An Samu Matsala a Shirin Ganawar Gwamnan Kano da Tinubu kan Batun Komawa APC

An Samu Matsala a Shirin Ganawar Gwamnan Kano da Tinubu kan Batun Komawa APC

  • Alamu sun nuna cewa ganawar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba za ta yiwu ba a halin yanzu
  • Wasu majiyoyi sun bayyana cewa gwamnan ya fara ganawa da jiga-jigan APC na Kano domin tabbatar masu da shirinsa na sauya sheka
  • Rahotanni sun nuna cewa duk da halin da siyasar Kano ke ciki, Abba ya lallaba cikin sirri ya gana da Kwankwaso a gidansa da ke titin Miller

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya fara ganawa da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar Kano a wani bangare da shirye-shiryen komawa jam'iyyar.

Wasu majiyoyi sun ce tun farko, Gwamna Abba ya nemi ganawa da Shugaba Bola Tinubu a kasar Faransa, amma daga bisani gwamnan ya soke tafiyar a kurarren lokaci.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an gano dalilai 3 da suka jawo jinkirin sauya shekar Gwamna Abba zuwa APC

Gwamna Abba.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin jihar Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Me ya hana Abba ganawa da Tinubu?

Jaridar Daily Nigerian ta ce yayin da wasu ke danganta soke tafiyar tasa zuwa Paris da "matsalar biza", wasu kuma na zargin cewa bai samu izinin ganawa da shugaban kasar ba.

Idan za a iya tunawa, a makon jiya ne Gwamna Abba ya yi wata ganawar sirri da ubangidansa na siyasa, Rabiu Kwankwaso, a gidansa da ke titin Miller a Kano.

Majiyoyi sun ce yayin ganawar, Abba ya tabbatar wa Kwankwaso cewa ba zai dauki kowane mataki ba sai ya gana da shugaban kasa, kuma ya shaida masa sharuɗɗan da ya gindaya na shiga APC, cewar Tribune Nigeria.

Gwamna Abba ya dage sai ya bar NNPP

Sai dai yayin da lokacin babban taron APC ke karatowa, kuma Abba ya kasa samun ganawa da Tinubu, ga matsin lamba na karuwa a kansa, majiyoyi sun ce akwai yiwuwar gwamnan ya sanar da ficewa daga NNPP "a kowane lokaci".

Kara karanta wannan

Abokin takarar Kwankwaso ya fito ya yi magana ana batun shirin Abba na komawa APC

Jaridar ta ce ta samu bayanai da ke nuna Gwamna Abba ya gana da shugaban kwamitin kasafi na majalisar wakilai, Abba Bichi, a ranar Talata don kara sanar da shi aniyarsa ta komawa APC.

Abba ya gana da hadimin Shugaba Tinubu

A ranar Laraba kuma, gwamnan ya gana da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin zama dan kasa da shugabanci, Nasir Ja’oji.

Idan wannan rahoto ya tabbata, Mai girma Gwamna Abba ya bukaci Ja'oji da ya kira shugaban jam’iyyar APC na jiha, Abdullahi Abbas, domin su zauna su tattauna.

Majiyoyi sun ce gwamnan ya kuma umarci mai magana da yawunsa da ya gayyaci wasu wakilan kafafen yada labarai zuwa Abuja domin "wani muhimmin taro."

Gwamna Abba da Ganduje.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje Hoto: Sanusi Bature, Dr. Abdullahi Ganduje
Source: Facebook

A ranar Litinin, masu ruwa da tsakin APC a Kano suka gudanar da wani taron dare a gidan Ganduje da ke Abuja, domin tattauna batun komawar gwamnan da kuma rajistar mambobi ta yanar gizo.

Amma lokacin da Gwamna Abba ya samu labarin shirin masu ruwa da tsakin na ci gaba da tafiya ba tare da shi ba, majiyoyi sun ce ya tuntube su yana neman a dage taron, tare da jaddada shirinsa na shiga APC.

Kara karanta wannan

Rikicin NNPP: An wanke Gwamna Abba, ba ya bukatar izinin Kwankwaso kafin komawa APC

Dalilan da suka hana Abba komawa APC

A dazu, mun kawo muku cewa an samu sababbin bayanai kan dalilan da suka sa aka samu jinkirin sauya shekar Gwamnan Abba daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa kusan an kammala dukkan shirye-shiryen sauya shekar, domin mai girma gwamnan ya riga ya yanke shawarar tafiya.

Daga cikin dalilai uku da aka tattaro, akwai sharadin da Shugaba Tinubu ya gindaya wa Abba na zama da masu ruwa da tsaki a Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262