Alaka Ta Yi Tsami: Mabiya Kwankwaso Sun ki Zuwa Taron da Abba Ya Shirya a Kano

Alaka Ta Yi Tsami: Mabiya Kwankwaso Sun ki Zuwa Taron da Abba Ya Shirya a Kano

  • Wasu 'yan siyasar Kano masu biyayya ga Rabiu Musa Kwankwaso ba su halarci taron da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shirya a Kano ba
  • Taron raba tallafi a Kano shi ne fitowar gwamnan na farko bainar jama'a tun bayan fara rade-radin sauya sheƙarsa daga NNPP mai-ci zuwa APC
  • Rashin zuwan manyan masu yi wa Kwankwaso biyayya taron ya ƙara tayar da jita-jita game da rikicin siyasa a Kano, musamman a Kwankwasiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Ba a ga masu biyayya ga tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ba a lokacin da Abba Kabir Yusuf ya bayyana a bainar jama’a karon farko bayan bullar rade-radin cewa yana duba yiwuwar sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya shafe sama da mako guda ba tare da fitowa bainar jama’a ba, inda ake cewa yana Abuja a tsawon wannan lokaci.

Kara karanta wannan

Ana maganar shiga APC, Abba Kabir ya caccaki Ganduje, ya yabi Kwankwaso

Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso
Jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso da gwamna Abba Kabir Yusuf. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa fitowarsa ta zo ne a wajen bikin kammala karatu da raba kayayyakin tallafi ga matasa 2,260 daga cibiyoyin koyon sana’o’i na gwamnati.

Taron da Abba Kabir ya shirya a Kano

A karon farko bayan fara maganar sauya sheka daga NNPP zuwa APC, Abba Kabir ya gudanar da taro raba tallafi a dandalin Open Space Theatre da ke Gidan Gwamnati, Kano.

Wadanda suka amfana sun fito ne daga cibiyoyi daban-daban da suka haɗa da Cibiyar Fina-finai, Cibiyar Kiwon Kaji, Cibiyar Kiwo, Cibiyar Tuki, Cibiyar Kiwon Kifi, Cibiyar Noma da Shuke-shuke, da sauransu.

Fitowar gwamnan ta ja hankalin jama’a ne saboda ita ce karon farko tun bayan fara rade-radin sauya sheƙarsa, lamarin da ya haifar da fassarori game da siyasa tsakanin magoya bayan jam’iyyar NNPP da APC.

Wasu mabiya Kwankwaso da ba a gani ba

A wajen taron, an lura da rashin halartar shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, wanda ake ganin yana daga cikin amintattun Kwankwaso.

Kara karanta wannan

"Bai yi butulci ba": Kwamishina a Kano ya wanke Abba daga zargin juya wa Kwankwaso baya

A maimakon haka, an ga Zubairu Abiya, wanda aka ɗauka a matsayin mai biyayya ga gwamnan da kuma aka bayyana a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na rikon kwarya bayan cewa an sauke Dungurawa.

Haka kuma, wasu manyan masu biyayya ga Kwankwaso da ake cewa suna adawa da yiwuwar sauya sheƙar gwamnan ba su bayyana ba.

Abba Kabir Yusuf yayin wani taro a Kano.
Abba Kabir Yusuf yana jawabi a wajen raba tallafi a Kano. Hoto: Ibrahim Adam
Source: Facebook

Daga cikinsu akwai Kwamishinan Matasa da Wasanni, Mustapha Rabiu Kwankwaso; Kwamishinan Kimiyya, Yusuf Kofar Mata; Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, AVM Ibrahim Umar (mai ritaya); da Shugaban Ma’aikatan Jihar, Abdullahi Musa.

Mutanen Abba Kabir da suka halarci taron

A gefe guda, an ga halartar kwamishinoni da dama, shugabannin ƙananan hukumomi, ’yan Majalisar Dokokin Kano da sauran manyan jami’an gwamnati.

Sakon da hadimin gwamnan, Sanusi Bature ya wallafa a Facebook ya nuna cewa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Ismail Jibril Falgore, da Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar Farouk Ibrahim, sun halarci taron.

Duk da halartar manyan jami’ai, rashin zuwan wasu fitattun jiga-jigan jam’iyyar ya ƙara fito da rarrabuwar kawuna a cikin NNPP a jihar.

Abba ya soki Ganduje, ya yabi Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya jagoranci taron raba kayan tallafi ga matasan da aka koya wa sana'o'i.

Kara karanta wannan

"Ni zan masu dariya a karshe," Kwankwaso ya kara tabo batun sauya shekar Gwamna Abba

Rahotanni sun nuna cewa Abba Kabir ya yaba wa Rabiu Kwankwaso bisa kawo shirin da ya yi a lokacin da ya kafa cibiyoyin a jihar Kano.

Baya ga haka, gwamnan ya caccaki tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje kan rufe cibiyoyin da ya yi a lokacin mulkinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng