An Fadi Sunayen Kiristoci 3 da Ake So Tinubu Ya Maye Gurbin Shettima da Su

An Fadi Sunayen Kiristoci 3 da Ake So Tinubu Ya Maye Gurbin Shettima da Su

  • An ce ana kara matsa lamba ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu game da tikitin APC gabanin zaɓen 2027, lamarin da ke jawo muhawara a cikin jam’iyya
  • Rahotanni sun ce wasu daga Amurka na neman a yi tikitin Musulmi da Kirista, abin da ya sa ake ta ambaton sunaye daban-daban da za a iya tafiya da su
  • Daga cikin sunayen da ake tattaunawa a kansu akwai Bishop Matthew Hassan Kukah, Yakubu Dogara da sabon Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Rahotanni sun nuna cewa ana kara matsin lamba kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba tsarin tikitin shugaban ƙasa da mataimaki yayin da yake shirin neman tazarce a zaɓen 2027.

Majiyoyi masu ƙarfi sun bayyana cewa wasu daga Amurka sun nuna ra’ayin cewa ya dace Tinubu ya tsaya da tikitin Musulmi da Kirista a 2027.

Kara karanta wannan

Rasha ta shiga rikicin Amurka da Iran, Trump na barazanar kai hari Tehran

Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima
Shugaba Bola Tinubu na gaisawa da Kashim Shettima. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Rahoton Daily Sun ya ce daga cikin sunayen da ke kan gaba akwai Fasto Matthew Hassan Kukah, tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, da kuma Ministan Tsaro, Laftanar Janar Christopher Musa.

Wadanda za su iya canzar Shettima a 2027

Bishop Matthew Hassan Kukah, wanda ya fito daga Jihar Kaduna, na daga cikin wadanda ake cewa sun fi fitowa fili a jerin masu yiwuwar zama mataimakin Tinubu a tikitin APC na 2027.

Haka nan kuma, ministan tsaro, Janar Christopher Musa (Mai ritaya) ma ɗan Kaduna ne, yayin da Yakubu Dogara ya fito daga Jihar Bauchi.

Wadannan fitattun mutane - Malamin addini, tsohon soja da 'dan siyasa sun fito ne daga Kudancin Kaduna da Kudancin jihar Bauchi.

Majiyoyi sun ce tun daga tsakiyar wa’adin wannan gwamnati ake ta rade-radin yiwuwar sauke Mataimakin Shugaban ƙasa na yanzu, Kashim Shettima, daga matsayin abokin takarar Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta ware sama da N1bn don yi wa gidajen Tinubu, Shettima kwaskwarima

Duk da haka, rahoton ya ce yawancin gwamnonin jam'iyyar APC na goyon bayan ci gaba da tafiya da Kashim Shettima a zaben 2027.

Sauyin da aka so kafin maganar Amurka

Rahotanni sun ce kafin matsin lamba daga Amurka, an fara la’akari da sauke Shettima tare da maye gurbinsa da tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, ko kuma Mai ba Shugaban ƙasa Shawara kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu.

Sai dai sabon yanayin matsin lamba ya sa aka fara ganin cewa ci gaba da Shettima ko maye gurbinsa da wani Musulmi na iya fuskantar ƙalubale.

Matsayin da Tinubu zai ba Shettima

A sakamakon haka, majiyar ta ce ana duba wasu hanyoyin ba Shettima wani matsayi ko dama idan har aka cire shi daga tikitin 2027.

Majiyoyi sun bayyana cewa daga cikin abubuwan da ake dubawa bayan 2027 akwai ba Shettima mukamin wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya ko kuma goyon bayan Tinubu domin ya nemi shugabancin ƙasa a 2031.

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima yana wani bayani. Hoto: @KashimSM
Source: Twitter

Tinubu ya yi kira ga sojojin Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana game da kare dimokuradiyya yayin taron ranar tunawa da sojoji ta kasa.

Kara karanta wannan

Wike ya maida martani ga masu bukatar Tinubu ya tsige shi daga kujerar Ministan Abuja

Bola Tinubu ya bayyana cewa sojoji suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen kare kundin tsarin mulkin Najeriya da dimokuradiyya.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan samar da walwalar sojoji da inganta ayyukansu domin su samar da cikakken tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng