Manyan 'Yan Siyasa 5 da Nyesom Wike ke Gwabza Rikici da Su a Najeriya
Tun bayan zaben shugaban kasa na 2023 masana siyasa ke cewa tsohon gwamnan Rivers ya fara fitowa karara yana rikici da manyan 'yan siyasa a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Masu bibiyar al'amura na ganin Ministan Abuja, Nyesom Ezonwo Wike yana rigima da manyan 'yan siyasa daga jam'iyyun PDP da APC.
Rikicin Nyesom Wike da manyan 'yan siyasa masu rike da madafun iko ya dauki hankalin jama'a da dama a fadin Najeriya, musamman a baya bayan nan.

Source: Facebook
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku jerin manyan 'yan siyasa da suke buga rikici da Nyesom Wike tun bayan zaben 2023.
1. Rikicin Nyesom Wike da Gwamna Simi Fubara
Sabanin gwamna Rivers, Siminalayi Fubara da Nyesom Wike na cikin rikici mafi girma da ministan Abuja ke gwabzawa tun bayan zaben 2023.
Fubara ya kasance ɗan siyasar da Wike ya tallafa masa har ya zama magajinsa, amma dangantakarsu ta lalace bayan rantsar da shi.
Rikicin ya haifar da yunƙurin tsige Fubara daga muƙaminsa a baya, tare da sake tasowa a 2026, baya ga rikice-rikicen Majalisar Dokokin jihar da suka janyo rarrabuwar kai.
Haka kuma, Punch ta wallafa cewa rikicin ya tilasta shiga tsakani daga matakin tarayya, ciki har da ayyana dokar ta-baci a 2025 domin shawo kan tabarbarewar al’amura.

Source: Instagram
Duk da sulhu da aka musu, a tsawon wannan lokaci, bangarorin biyu sun riƙa musayar kalamai a bainar jama’a, tare da ɗaukar matakai masu tsauri.
A yanzu haka, rahotanni sun nuna cewa Wike na kokarin hana Fubara sake samun tikitin tsayawa takarar gwamna a zaɓen 2027.
2. Tsohon fadan Wike da Rotimi Amaechi
Dangane da tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, akwai dogon rikici tsakanin sa da Ministan Abuja, Nyesom Wike.
A lokuta da dama, Wike kan soki burin Amaechi na zama shugaban kasa, yana danganta shi da gazawa ko rashin tushe a siyasar Rivers.

Source: Twitter
A martanin da ya ke yawan yi, Ameachi ya na nuna shi mai gidan Wike ne, lura da cewa sai da ya sauka a mulki kafin ministan ya biyo shi a baya.
A lokacin Amaechi yana gwamna ne ya yi wa magajin nasa hanyar zama Ministan Goodluck Jonathan, Vanguard ta tabo kawo labarin nan a 2013.
3. Wike ya soki Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed
Nyesom Wike ya kuma samu sabani da gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, rikici da ya ƙara fito da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar PDP a matakin ƙasa.
Rikicin ya bayyana ne a bainar jama’a lokacin da Bala Mohammed ya zargi Wike da haddasa rikici a Jihar Bauchi tare da ƙoƙarin tayar da fitina a cikin tsarin jam’iyyar PDP a wata hira da ya yi da Channels TV.

Source: Facebook
Gwamnan Bauchi ya ce Wike na ƙara rarrabuwar kawuna a jam’iyyar, musamman a lokacin da PDP ke ƙoƙarin sake tsari da ƙarfafa haɗin kai bayan zaɓuka.
A martanin da ya yi, Wike ya ce Bala Mohammed ne ya fara tsoma baki a harkokin siyasar Jihar Rivers, duk da cewa ya taba gargadin shi tun da wuri da ya nisanci harkokin siyasar jiharsa.
4. Dangantakar Gwamnan Oyo da Wike ta watse
Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya shiga jerin manyan ’yan siyasar PDP da suka samu sabani da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, a rikicin cikin gida da ke ci gaba da girgiza jam’iyyar.
Rikicin ya bayyana ne a bainar jama’a lokacin da Makinde ya zargi Wike da cewa ya taɓa yin alƙawarin riƙe jam’iyyar PDP ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Facebook
Sai dai Wike bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen mayar da martani. Ya yi kakkausar suka ga Makinde, yana musanta zargin gaba ɗaya tare da cewa bai taɓa yin alƙawarin hakan ba.
5. Musayar yawun Wike da Sakataren APC
Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike, ya buga rikici da Sakataren Jam’iyyar APC na ƙasa, Ajibola Basiru, kan siyasar Jihar Rivers da ke ci gaba da ɗaukar hankalin jama’a.
Rikicin ya ɓarke ne bayan Basiru ya yi magana kan halin da siyasa ke ciki a Rivers, lamarin da Wike ya nuna rashin jin daɗinsa tare da gargadin cewa bai kamata ya tsoma baki a batun da bai shafe shi kai tsaye ba.

Source: Twitter
Sai dai Ajibola Basiru bai ja da baya ba, inda ya mayar da martani da cewa a matsayinsa na sakataren APC na ƙasa, yana da cikakken ’yancin yin magana kan harkokin jam’iyyar a kowace jiha ta ƙasar nan, ciki har da Rivers.
Ya kuma ƙalubalanci Wike da ya ajiye muƙaminsa na Ministan Abuja idan da gaske yana son yin siyasa, ya dawo Rivers ya fuskanci abokan hamayyarsa a fili.
Dalilin rikicin Wike da Fubara a Rivers
A wani labarin kun ji cewa sabon rikici ya kara barkewa tsakanin gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Wike bayan Bola Tinubu ya musu sulhu.
Wata majiya ta bayyana cewa maganar kasafin kudi da Fubara ya ki amincewa da ita na cikin manyan abubuwan da suka tayar da rikicin.
Baya ga haka, an ce maganar sake takarar Fubara karo na biyu a 2027 na cikin abubuwan da suka harzuka Wike, inda ya ce hakan ba zai yiwu ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



