guji duk wani kazamin rikici, tare da kiyaye hadin kai da fahimtar juna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano –Jam'iyyar NNPP ta bayyana cewa har yanzu tana fatan Gwamna Abba Kabir Yusuf zai fasa sauya sheka zuwa APC mai mulkin Najeriya.
Mai magana da yawun jam'iyyar na kasa, Ladipo Johnson, ya shaida wa Legit hakan a wata hira da ya yi ta wayar tarho.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta hango lam'a a kalaman Kwankwaso na tilasta wa masoyansa koma wa APC

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa yanzu haka shiri ya yi nisa na sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP a Kano zuwa APC.
Fatan jam'iyyar NNPP a kan Gwamna Abba
A martaninsa game da wannan shiri, Ladipo Johnson ya bayyana cewa babu wata jam'iyya da za ta ji dadin rasa Gwamnanta, saboda haka lokaci bai kure ba da Gwamna Abba zai iya hakura da sauya jam'iyya idan ya ga dama.
A kalamansa:
"Na san ana ta maganganu da tuntuba a kan al'amarin, duk da ba za mu iya tilasta wa junanmu yin abin da ba ma ra'ayi ba."
"Akwai dama, ba lallai ne ya tabbata ba, amma akwai damar Gwamna ya fasa sauya sheka."
Ya kara da cewa an yi zama iri-iri, an samu shawarwari da tuntuba domin ganin Gwamnan ya ci gaba da zama a cikin NNPP da Kwankwasiyya, kuma yana ganin ba a cire rai da canja ra'ayi ba.

Kara karanta wannan
Rikicin NNPP: An wanke Gwamna Abba, ba ya bukatar izinin Kwankwaso kafin komawa APC
NNPP ta nemi hadin kan ‘yan Kwankwasiyya
A kalaman Ladipo Johnson, bai kamata a samu wata baraka da za ta jawo rikici mara dadi a tsakanin ‘yan Kwankwasiyya ba, yana mai jaddada bukatar fahimtar juna da hakuri.
Ya ce duk da ana fatan Gwamna Abba Kabir Yusuf zai iya fasa sauya sheka, babu wanda zai masa dole ya ci gaba da zama a NNPP idan ba ya so, domin siyasa ta ginu ne a kan ra'ayi.

Source: Twitter
Ya ce:
"Idan Mai Girma Gwamna da magoya bayansa na son sauya sheka, babu dalilin da zai sa dole s addai an bata da juna."
"Idan suna ganin cewa can ta fi masu nan, to shikenan. Ba sai an samu saɓani a tsakanin mutanen da suka shafe shekaru a tare ba."
"Ba na jin APC ta fi masa nan, da APC wuri ne mai kyau, da dukkaninmu mun zama ‘yan jam'iyyar."
Ya kammala da cewa jam'iyyar NNPP za ta ci gaba da kokarin kare hadin kai da martabar ‘yan Kwankwasiyya, tare da fifita zaman lafiya da girmama ra’ayoyin juna a kowane mataki na siyasa.
NNPP ta magantu kan hukuncin kotu
A baya, mun ruwaito cewa NNPP ta yi watsi da rahotannin da umarnin wata kotun jihar Kano da ta yi umurnin rushe shugabancin jam’iyyar a matakin jihar, kananan hukumomi da mazabu.
Kakakin jam’iyyar na ƙasa, Ladipo Johnson, ya ce hukuncin da ake yadawa bai bi ka’idojin da kundin tsarin jam’iyyar ya tanada ba, saboda babu maganar rushe mata shugabanci.
A cikin sanarwar da NNPP ta fitar, ta jaddada cewa tsarin zaben shugabanci da yanke hukunci a cikin jam’iyya yana ƙarƙashin dokokin jam’iyyar da suka amince da su tun farko.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
