"Bai Yi Butulci ba": Kwamishina a Kano Ya Wanke Abba daga Zargin Juya wa Kwankwaso Baya

"Bai Yi Butulci ba": Kwamishina a Kano Ya Wanke Abba daga Zargin Juya wa Kwankwaso Baya

  • Kwamishinan yaɗa labarai na Kano ya ƙaryata zargin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso butulci
  • Ya ce siyasa lissafi ce da ake auna ribar da al’umma za ta amfana, kuma babu komai a bakin Gwamnan Kano sai talakawansa
  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bayyana irin ribar da ake fatan samu idan maganar sauya sheka zuwa APC ke yi ya tabbata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya wanke Gwamna Abba Kabir Yusuf daga zargin da ake yi masa na butulci ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Ya bayyana cewa maganar sauya sheƙa ta al'umma ce, kuma akwai riba da ake fatan jihar Kano za ta samu idan hakan ya tabbata.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Kwankwaso ya nemi a biya su da Gwamna Abba ya karbi katin shiga APC

Ibrahim Waiya ya ce Abba bai yi butulci ba
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Kwamared Waiya ya yi wannan bayani ne a wata hira da ya yi da Premier Radio, wadda aka wallafa a shafin Facebook na gidan rediyon.

Kwamishina ya wanke Abba daga zargin butulci

A cewarsa, ana yin nazarin siyasa ne domin a tantance ribar da al’umma za ta samu daga kowanne mataki ko sauyi da ake shirin ɗauka, ba wai domin faranta kai ba.

Ya ce:

“Duk wani abu da ake faɗi, da kalmomi marasa daɗi, da abubuwan da wasu ke faɗawa Mai girma Gwamna na cewa zai yi butulci, babu maganar butulci a cikin lissafin siyasa.”

A cewarsa:

"Lissafi ne, zama ake a yi lissafi. Haka za ka zauna ka yi lissafin siyasa a kan faifai, ka duba ta ina zai bullo, musamman idan ka yi la’akari da abin da al’ummarka za ta amfana.”

Wannan, a cewarsa, shi ne ginshiƙin siyasa ta gari wadda ke duban makomar jama’a da abin da za su samu daga dukkannin matakan da za a dauka.

Kara karanta wannan

"Ni zan masu dariya a karshe," Kwankwaso ya kara tabo batun sauya shekar Gwamna Abba

Ibrahim Waiya ya goyi bayan Gwamnan Kano

Kwamred Ibrahim Waiya ya jaddada cewa babu abin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke fifitawa face muradin al’ummar Kano da suka zaɓe shi.

Ya ce duk wani yunkuri da Gwamna zai ɗauka, yana duban tasirinsa ne ga jama’a, ba son kai ko ribar ƙashin kai da zai samu yi ba.

Waiya ya ce babu abin da ran Gwamna illa samo wa Kanawa mafita
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A kalamansa:

"Idan ana maganar siyasa, in dai don al’umma ake yi, ba ka fara kawo kanka ba; abin da za ka fara dubawa shi ne al’ummarka.”

Kwamishinan ya bayyana fatan cewa irin waɗannan matakai za su taimaka wajen warware matsaloli da ƙalubalen da aka dade ana fuskanta a jihar.

A cewarsa, duk wata matsala ko masifa da ta dabaibaye Kano sakamakon hadin baki ko wasu tsare-tsare na baya, akwai yiwuwar a shawo kanta idan aka ɗauki matakan da suka dace.

Ya ce:

"Duk abin da za a yi da duk juyin da za a yi, al'ummata ya ke magana. Kuma mu muna ganin, idan an yi irin wannan, zai iya zama alheri ga jihar Kano."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fadi baiwarsa da abin da ya bambanta shi da sauran ƴan siyasa

"Duk wasu matsaloli da duk wasu masifu da aka saka Kano a ciki, da duk wani hadin baki da aka yi, ake cutar da jihar Kano, duk wadannan za su iya warware wa."

Abba zai ga Tinubu bayan ganawa da Kwankwaso

A baya, mun wallafa cewa rahotanni daga Kano sun nuna cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi wata ganawa ta sirri da uban gidansa a siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

An ce taron ya gudana ne a daren Talata, 6 ga Janairu, 2026, inda majiyoyi suka bayyana cewa an gudanar da shi ba tare da hayaniya ba a yayin da batun sauya sheƙa ya girmama.

Rahotanni sun kara da cewa gwamnan ya isa gidan Kwankwaso da tsakar dare ne, tare da wani mai shiga tsakani da ake kira Sarkin Gobir, inda suka zo cikin motarsu ta kashin kansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng