Kwankwaso na Fuskantar Babbar Matsala a Siyasa, Ya Fara Rasa Farin Jini a Kano

Kwankwaso na Fuskantar Babbar Matsala a Siyasa, Ya Fara Rasa Farin Jini a Kano

  • Farin jinin jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Injiniya Rabiu Kwankwaso da mabiyansa ya fara dusashewa a siyasar jihar Kano
  • Kungiyar KPRA ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da shugabanta, Isyaku Lawal Tofa ya fitar kan kan rade-radin sauya shekar gwamnan Kano
  • KPRA ta yi kira ga mambobin jam'iyyar NNPP da mabiyan Kwankwaso su zauna su yi tunani kan irin siyasar da maigidansu ke yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Wata kungiya mai rajin kare hakkin al’ummar Kano (KPRA), ta bayyana cewa farin jinin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwasoa siyasa ya ragu matuka.

Kungiyar ta ce a yanzu Rabiu Musa Kwankwaso da mabiyansa 'yan tafiyar Kwankwasiyya sun fara fita da zukatan jama'a a jihar Kano.

Kwankwaso.
Tsohon 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

A rahoton This Day, kungiyar ta bayyana cewa al'amuran da ke faruwa a siyasar Kano kwanan nan sun kara fito da rigingimun cikin gida da ke addabar jam'iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP ta zabi na zaba tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba

Wane koma-baya Kwankwaso ya samu?

Haka zalika, KPRA ta ce rikicin siyasar Kano wata alama ce da ke nuna yadda ikon Kwankwaso da magoya bayansa a kan al’amuran jihar yake dusashewa.

KPRA ta yi wannan furucin ne bayan bayyanar Gwamna Abba Kabir Yusuf a bainar jama'a, a daidai lokacin da ake ta rade-raden cewa yana shirin sauya sheka daga NNPP zuwa APC.

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Isyaku Lawal Tofa, ya fitar, ya bayyana cewa rashin halartar mukarraban Kwankwaso taron gwamnan ya nuna yadda suka ware kansu.

KPRA ta soki salon siyasar Kwankwaso

Tofa ya ce zamanin da Kwankwaso ke juya akalar siyasar Kano ya zama tarihi, domin gwamnatin Abba tana da ikon tafiyar da jihar ba tare da katsalandan ba.

Kungiyar ta siffanta salon siyasar Kwankwaso a matsayin wadda ta ginu a kan nuna karfi da danniya, kuma a cewarta, hakan ba alheri ba ne, cewar Daily Post.

KPRA ta nuna gamsuwarta da ganin Shugaban Majalisar Jiha, Rt. Hon. Ismail Jibril Falgore, da Sakataren Gwamnati, Umar Farouk Ibrahim, a tare da gwamnan, tana mai cewa hakan yana nuna hadin kai ga manufofin Abba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya kara kaimi wajen shawo kan jama'a, Abba na shirin shiga APC

Gwamnan Kano, Abba Kabir.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf tare da mukarrabansa a wurin taro a gidan gwamnati Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

An ba 'yan jam'iyyar NNPP shawara a Kano

Kungiyar ta yi kira ga mambobin NNPP, musamman masu yi wa tsohon gwamnan biyayya, da su tsaya su yi tunani, sannan su sanya muradin al’ummar Kano a gaba fiye da son kansu.

"Lokacin da za mu canza tunani ya yi, mutanen Kano sun cancanci shugabanni wadanda za su sanya jin dadinsu a gaba maimakon son kansu ko na kungiya," in ji Isyaku Lawal Tofa

A karshe, KPRA ta jaddada cewa lokaci ya yi da salon siyasar Kano zai sauya, inda ta ce ruguza tasirin Kwankwaso tamkar "hutu ne ga al'umma" domin shimfida kyakkyawan shugabanci.

Me ya jawo sabanin Abba da Kwankwaso?

A wani rahoton, kun ji cewa alamu sun nuna cewa dangantaka ta yi tsami tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da ubangidansa a siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Wasu bayanai sun nuna cewa Abba da Kwankwaso sun fara samun sabani ne kan batun wanda zai yi takarar gwamnan Kano karkashin inuwar NNPP a 2027.

Wata majiya ta ce gwamnan zai fice daga NNPP zuwa jam’iyyar APC ne domin cimma burinsa na sake tsayawa takarar gwamna karo na biyu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262