Dan Atiku Ya Sauya Sheka daga PDP zuwa APC, Ya Goyi bayan Tazarcen Tinubu

Dan Atiku Ya Sauya Sheka daga PDP zuwa APC, Ya Goyi bayan Tazarcen Tinubu

  • Daya daga cikin 'ya'yan Alhaji Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya
  • Abubakar Atiku Abubakar wanda aka fi sani da Abba ya samu tarba daga wajen jiga-jigan jam'iyyar APC bayan sauya shekarsa
  • Ya bayyana dalilin da ya sa ya zabi shiga jam'iyyar APC tare da goyon bayan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Abubakar Atiku Abubakar, ɗan tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Abubakar Atiku Abubakar ya yi alkawarin yin aiki domin sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Dan Atiku Abubakar ya koma jam'iyyar APC
Abubakar Atiku Abubakar a wajen sauya shekarsa zuwa APC Hoto: @barauijibrin
Source: Twitter

Dan Atiku ya koma APC daga PDP

Jaridar Vanguard ta ce an sanar da sauya shekar ne a hukumance ranar Alhamis, 15 ga watan Janairun 2026 a majalisar tarayya.

Kara karanta wannan

"Za a iya": Jigo a ADC ya gano hanyar da 'yan adawa za su kifar da Tinubu a 2027

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin da kuma shugabannin APC daga shiyyar Arewa maso Gabas sun tarbi Abubakar wanda aka fi sani da Abba.

Abba Atiku ya yi jawabi

Da yake jawabi a wajen taron, Abba ya sanar da ficewarsa daga PDP tare da bayyana shigarsa APC, yana mai bayyana matakin a matsayin na kashin kai kuma mai cike da tarihi, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Haka kuma ya umarci dukkan jagorori da kungiyarsa wadda a baya aka sani da Haske Atiku Organisation da aka kafa a 2022, da su gaggauta shiga APC tare da mara wa ajandar Renewed Hope ta Shugaba Tinubu baya.

“Sunana Abubakar Atiku Abubakar, amma kowa na kirana Abba. Ina nan yau domin sanar da ficewata daga tsohuwar jam’iyyata, inda muka yi aiki a 2023, da kuma yanke shawarar shiga APC."

- Abubakar Atiku Abubakar

Meyasa ya koma APC?

Ya danganta matakin da ya ɗauka da irin salon jagoranci na Sanata Barau Jibrin da kuma yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da mulki.

“Da wannan ci gaba, zan yi aiki tare da Sanata Barau domin tabbatar da sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wa’adi na biyu a 2027."

Kara karanta wannan

'Tsari mai kyau,' Jigon ADC ya fadi yadda za a cire Tinubu daga Aso Rock a 2027

"Saboda haka, ina umartar dukkan jagorori da mambobin ƙungiyata da su shiga APC tare da yin aiki domin Shugaba Tinubu."

- Abubakar Atiku Abubakar

Abubakar Atiku Abubakar ya fice daga PDP zuwa APC
Abubakar Atiku Abubakar tare da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin Hoto: @barauijibrin
Source: Twitter

Ya samu tarba daga jiga-jigan APC

Da yake maraba da shi cikin jam’iyyar, mataimakin shugaban APC na lasa (Arewa maso Gabas), Kwamared Mustapha Salihu, ya bayyana sauya shekar a matsayin abin misali kuma mai tasiri.

“Yau na ɗaya daga cikin ranakun farin ciki. Wannan matashi ya ga manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu, kuma ya yanke shawarar mara musu baya."

- Mustapha Salihu

Datti Baba Ahmed ya dura kan Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023, Datti Baba-Ahmed ya ragargaji Atiku Abubakar.

Datti Baba-Ahmed ya nuna damuwa kan tsawon lokacin da Atiku Abubakar ya dauka yana neman mulkin Najeriya.

Jigon jam'iyyar LP ya ce duba dadewar Atiku a duniya, ya kamata ya bar matasa masu danyen jini su samu dama a siyasar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng