PDP Ta Shiga Tsilla Tsilla, Sanata Ya Yi Murabus daga Jam'iyyar

PDP Ta Shiga Tsilla Tsilla, Sanata Ya Yi Murabus daga Jam'iyyar

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta samu koma baya bayan ta rasa daya daga cikin sanatocin da ke da su a majalisar dattawa
  • Sanata Ogoshi Onawa mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Kudu ya sanar da yin murabus dinsa daga jam'iyyar PDP maras rinjaye
  • Ogoshi Onawo ya bayyana dalilan da suka sanya ya raba gari da jam'iyyar PDP duk kuwa da damar da ta ba shi ya yi takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Nasarawa - Sanatan da ke wakiltar mazabar Nasarawa ta Kudu a Majalisar dattawa, Ogoshi Onawo, ya yi murabus daga jam'iyyar PDP.

Sanata Ogoshi Onawo ya bayyana cewa murabus dinsa daga jam'iyyar PDP ya fara aiki ne nan take.

Sanata Ogoshi Onawo ya yi murabus daga PDP
Sanata Ogoshi Onawo a zauren Majalisar dattawa Hoto: Rt Comr Mustapha
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Sanata Onawo ya sanar da matakin nasa ne ta hanyar wata wasikar murabus mai dauke da kwanan wata 10 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

An kira sunan Atiku da aka lissafa 'yan siyasar da suka 'ruguza' jam'iyyar PDP

Sanata Onawo ya bar jam'iyyar PDP

Sanata Ogoshi Onawo ya aika wasikar ga shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Galadimawa, a karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa.

“Ina rubuto wannan wasika ne domin sanar da ku a hukumance cewa na yi murabus daga kasancewa mamba na jam’iyyar PDP, gundumar Galadimawa, karamar hukumar Doma, tun daga ranar, 10 ga watan Janairun, 2026."

- Sanata Ogoshi Onawo

Meyasa Sanatan ya fice daga PDP?

Sanatan ya bayyana cewa shawarar da ya dauka ta ficewa daga PDP ta samo asali ne saboda dalilai na kashin kansa kawai.

“Na dauki wannan mataki ne bayan yin dogon nazari, kuma gaba ɗaya saboda dalilai na kashin kaina.”

- Sanata Ogoshi Onawo

Onawo ya yi godiya ga jam'iyyar PDP

A cikin wasikar, Sanata Ogoshi Onawo ya gode wa shugabancin jam’iyyar PDP, mambobinta da magoya bayanta bisa damar da suka ba shi na yin hidima a karkashin inuwar ta, jaridar The Nation ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Atiku ko Obi: Sanatar ADC ta fadi wanda za ta goyi baya a zaben shugaban kasa na 2027

“Ina mika godiya ta musamman ga shugabannin jam’iyyar PDP mambobi da magoya baya bisa damar da suka ba ni domin na yi amfani da ita wajen yi wa al’ummata hidima tsawon shekaru.”

- Sanata Ogoshi Onawo

Jam'iyyar PDP ta rasa daya daga cikin sanatocinta
Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki Hoto: Kabiru Tanimu Turaki, SAN
Source: Instagram

'Dan majalisar ya yaba wa magoya bayansa

Ya kuma yaba da goyon bayan da ya samu a lokacin da yake cikin PDP, tare da yi wa jam’iyyar fatan alheri da samun ci gaba.

“Ina matukar godiya bisa amincewa, hadin kai da goyon bayan da na samu a tsawon lokacin da na yi a jam’iyyar. Don Allah ku karɓi godiyata tare da fatan alheri ga ci gaba da nasarar jam’iyyar."

- Sanata Ogoshi Onawo

Sanatan bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba. Sai dai rahotanni na danganta shi da jam’iyyar ADC, inda aka ce an gan shi a taronta a watan Yuli na shekarar 2025.

Batun ficewar Gwamna Bala daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar PDP na jihar Bauchi ya yi magana kan batun sauya shekar Gwamna Bala Mohammed.

Hon. Samaila Adamu Burga watsi da abin da ya kira rahotannin karya da yaudara da ke zargin cewa Gwamna Bala Mohammed na shirin ficewa daga PDP zuwa ADC.

Ya bayyana cewa Gwamna Bala Mohammed wanda zai bar ofis a 2023 ba shi da wata niyya ko kaɗan ta barin PDP zuwa ADC ko wata jam’iyya daban.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng