Kwankwaso Ya Kara Kaimi wajen Shawo kan Jama'a, Abba na Shirin Shiga APC

Kwankwaso Ya Kara Kaimi wajen Shawo kan Jama'a, Abba na Shirin Shiga APC

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na karɓar ƙungiyoyin matasa, 'yan siyasa, 'yan kasuwa a gidajensa domin ƙarfafa akidar Kwankwasiyya
  • Matakin ya zo ne a daidai lokacin da ake rade-radin sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki a Najeriya
  • Masu lura da siyasa na ganin rikicin ya nuna rarrabuwar kai tsakanin mabiya tafiyar Kwankwasiyya da Rabiu Kwankwaso ke jagoranta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - A daidai lokacin da ake ci gaba da rade-radin sauya sheƙar Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, na cigaba da hada kan jama'a.

Rahotanni sun nuna cewa Kwankwaso ya shafe sama da mako guda yana karɓar tawaga daban-daban da ƙungiyoyin siyasa, da ƙungiyoyin matasa.

Kara karanta wannan

Alaka ta yi tsami: Mabiya Kwankwaso sun ki zuwa taron da Abba ya shirya a Kano

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da 'yan NNPP
'Yan Kwankwasiyya a gidan Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Legit Hausa ta bibiyi shafukan Facebook da X na hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ta tattaro yadda ya ke karba matasa a gidajensa da ke Kano da Abuja, inda suke sake jaddada biyayyarsu ga akidar Kwankwasiyya.

Wannan yunƙuri ya zo ne bayan alamun rashin jituwa da aka fara gani tsakanin Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf, wanda ake ɗauka a matsayin ɗaya daga cikin manyan almajiransa a siyasa tun kafin cin gwamna a zaɓen 2023.

Rabiu Kwankwaso na tattara matasan Kano

Yawancin tawagar da Kwankwaso ke karɓa sun ƙunshi ƙananan ƙungiyoyi matasa, tsofaffin masu yaƙin neman zaɓe da masu wayar da kan jama’a a.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa irin waɗannan kungiyoyi ne suka taka rawar gani wajen nasarar tabbatar da nasarar NNPP a zaɓen 2023 a Kano.

A yayin ziyarce-ziyarce, wakilan ƙungiyoyin suna bayyana biyayyarsu ga Kwankwaso tare da nisanta kansu daga abin da suka kira dabarun siyasa na masu mulki.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Kwankwaso ya nemi a biya su da Gwamna Abba ya karbi katin shiga APC

Matasa da sauran masu ziyarar sun jaddada cewa akidar Kwankwasiyya ita ce ginshiƙin tafiyarsu, ba mukamai ko shiga gwamnati ba.

Masu sharhi kan siyasa na ganin cewa duk da ƙarancin yawan kungiyoyin, ziyarce-ziyarcen suna da ma’ana ta siyasa, domin suna nufin tabbatar wa magoya baya cewa Kwankwasiyya na nan daram duk da rikicin da ake hasashen na iya ɓarke wa.

Shugabannnin Kwankwasiyya a gidan Rabiu Kwankwaso
Shugabannin Kwankwasiyya na kasashen waje a gidan Rabiu Kwankwaso a Abuja. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

A gefe guda kuma, ana kyautata zaton cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu goyon bayan mafi yawan wadanda aka zaba da kuma jami’an gwamnati a jihar.

Daga cikin masu biyayya ga Abba Kabir akwai kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, ’yan majalisa da shugabannin ƙananan hukumomi.

Abba Kabir ya yabi Rabiu Kwankwaso

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sha yabo wajen gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya yaba wa Kwankwaso ne kan yadda ya kirkiro cibiyoyin koyon sana'o'i domin taimakon matasan Kano.

A daya bangaren kuma, Abba Kabir Yusuf ya caccaki Abdullahi Ganduje kan dakatar da cibiyoyin koyon sana'o'in a lokacin mulkinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng