"Za a Iya": Jigo a ADC Ya Gano Hanyar da 'Yan Adawa Za Su Kifar da Tinubu a 2027

"Za a Iya": Jigo a ADC Ya Gano Hanyar da 'Yan Adawa Za Su Kifar da Tinubu a 2027

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa, Dele Momodu, ya yi tsokaci kan babban zaben gama gari na shekarar 2027 da ake tunkara
  • Dele Momodu ya bayyana cewa raba Shugaba Bola Tinubu da mulkin Najeriya ba abu ba ne mai wuya kamar yadda wasu ke tunani
  • 'Dan siyasar ya bayyana cewa jam'iyyar adawa ta ADC na da jiga-jigan da za su iya fafatawa da Tinubu kuma har su samu nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa, Dele Momodu, ya ce akwai yiwuwar kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaben gama gari na 2027.

Dele Momodu ya ce za a iya kifar da Shugaba Tinubu ne idan ’yan adawa suka sanya ido sosai kan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Dele Momodu ya ce za a iya kifar da Tinubu
Dele Momodu tare da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DeleMomodu
Source: Facebook

Cif Dele Momodu ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin The Morning Brief na Channels Tv a ranar Alhamis, 15 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

'Tsari mai kyau,' Jigon ADC ya fadi yadda za a cire Tinubu daga Aso Rock a 2027

Yadda za a raba Bola Tinubu da mulki

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya jaddada cewa cire Shugaba Tinubu daga mulki ba abu ne mai wuya ba.

A cewar dan siyasar, wanda kwanan nan ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa ADC, ’yan adawa na bukatar ’yan takara masu karfin siyasa da jajircewar da za su iya kalubalantar jam’iyya mai mulki.

“Ban san dalilin da ya sa mutane ke tunanin ba zai yiwu a cire Asiwaju ba. Ku yarda da ni, muddin muka sanya ido sosai kan INEC, kuma shi ya sa ake bukatar ’yan takara da za su iya yin abin kirki."

- Dele Momodu

Jam'iyyar ADC na da manyan jiga-jigai

Momodu ya bayyana cewa jam’iyyar ADC na da fitattun jiga-jigai da dama da za su iya fafatawa da Shugaba Tinubu da APC.

Ya ambaci tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma tsohon kakakin majalisar wakilai, Aminu Tambuwal; tsohon ministan babban birnin tarayya kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan

Tambuwal ya gano babbar matsalar da ta addabi bangaren zabe a Najeriya

Hakazalika ya ambaci tsohon gwamnan jihar Rivers, Chibuike Rotimi Amaechi, a matsayin wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar.

“Don haka muna da mutane da yawa, jerin ’yan siyasa masu karfi a cikin ADC. A gare ni, ba batun mutum daya ba ne."
"Tabbas akwai Peter Obi, wanda INEC ta rubuta cewa ya zo na uku da Atiku Abubakar wanda ya zo na biyu."

- Dele Momodu

Dele Momodu ya ce ADC na da karfi
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Dele Momodu Hoto: @DeleMomodu
Source: Facebook

ADC za ta iya galaba kan Tinubu da APC

Momodu ya sake jaddada cewa ADC na da kyakkyawan matsayi, ganin cewa daga cikin manyan ’yan takara uku a zaben da ya gabata, jam’iyyar na dauke da biyu – Atiku Abubakar da Peter Obi.

“Wannan ya kamata ya nuna mana cewa idan muka tafiyar da al’amuranmu yadda ya kamata, za mu samu rinjayen kuri’u da za su iya ruguza APC."

- Dele Momodu

Jigon na jam’iyyar ADC ya tabbatar da cewa ’yan adawa na da karfin da zai ba su damar kalubalantar APC a fagen siyasa.

Wanda ya dace da takarar ADC

Kara karanta wannan

Wike ya maida martani ga masu bukatar Tinubu ya tsige shi daga kujerar Ministan Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Dele Momodu ya yi magana kan wanda ya dace ya samu tikitin ADC.

Dele Momodu ya Dele Momodu ya ce Atiku Abubakar ne ya fi dacewa haɗakar ƴan adawa ta tsayar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Fitaccen ɗan jaridar ya bayyana cewa Atiku ya fi sauran masu neman tikitin jam'iyyar haɗaka ƙarfin da zai gwabza da Shugaba Bola Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng