Magana Ta Kare: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kammala Shirin Shiga APC, an Sa Rana

Magana Ta Kare: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kammala Shirin Shiga APC, an Sa Rana

  • Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na dab da sauya sheƙa daga NNPP zuwa jam’iyyar APC bayan kammala shawarwari
  • Shugabannin APC a Kano sun ce an shirya tarba ta musamman domin karɓar gwamnan, inda ake sa ran manyan jiga-jigan siyasa za su halarta
  • Matakin ya janyo rarrabuwar kai a NNPP da tafiyar Kwankwasiyya, yayin da Rabiu Musa Kwankwaso ke nuna rashin amincewa da wannan sauyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Alamu sun nuna cewa siyasar jihar Kano na gab da shiga wani sabon salo, bayan da rahotanni ke nuni da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC.

Wata majiya daga majalisar zartarwar jihar Kano ta tabbatar da cewa an kammala dukkan matakan shirye-shirye, kuma jam’iyyar APC a jihar ta shiga yanayin shirin tarbar gwamnan tare da magoya bayansa.

Kara karanta wannan

Alaka ta yi tsami: Mabiya Kwankwaso sun ki zuwa taron da Abba ya shirya a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf a gaban wasu jama'a a Kano. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

The Nation ta rahoto cewa an fara tsara sauya sheƙar tun farko a ranar 5, Janairu, 2026, amma aka ɗaga shi domin bai wa gwamnan damar ƙara samun goyon bayan wasu masu muhimmanci, musamman ‘yan majalisar dokoki.

Dalilan sauya sheƙar Abba Kabir Yusuf

Majiyoyi na kusa da gwamnati sun bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yanke shawarar sauya sheƙa ne domin ƙarfafa ayyukan gwamnatinsa da kuma samun cikakken goyon bayan jam’iyyar da ke mulki a matakin ƙasa.

An ce gwamnan na ganin kasancewa cikin APC zai ba shi damar aiwatar da shirye-shiryen raya jihar Kano cikin kwanciyar hankali, musamman duba da rikice-rikicen shugabanci da shari’o’in kotu da ke addabar jam’iyyar NNPP.

Wata majiya ta ce waɗannan matsaloli na iya jefa mulkinsa cikin hadari, abin da ya sa ya fi jin kwanciyar hankali a APC fiye da jam’iyyar da ya hau mulki da ita.

Abba zai shiga APC a ranar Litinin

Kara karanta wannan

"Ni zan masu dariya a karshe," Kwankwaso ya kara tabo batun sauya shekar Gwamna Abba

Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan Kano kuma tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya dawo Najeriya domin halartar tarbar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

An ce shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, tare da sauran jiga-jigan jam’iyyar, sun aike da gayyata ta musamman ga gwamnan, suna masa tabbacin cikakken haɗin kai da goyon baya a cikin jam’iyyar.

Majiyar ta ƙara da cewa ana sa ran dukkan shugabannin ƙananan hukumomi a Kano, da ‘yan majalisar dokokin jihar da ke ƙarƙashin NNPP, za su bi gwamnan zuwa APC a yau Litinin, 12 ga Janairun 2026.

Sai dai wannan mataki ya fuskanci adawa daga jagoran NNPP da tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya bayyana cewa bai amince da sauya sheƙar ba.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa an jibge jami'an tsaro a gidan gwamnatin Kano yayin da shirye-shirye sauya shekar gwamnan ta kankama.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf yayin wani taro. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Kwankwaso na karbar 'yan jam'iyyar NNPP

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na cigaba da karbar 'yan Kwankwasiyya a gidajensa na Kano da Abuja.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: Dalilan da suka sanya Gwamna Abba zai rabu da NNPP zuwa APC

Hakan na zuwa ne yayin da ake rade-radin cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na dab da shiga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Jama'an Kwankwasiyya da ke zuwa gidan Kwankwaso suna jaddada cewa za su cigaba da kasancewa tare da shi a jam'iyyr NNPP.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng