Gwamnatin Kano Ta Hango Lam'a a Kalaman Kwankwaso na Tilastawa Masoyansa Koma wa APC
- Gwamnatin Kano ta yi martani ga kalaman Rabiu Musa Kwankwaso na cewa ana tilasta wa 'yan Kwankwasiyya su sauya sheka tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf
- Kwamishinan yada labarai na jihar, Ambasada Ibrahim A Waiya bai musanta cewa an yi yekuwa idan akwai masu son bin Gwamna zuwa jam'iyyar APC ba
- Sai dai a cewar Waiya, babu wani mai rike da mukami ko 'yan siyasa da aka yi wa tilas ko aka masu barazana saboda lallai su bi Abba Kabir Yusuf ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta musanta ikirarin da jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi mata.
A makon da ya gabata ne Kwankwaso ya zargi gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf da tilasta wasu jami’an gwamnati da zababbun shugabannin ƙananan hukumomi tafiya APC.

Kara karanta wannan
Rikicin NNPP: An wanke Gwamna Abba, ba ya bukatar izinin Kwankwaso kafin komawa APC

Source: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa Kwankwaso ya bayyana cewa ya samu rahotanni marasa dadi na yi wa mutanensa dole su koma APC, har ma ya ba su dama su yi hakan.
Zargin da Kwankwaso ya yi wa Abba
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kwankwaso ya koka game da abin da ya kira tirsasa wa 'yan Kwankwasiyya, zababbu da wadanda aka nada mukamai su koma APC.
A cewarsa:
“Na samu rahotanni da dama, wasu masu kyau, wasu kuma masu matuƙar tayar da hankali da ke nuna cewa gwamnatin Kano na tilasta WA jami’ai da shugabannin ƙananan hukumomi su sa hannu kan takardu domin goyon bayan Gandujiyya ko Kwankwasiyya.”
Ya shawarci waɗanda ake tilastawa da su bi umarnin idan lamarin ya zama dole, domin kauce wa tsangwama ko fuskantar kalubale daga gwamnati.
Gwamnati ta musanta zargin Kwankwaso
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Ibrahim Waiya, ya musanta zargin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wa gwamnati a ranar Laraba 14 ga watan Janairu, 2026.

Source: Facebook
Waiya ya ce babu tilas a cikin shirin sauya sheƙa. Ya bayyana cewa jam’iyyar APC na gayyatar duk wanda ke son shiga cikinta ne kawai, ba wai jami’an gwamnati kaɗai ba.
A cewarsa:
“Abin da ya faru shi ne jam’iyyarmu na kiran duk wanda yake da niyyar shiga APC ya yi hakan da kansa. Babu wanda ake tilastawa, sabanin abin da ake yaɗawa.”
Zargin ya zo ne a daidai lokacin da ake ta yaɗa jita-jitar cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin ficewa daga NNPP zuwa APC gabanin zaɓen gaba.
Duk da cewa Gwamna Yusuf bai fito fili ya tabbatar da shirin sauya sheƙa ba, makusantansa da dama sun nuna alamu a kalamansu cewa akwai maganar.
Mataimakin Gwamna ya bi Kwankwaso?
A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya fara nuna inda siyasarsa ta karkata a rikicin da ke tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwankwaso.
An hangi Kwamared Gwarzo ne a gidan Kwankwaso da ke titin Miller a Kano, inda ya kai masa ziyara a ranar Laraba. Ziyarar ta jawo hankalin jama’a, musamman ganin halin da siyasar jam’iyyar NNPP.
Kwankwaso, wanda shi ne jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya karɓi Mataimakin Gwamnan tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar da magoya baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

