Magana Ta Fito, An Gano Dalilai 3 da Suka Jawo Jinkirin Sauya Shekar Gwamna Abba zuwa APC
- A ranar Litinin, 12 ga watan Janairu, 2026, aka yi tsammanin Gwamna Abba Kabir Yusuf zai fice daga NNPP zuwa APC mai mulkin kasa
- Sai dai wasu majiyoyi masu karfi sun bayyana dalilan da suka jawo jinkirin sauya shekar Gwamna Abba, duk da ya kammala shirye-shirye
- Daga cikin dalilai uku da aka tattaro, akwai sharadin da Shugaba Tinubu ya gindaya wa Abba na zama da masu ruwa da tsaki a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - An yi tsammanin cewa a farkon makon nan, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano zai sauya sheka daga NNPP zuwa APC mai mulkin Najeriya.
Sai dai an samu sababbin bayanai kan dalilan da suka sa aka samu jinkiri game da rade-radin sauya shekar Gwamnan Abba daga jam’iyyar NNPP da ta kai shi mulki.

Source: Facebook
Tattaunawa da masu ruwa da tsakin Kano
Majiyoyi masu tushe sun tabbatar wa jaridar Nigerian Tribune cewa, kusan an kammala dukkan shirye-shiryen sauya shekar, kuma gwamnan ya riga ya yanke shawarar tafiya.
Sai dai majiyoyin sun bayyana cewa Gwamna Abba ya jinkirta shiga APC ne domin kammala tuntubar wasu muhimman masu ruwa da tsaki.
Sharadin da Tinubu ya gindaya wa Abba
Rahotanni sun nuna cewa lokacin da gwamnan ya fara tuntubar fadar shugaban kasa da uwar jam’iyyar APC ta kasa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi shawarar ya koma ya zauna da masu ruwa da tsakin NNPP da na APC a Kano.
A lokacin tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya tafi kasar Saudiyya don gudanar da aikin Umrah.
An ruwaito cewa Ganduje ya nuna goyon bayansa ga shigowar Abba Yusuf cikin APC, domin hakan zai rage karfin tsohon babban abokin hamayyarsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: An bayyana abin da ya jawo sabani tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba
Wani na kusa da Ganduje, Dr. Baffa Dan’agundi, ya tabbatar da cewa shirye-shiryen karbar gwamnan sun yi nisa a matakin kasa da kuma na jiha, cewar rahoton This Day.
Matsalar bangaren Sanata Barau
Baya ga batun Ganduje, wani babban dalilin jinkirin shi ne dambarwar da za ta iya tasowa tsakanin gwamnan da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, wanda ake kyautata zaton yana sha'awar takarar gwamna a 2027.
Tunda Gwamna Abba a zangonsa na farko yake, shigowarsa APC na nufin zai nemi tikitin takara a zango na biyu, wanda hakan na iya yin karo da burin Sanata Barau.

Source: Facebook
"Dole ne a tattauna da Barau Jibrin domin samun nasarar wannan sauya sheka. Ina jin za a nemi ya zauna inda yake (a majalisa), idan Gwamna Abba ya kammala zangonsa na biyu, sai Barau ya karba a 2031," in ji wata majiya.
A halin yanzu, ana ganin dinke barakar da ke tsakanin wadannan manyan jiga-jigai na APC a Kano ne babban abin da ya rage kafin a yi bikin karbar Gwamna Abba Kabir Yusuf a hukumance.
Gwamnatin Kano ta musanta zargin Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta yi martani ga kalaman Rabiu Musa Kwankwaso na cewa ana tilasta wa 'yan Kwankwasiyya su sauya sheka tare da Abba Kabir Yusuf.
Tun farko, Kwankwaso ya bayyana cewa ya samu rahotanni marasa dadi na yi wa mutanensa dole su koma APC, har ma ya ba su dama su yi hakan.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Ibrahim Waiya, ya musanta zargin da Sanata Kwankwaso ya yi, ya ce babu tilas a shirin sauya sheƙa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

