APC: Kudu Maso Gabas Sun Dura kan Peter Obi, Sun Fadi Wanda Za Su Zaba a 2027
- Shugabannin APC na Kudu maso Gabas sun ayyana goyon baya ga Bola Tinubu a zaben 2027 domin tabbatar da cigaba da samun daidaito
- Wannan mataki ya zo ne kwanaki kadan bayan Peter Obi ya ayyana tsayawa takara a jam'iyyar ADC domin kalubalantar jam'iyya mai mulki
- Gwamnonin Kudu maso Gabas sun sha alwashin cewa ba za su sake yarda a rarraba kuri'un Inyamurai ba don kare muradin yankinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Enugu - Kusan makonni biyu kenan da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ayyana komawarsa jam’iyyar ADC domin yin takara a 2027.
Kwana 11 bayan haka, shugabannin jam’iyyar APC na shiyyar Kudu maso Gabas sun yi taro na musamman inda suka amince su marawa Shugaba Bola Tinubu baya a karo na biyu.

Source: Facebook
Kudu maso Gabas sun amince da tazarcen Tinubu
Wannan mataki na APC ya zo ne a matsayin martani ga Peter Obi, wanda ya yi alƙawarin amfani da sabuwar jam’iyyarsa ta ADC domin "ceto Najeriya," in ji rahoton Arise News.
A wani taro mai cike da tarihi da aka gudanar a Presidential Hotel da ke Enugu, shugabannin APC sun hade kansu ne ƙarƙashin jagorancin gwamnonin Kudu maso Gabas guda uku.
Bisa jagorancin Gwamna Hope Uzodimma (Imo), Francis Nwifuru (Ebonyi), da Peter Mbah (Enugu), shugabannin APC sun bayyana cewa Tinubu ne kaɗai ɗan takararsu a 2027.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, ne ya gabatar da kudurin marawa Tinubu baya, inda Ken Nnamani ya goyi bayan hakan.
Shugabannin APC a shiyyar sun gargaɗi mutanen yankin nasu da kada su yarda a rarraba ƙuri'unsu tsakanin jam'iyyu da dama, wanda hakan ke rage tasirinsu a siyasar ƙasa.
Me ya sa Kudu maso Gabas suka zaɓi Tinubu?
Gwamna Peter Mbah ya bayyana wannan sauyin matsayi a matsayin “wayewar siyasa wadda aka gina kan kyakkyawan tunani.”
Shugabannin sun ce sun gamsu da yadda Tinubu ya maida hankali wajen gina ababen more rayuwa a shiyyar da kuma naɗa ’ya’yansu a manyan muƙaman gwamnati.
Sun jaddada cewa APC ita ce mafi kyawun dandali da zai tabbatar wa Inyamurai samun rabonsu na arzikin ƙasa da ci gaba.

Source: Facebook
Hasashen komawar wasu gwamnoni APC
A cikin sanarwar bayan taro da suka fitar, sun nesanta kansu da duk wani ɗan siyasa daga yankin da ke neman shugabancin ƙasa don son kansa, in ji rahoton Punch.
Gwamna Nwifuru ya ƙara da cewa yana da yaƙinin cewa kafin 2027, dukkan gwamnonin Kudu maso Gabas za su dawo jam’iyyar APC.
Sun yi rantsuwar tattara dukkan albarkatunsu domin tabbatar da cewa Tinubu ya samu gagarumar nasara a jihohi biyar na shiyyar.
'Tinubu ya cancanci tazarce,' - Omokri
A wani labari, mun ruwaito cewa, Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya cancanci tazarce a 2027.
Fitaccen marubucin ya bayyana cewa 'yan Najeriya sun zabi jam'iyyar APC a zabukan cike gurbi da aka gudanar ranar Asabar saboda wasu dalilai 20.
Wannan na zuwa ne bayan shugabar Hukumar Cinikayya ta Duniya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya “daidaita” tattalin arzikin Najeriya.
Asali: Legit.ng


