'Tsari Mai Kyau,' Jigon ADC Ya Fadi yadda Za a Cire Tinubu daga Aso Rock a 2027
- Wani jigon ADC, Dele Momodu ya ce jam'iyyar ADC tana kan sake fasalin gudanarwarta domin kifar da Shugaba Bola Tinubu a 2027
- Momodu ya jaddada cewa hadewar Atiku Abubakar da Peter Obi a karkashin ADC zai samar da miliyoyin kuri'un da zasu doke APC
- Jigon na ADC ya bukaci yan adawa su yi amfani da tsari mai kyau domin tabbatar da cewa sun samu shugabancin kasa a zabe mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wani babban jigo a ADC, Dele Momodu, ya bayyana cewa jam’iyyarsu tana kan sake fasalinta domin zama dandalin da ya fi cancanta 'yan Najeriya su zaba a shekarar 2027.
Momodu ya jaddada cewa za a iya doke Shugaba Bola Tinubu da jam'iyyar APC idan har 'yan adawa sun hada kai tare da amfani da dabarun siyasa na kwarai.

Source: Twitter
Dele Momodu ya fadi amfanin jam'iyyar ADC
A wata hira da gidan talabijin na Arise News a ranar Litinin, 12 ga Janairu, 2025, Momodu ya bayyana cewa jam’iyyar ADC ta dukufa a gyara kundin tsarin mulkinta.
A cewar babban dan siyasar, ADC ta kuma dage wajen gina hadaka da sauran jam'iyyun siyasa domin kauce wa kura-kuran da suka taba faruwa a baya.
Ya ce, Najeriya na bukatar jam’iyya mai dattako da ta bambanta da APC, inda ya bayyana cewa, yanzu haka kasar tana bukatar garambawul a cikin gaggawa.
Daya daga cikin manyan makaman da Momodu ya nuna jam’iyyar ADC ke da shi a yanzu, shi ne kasancewar ta mallaki 'yan takarar shugaban kasa na zaben 2023.
Karfin hadaka: Atiku Abubakar da Peter Obi
Ya ce duk jam’iyyar da ta samu damar hada kan Atiku Abubakar da Peter Obi a waje guda, wanda ya ce hakan zai zama babban kalubale ga jam’iyya mai mulki.
"Duk wanda ya raina jam’iyyar da take da Atiku Abubakar da Peter Obi, to ya yi hakan ne domin kansa. Idan ka hada kuri’unsu, za ka ga cewa kuri’u ne masu yawa," inji Dele Momodu.
Game da batun wanda zai tsaya takara tsakanin Atiku, Peter Obi, da kuma Rotimi Amaechi, Momodu ya ce gasa abu ne da ba za a iya kauce masa ba a dimokuradiyya.
Sai dai, ya bayyana ra'ayinsa na kashin kansa cewa Atiku Abubakar ne yafi dacewa sakamakon kwarewarsa, sanin harkokin duniya, da kuma iya lissafin siyasa.

Source: Getty Images
Lissafin 'yan adawa gabanin 2027
Momodu ya yi gargadi cewa zaben 2027 zai dogara ne kan lissafin alkaluma, wadanda suka hada da:
- Kabilanci: Momodu ya ce kabilanci zai zama babban abin la'akari a zaben 2027 domin kowane yanki na kukan an ware shi.
- Shekaru: Momodu ya kare Atiku kan maganar shekaru, inda ya ce babu bambanci sosai tsakanin shekarun Atiku da na Shugaba Tinubu.
- Rarraba mulki: Momodu ya jaddada cewa babu inda kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce dole mulki ya rika zagayawa bayan shekaru takwas.
A karshe, Momodu ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ba mutum ne da za a iya kayarwa cikin sauki ba, don haka ana bukatar gogaggun ‘yan siyasa wadanda aka taba gwada wa aka gani domin tunkararsa.
Kalli hirar a nan kasa:
'Wanda ya dace ADC ta ba takara' - Momodu
Tun da fari, mun ruwaito cewa, jigon ADC, Dele Momodu ya ce Atiku Abubakar ne ya fi dacewa haɗakar ƴan adawa ta tsayar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Fitaccen ɗan jaridar ya bayyana cewa Atiku ya fi sauran masu neman tikitin jam'iyyar haɗaka ƙarfin da zai gwabza da Shugaba Bola Tinubu.
Momodu, wanda ya taɓa neman tikitin takarar shugaban ƙasa ya roki magoya bayan Obi da Amaechi, su goyi bayan ɗan takararsu cikin lumana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


