"Wannan Siyasar ba a Zaƙalƙale Mata:" Kwankwaso Ya Bi Ta kan Yaran Abba

"Wannan Siyasar ba a Zaƙalƙale Mata:" Kwankwaso Ya Bi Ta kan Yaran Abba

  • Jagoran NNPP na kasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi gargadi ga makusantan Gwamna Abba Kabir Yusuf a Dawakin Tofa
  • Ya ce siyasa tafiya ce mai dogon zango, ba a zaƙalƙale ta da gaggawa da rashin kunya matukar ana so a kai ga tudun mun tsira
  • Darakta Janar kan yada labarai tare da Shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, Anas 'dan Maliki na gaba-gaba a batun sauya shekar Abba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jagoran NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya aika saƙon gargadi ga wasu matasan 'yan siyasa da ke taso wa a karamar hukumar Dawakin Tofa.

Gargadin na zuwa a yayin da Sanusi Bature Dawakin Tofa da Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa, Anas Mukhtar Bello Danmaliki ke nuna goyon baya karara ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Zafin siyasa bai hana aiki: Abba ya fadi shirin gwamnati a kan matasa 50, 000 a Kano

Kwankwaso ya ja kunnen 'yan siyasa a Dawakin Tofa
H-D: Sanusi Bature D-Tofa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, Anas Mukhtar Bello 'Dan Maliki Hoto: Comr Ammar Sarkin Yaki
Source: Facebook

A bidiyon da AbdulAziz Na'ibi Abubakar ya wallafa a shafin X, an ji Kwankwaso ya koya wa jiga-jigai a gwamnatin Abba yadda ake siyasa har a sharbi romonta.

Kwankwaso ya aika sako da 'yan Dawakin Tofa

A cewar Kwankwaso, akwai bukatar ’yan siyasa, musamman matasa, su yi taka-tsantsan wajen tafiyar da suka tsinci kansu a ciki.

Ya bukaci a isar da saƙonsa ga yaran siyasa da ke ganin sun soma tasiri yana mai cewa tafiyar siyasa ba ta gaggawa ba ce.

Kwankwaso ya jaddada cewa har manya a Dawakin Tofa sun taɓa yin kuskure saboda hanzari, don haka matasa su yi koyi da darasi.

ʼKu gaya wa ƴan siyasar ku yara, su riƙa bi a hankali saboda wannan tafiyar manya ma na Dawakin Tofa sun buga kansu a bango".
"Ku gaya wa yara matasa wanda su ke ganin sun soma balaga a siyasa, ku gaya wa ƴan Dawakin Tofa suna da darasi da za su koya, wannan tafiyar ba a zaƙalƙale mata".

Kara karanta wannan

Rikicin NNPP: An wanke Gwamna Abba, ba ya bukatar izinin Kwankwaso kafin komawa APC

Kwankwaso ya shawarci yaran yan siyasa

Kwankwaso wanda ya dade ana damawa da shi ya bayyana cewa siyasa tana buƙatar hangen nesa na dogon lokaci, inda mutum ke gina amana da jama’a a hankali.

Kwankwaso ya shawarci matasan yan siyasa
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso yayin jawabi a wani taro Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

A ganinsa, duk wanda ya yi tunanin samun riba cikin gaggawa zai iya fuskantar matsala a gaba. Don haka ya shawarci ’yan siyasa su guji maganganu ko matakai da za su iya raba kai da jama’a.

"In kana neman ka zauna lafiya to ka tafi saisa-saisa, in ka ce za ka zaƙalƙale ka yi rashin kunya magana ce ta lokaci.

Gargadin Kwankwaso na zuwa ne bayan wasu daga cikin makusantan Gwamna Abba Kabir Yusuf suna uwa da makarbiya game da batun sauya sheka zuwa APC.

Sunusi Bature da Anas Danmaliki na daga cikin jiga-jigan ɓangaren wamna da suka fara fitowa fili domin bayyana matsayar bangarensu da goyon bayansu.

Dawakin Tofa dai ita ce karamar hukumar tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda har yanzu ke takun saka irinta da suyasa da Kwankwaso - tsohon ubangidansa a siyasar Kano.

Kara karanta wannan

Da gaske Kwankwaso ya goyi bayan Abba Kabir zuwa APC? NNPP ta fayyace gaskiya

Abbai bai butulce wa Kwankwaso ba - Gwamnati

A baya, kun samu labarin cewa Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya kare Gwamna Abba Kabir Yusuf daga zargin butulci da ake ganin ya yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A cewarsa, ana yin nazarin siyasa ne domin a tantance amfanin kowanne mataki da ake shirin ɗauka, musamman idan ya shafi makomar jihar Kano da jama’arta, kamar yadda Gwamna ke nazari.

Ya ce duk wani sauyi ko shawara da ake tunanin ɗauka, ana duba tasirinsa ne ga al’umma gaba ɗaya, ba wai don faranta wa kashin kai ba, kuma yana ganin akwai hikima a batun canja jam'iyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng