Dabaru 2 da Ministan Buhari Ya Yi da Suka Jawo Nasarar Tinubu a 2023

Dabaru 2 da Ministan Buhari Ya Yi da Suka Jawo Nasarar Tinubu a 2023

  • Tsohon Ministan yaɗa labarai, Lai Mohammed, ya bayyana dabarun da ya ce sun taimaka wa jam’iyyar APC da Bola Ahmed Tinubu samun nasara a zaben 2023
  • Ya ce ya yi amfani da wata dabara mai bangarori biyu ba tare da shiga gangamin siyasa kai tsaye ba, duk da gargadin da aka yi wa ministoci a wancan lokacin
  • Lai Mohammed ya ce mayar da hankali kan nasarorin gwamnati da karyata jita-jitar 'yan adawa ne suka sauya yanayin kamfen din da aka yi a lokacin zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana yadda ya taka rawa wajen taimaka wa jam’iyyar APC da Bola Ahmed Tinubu samun nasara a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Borno: Tsohon ɗan takarar gwamna ya yi watsi da PDP, ya rungumi ADC gabanin 2027

Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a cikin wani littafi da ya wallafa kwanan nan, inda ya yi bayani dalla-dalla kan irin rawar da ya taka a lokacin kamfen din zaben 2023.

Lai Mohammed da shugaba Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu da Lai Mohammed. Hoto: Bayo Onanuga|Bashir Ahmed
Source: Facebook

The Guardian ta rahoto ya ce ya yi aikin ne duk da gargadin da marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa ministoci da manyan jami’an gwamnati da kada su bar ayyukansu su tsunduma siyasa.

Ya ce duk da wannan umarni, bai karya doka ba, domin bai shiga gangamin siyasa ko rura wutar jam’iyya ba, sai dai ya kare ayyukan gwamnati da gaskiya ta hanyar bayanai da hujjoji.

Dabaru 2 da Lai Mohammed ya yi a 2023

Lai Mohammed ya ce kafin zaben 2023, 'yan adawa sun yi ta yada ra’ayin cewa gwamnatin APC karkashin Muhammadu Buhari ba ta cimma komai ba, don haka babu abin da zai sa jam’iyyar ta sake samun mulki.

A cewarsa, wannan ra’ayi ba gaskiya ba ne, illa wata dabara ta siyasa domin raunana jam’iyyar APC da kuma rage karfin Bola Ahmed Tinubu a idon jama’a.

Tsohon ministan ya ce ya fahimci hadarin irin wannan labari, shi ya sa ya dauki matakin mayar da martani ta hanyar tsari mai bangarori biyu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kashe Naira biliyan 40 a zamanantar da gadar Legas da CCTV

Ya ce dabarar farko ita ce fito da nasarorin gwamnatin Buhari a fili, sannan ta biyu ita ce karyata bayanan da 'yan adawa ke yadawa ta hanyar baje hujjoji.

Lai Mohammed ya jaddada cewa bai yi amfani da maganganu ko zarge-zarge ba, sai dai bayanai masu tushe da hujjoji game da ayyukan da aka yi.

Me ya jawo cin zaben Tinubu a 2023?

Lai Mohammed ya ce a lokacin da ya rage kwanaki 130 kafin babban zaben, ma’aikatarsa ta kaddamar da wani shiri na musamman domin bayyana nasarorin gwamnatin Buhari daga 2015 zuwa 2023.

Vanguard ta wallafa cewa tsohon ministan ya ce a karkashin shirin, kowane minista ya gabatar da bayanin abin da ma’aikatarsa ta cimma.

Ya ce an bai wa ‘yan jarida da jama’a damar yin tambayoyi kai tsaye, domin tabbatar da sahihancin bayanan da ake gabatarwa. Wannan tsari, a cewarsa, ya sa jama’a suka samu cikakken bayani kan ayyukan gwamnati ba tare da rufa-rufa ba.

Lai Mohammed da shugaba Muhammadu Buhari
Tsohon minista, Lai Mohammed da Muhammadu Buhari. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Twitter

Kafin zabe ya kammala, Lai Mohammed ya ce an kara fito da wasu bayanan ayyukan gwamnati, ciki har da bayanai na rubuce da na bidiyo, tare da kafa wata hanyar intanet da ke adana dukkan wadannan bayanai.

Kara karanta wannan

Lai Mohammed ya fadi yadda tsohon minista ya munafurce shi a gaban Buhari

A cewarsa, wannan dabara ta sauya yanayin kamfen din siyasa baki daya, domin ta tilasta wa 'yan adawa komawa matsayin masu kare kansu maimakon caccakar APC, wanda hakan ya kara ba Tinubu karbuwa.

Ana so Tinubu ya maido El-Rufa'i

A wani labarin, mun kawo muku cewa an fara kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya dawo da Nasir El-Rufa'i jam'iyyar APC.

Jigo a APC a Arewa maso Yamma, Salihu Isa Nataro ne ya yi kira ga shugaban kasar, inda ya ce El-Rufa'i zai taimaka masa sosai a 2027.

Nataro ya ce babu manyan APC da za su iya tsayuwa tsayin daka domin tabbatar da shugaban kasa ya samu nasara yadda ya kamata a Arewa maso Yamma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng