Da Gaske Kwankwaso Ya Goyi Bayan Abba Kabir zuwa APC? NNPP Ta Fayyace Gaskiya

Da Gaske Kwankwaso Ya Goyi Bayan Abba Kabir zuwa APC? NNPP Ta Fayyace Gaskiya

  • NNPP ta yi karin haske kan jita-jitar cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya goyi bayan shirin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na koma APC
  • Tuni jam'iyyar hamayyar ta NNPP ta ce an sauya kalaman Sanata Kwankwaso ne domin halatta shirin sauya sheƙar wasu ’ya 'yanta
  • Jam’iyyar ta kalubalanci Gwamna Abba Yusuf da magoya bayansa da su fice ba tare da amfani da sunan jagoransu wato Kwankwaso ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Jam’iyyar NNPP ta mayar da martani kan rahotannin da ake yadawa wai Rabiu Kwankwaso ya amince da mara bayan ga sauya shekar Abba Kabir Yusuf.

Jam'iyyar ta ƙaryata labarin inda ta ce kwata-kwata an juya kalaman jagoran Kwanwasiyya ne amma ba haka yake nufi ba.

'Babu inda Kwankwaso ya goyi bayan Abba a koma APC'
Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Kwankwaso. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

NNPP ta soki masu yada karya kan Kwankwaso

Hakan na cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na NNPP na Ƙasa, Ladipo Johnson, ya fitar a daren Talata 13 ga watan Janairun 2026 a Abuja, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fadawa ciyamomin Kano abin da za su yi a shirin Abba na shiga APC

Jam’iyyar ta yi wannan martani ne kan wani rahoto da kafar yaɗa labarai ta Premium Times ta wallafa, wanda ya nuna cewa Rabiu Kwankwaso ya shawarci magoya bayansa su yi aiki tare da APC, a daidai lokacin da ake rade-radin cewa Gwamna Yusuf na shirin barin NNPP.

Sai dai Ladipo ya bayyana rahoton a matsayin “ƙarya mafi muni” yana zargin wasu ’yan siyasa da karkatar da kalaman Kwankwaso domin wata manufarsu.

Johnson ya ce wannan ce-ce-ku-ce ta bayyana irin matsanancin yunƙurin wasu mambobin jam’iyyar da ake zargin suna shirin ficewa daga NNPP, yana mai jaddada cewa matsayar Kwankwaso kan batun a bayyane take kuma ba ta sauya ba.

Ya zargi masu hannu a lamarin da yaudarar jama’a da kuma ƙoƙarin yi wa jagoran jam’iyyar baƙar fata ta siyasa, yana mai cewa karkatar da kalamansa domin ruɗar jama’a abin kunya ne da rashin gaskiya.

Kakakin jam’iyyar ya kalubalanci Gwamna Abba Yusuf da magoya bayansa da su fice daga jam'iyyar NNPP idan hakan ne burinsu, ba tare da ɓoye kansu a bayan sunan Kwankwaso ba.

Ya ce:

“Idan kun yanke shawarar barin jam’iyyar, ku tafi. Idan kuna ganin kuna da goyon bayan jama’a kuma kuna tafiya zuwa wuri mafi alheri, ku tafi kai tsaye.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP ta zabi na zaba tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba

“Kada ku yaudari jama’a da cewa kuna da goyon baya ko albarkar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.”
NNPP ta kare Kwankwaso game da rigimar siyasar Kano
Jagoran siyasar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Abin da Rabiu Kwankwaso ke nufi

Johnson ya jaddada cewa Kwankwaso ya bayyana shirin da ake zargin gwamnan da wasu mambobin Kwankwasiyya ke yi na sauya sheƙa a matsayin cin amanar amincewa da mutanen Jihar Kano suka ba su.

A cewarsa, tsohon Gwamnan Kano ya fi damuwa da rage zafin rikicin siyasa a jihar fiye da shiga fafatawar siyasa ta barazana da ruɗani.

Sanarwar ta ce Kwankwaso ya bayyana cewa waɗanda ake matsa musu lamba su sauya sheƙa suna da ’yancin tafiya, yana mai cewa zaɓen shekarar 2027 zai zo ya wuce, kuma al’ummar Kano za su yi hukunci kan masu cin amana.

An fadi dalilin sabanin Abba da Kwankwaso

An ji cewa alamu sun nuna dangantaka ta yi tsami tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da ubangidansa a siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Hakan na zuwa ne yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke ci gaba da shirin sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki a Najeriya.

Wata majiya ta bayyana cewa buri na siyasa ya taka rawar gani wajen kawo sabani tsakanin madugun Kwankwasiyya da Gwamna Abba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.