Ihedioha: Jam'iyyar ADC Ta Kara Karfi yayin da Tsohon Gwamna Ya Shiga cikinta
- Jam'iyyar ADC ta kara samun tagomashi a yankin Kudu maso Gabas na Najeriya bayan shigowar tsohon gwamna zuwa cikinta
- Tsohon gwamnan jihar Imo, Rt. Hon. Emeka Ihedioha ya yi rajista a hukumance a jam'iyyar ADC wadda ke adawa a Najeriya
- Emeka ihedioha ya bayyana cewa Najeriya da jiharsa ta Imo na bukatar shugabanci da zai mayar da hankali kan muradun jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Imo - Tsohon gwamnan jihar Imo, Rt. Hon. Emeka Ihedioha, ya shiga jam’iyyar ADC a hukumance.
Emeka Ihedioha ya kammala rajistarsa a jam'iyyar ADC a ranar Litinin, 12 ga watan Janairu, 2026, a mazabar Mbutu, da ke karamar hukumar Aboh-Mbaise ta jihar Imo.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa an ba tsohon gwamnan katin zama mamban jam’iyyar ADC mai lamba 001.
Emeke Ihedioha ya zama mamba a ADC
Sakataren ADC a mazabar, Prince Obinna Opara, ne ya gudanar da rajistar, yayin da shugabanta a mazabar, Chief Alex Ahamuefula, ya mika masa katin zama mamba.
Shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki, da shugabannin al’umma, ciki har da Evangelist Dr. Obi Nwaigwe, Magajin Garin Mbutu, da Hon. Jonathan Egbule, shugaban karamar hukumar Aboh-Mbaise, da sauran jama’a sun halarci wurin.
Me Ihedioha ya ce kan shigarsa ADC?
Da yake jawabi bayan kammala rajistar, Ihedioha ya ce shigarsa jam’iyyar ADC ba ta zo a bazata ba, illa bisa amanna da ka’idojin jam’iyyar na gaskiya, tsayayyun manufofi, da yi wa jama’a hidima.
Ya ce Najeriya da jihar Imo na bukatar shugabanci da ke mayar da hankali kan muradun jama’a, tare da gudanarwa mai sauraron koke da bukatun al’umma, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar da hakan.
“Al’ummarmu na bukatar shugabanci da ke sauraro, yin hidima, kuma da ke fifita moriyar kowa sama da son zuciya. Na gamsu cewa jam’iyyar ADC na bayar da ingantaccen dandali domin cimma wadannan manufofi."
- Emeka Ihedioha
Ihedioha ya kara da cewa rajistarsa a matakin mazaba na nuna tsayuwarsa kan siyasar tushe inda nan ne asali.
Shugabannin jam'iyyar ADC sun yi masa maraba
Daga bangaren shugabannin kasa na jam’iyyar da suka halarta akwai mataimakin shugaban ADC na kasa (shiyyar Kudu maso Gabas), Sir Bon Unachukwu, da shugaban kungiyar tsofaffin ’yan majalisu ta Najeriya, Uko Nkole.

Source: Facebook
Sir Bon Unachukwu ya bayyana shigar Ihedioha jam’iyyar a matsayin babban karin karfi ga ADC a shiyyar Kudu-Maso-Gabas da ma kasa baki daya, yana mai cewa jam’iyyar ta yi maraba da tsohon gwamna kuma gogaggen ma’aikacin gwamnati.
Shugaban ADC na jihar Imo, Farfesa James Okoroma, tare da mambobin kwamitin zartarwa na jiha, ne suka tarbi tsohon gwamnan tare da shaida rajistar da aka yi masa.
Da yake maraba da shi a madadin jam’iyyar, Farfesa Okoroma ya ce shigowar Ihedioha ya kara karfin ADC a jihar Imo, tare da jaddada kudurin jam’iyyar na dimokuradiyya a cikin gida da kuma karfafa siyasar tushe.
Batun 'dan takarar jam'iyyar ADC a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyaf ADC ta yi magana kan jita-jitar cewa ta tsayar da wanda za ta tikitin takara a zaben 2027.
Jam’iyyar ADC ta yi fatali da jita-jitar da ake yaɗawa cewa ta riga ta tsaida ɗan takarar shugaban ƙasa da zai fafata mata a zaɓen 2027.
ADC ta ce bai kamata a fassara turuwar da ’yan siyasa ke yi zuwa jam’iyyar a halin yanzu a matsayin wata yarjejeniya ta sirri kan wanda zai riƙe tutar jam’iyyar ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


