Rikicin NNPP: An Wanke Gwamna Abba, ba Ya Bukatar Izinin Kwankwaso kafin Komawa APC

Rikicin NNPP: An Wanke Gwamna Abba, ba Ya Bukatar Izinin Kwankwaso kafin Komawa APC

  • Tsagin NNPP ya soki tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso kan batun sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Sakataren tsagin NNPP na kasa, Ogini Olaposi ya ce Gwamma Abba na da 'yancin sauya sheka zuwa kowace jam'iyya idan ya ga dama
  • Olaposi ya bayyana cewa Gwamna Abba bai ci amanar Rabiu Kwankwaso ba, sakamako ne na abin da ya shuka a siyasarsa ta baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Tsagin NNPP ta kasa ta bayyana cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na da cikakken ikon komawa jam’iyyar APC ko wata jam’iyya daban idan ya ga dama.

A cewar tsagin jam'iyyar NNPP, Gwamna Abba na da 'yancin yafiya APC ba tare da ya nemi amincewar ubangidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba.

Kara karanta wannan

Da gaske Kwankwaso ya goyi bayan Abba Kabir zuwa APC? NNPP ta fayyace gaskiya

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na jawabi a wurin taro Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamna Abba na bukatar izinin tafiya APC?

Jam’iyyar ta kuma jaddada cewa ko zama zai ci gaba da yi a NNPP, gwamnan ba ya bukatar wani babban jagora ya ba shi izini, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Wannan martani na zuwa ne bayan wata sanarwa da kakakin NNPP na bangaren Kwankwaso, Ladipo Johnson ya fitar, inda ya karyata rahotannin cewa Kwankwaso ya amince da shirin Abba na sauya sheka zuwa APC.

A rahoton TVC News, Johnson ya zargi wasu mutane da kokarin ruda jama’a kan matsayar Kwankwaso game da rade-radin ficewar gwamnan daga NNPP.

Martanin tsagin jam’iyyar NNPP

Da yake magana a Legas ranar Litinin, sakataren tsagin NNPP na kasa, Ogini Olaposi, ya bayyana cewa a matsayin Abba na gwamna daya tilo kuma jagoran jam’iyyar, kundin tsarin mulki ya ba shi damar yanke hukunci kan makomarsa ta siyasa.

“Duk da cewa muna ba gwamna shawarar ya zauna a NNPP, mun fahimci cewa yana da hakkin shiga kowace jam’iyya da yake so, musamman duba da rigingimun shari’a da suka yi masa katutu,” in ji Olaposi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fadawa ciyamomin Kano abin da za su yi a shirin Abba na shiga APC

Ya ci gaba da cewa NNPP ba ta da wata matsala da kowace jam'iyya ciki har da APC, don haka ba za ta tursasa wa gwamna zama ba idan ya riga ya yanke shawarar tafiya.

Shin Abba ya ci amanar Kwankwaso?

Olaposi ya bukaci Kwankwaso da tafiyar Kwankwasiyya da su daina dauke hankalin gwamnan tare da ba shi sarari ya gudanar da ayyukan alheri da yake yi a Kano.

Game da zargin cin amana da Kwankwaso ya yi wa masu shirin sauya sheka, jam’iyyar NNPP ta mayar da martani da cewa hakan "sakamakon abin da mutum ya shuka ne."

Kwankwaso.
Jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso yana jawabi a taron Kwankwasiyya Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Ta tuna wa Kwankwaso yadda shi ma ya yi kokarin karbe ikon jam’iyyar da ta ba shi damar tsayawa takara kyauta a shekarar 2023.

A karshe, jam’iyyar NNPP ta nanata cewa Kwankwaso ya riga ya zama korarre daga NNPP, kuma za su ci gaba da mara wa Gwamna Abba Kabir Yusuf baya a duk matakin da ya dauka.

Shawarar Kwankwaso ga ciyamomi

A wani rahoton, kun ji cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya ba ciyamomin Kano shawarar sanya hannu kan takardar goyon bayan sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An bayyana abin da ya jawo sabani tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce ya samu kiraye-kirayen waya game da yadda gwamnatin Kano ke tilasta zababbun shugabannin su sanya hannu kan wata takarda.

Jagoran na NNPP ya jaddada cewa masoyansa na nan daram suna.jiran zaben 2027 domin nuna karfin Kwankwasiyya a Kano da kasa baki daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262