ADC na Shirin Hadaka da PDP da NNPP domin Kifar da Tinubu a 2027

ADC na Shirin Hadaka da PDP da NNPP domin Kifar da Tinubu a 2027

  • Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa ana tattaunawa tsakaninta da jam'iyyun NNPP da PDP kan yiwuwar haɗaka gabanin zaɓen 2027 mai zuwa
  • Kakakin ADC ya bayyana cewa manufar yunƙuri shi ne samar da rayuwa mai inganci ga ‘yan Najeriya ba karɓar mulki kaɗai ba wajen APC
  • Yayin da ake cigaba da maganar 2027, jam'iyyar ADC ta kafa kwamitin duba kundin tsarin mulkinta domin ƙarfafa dimokiraɗiyya da haɗin kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Alamu na ƙara bayyana cewa wasu jam’iyyun siyasa a Najeriya na nazarin sake haduwa gabanin zaɓen shekarar 2027, da nufin kalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyarsa ta APC.

Wannan yunƙuri na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta tattaunawa a bayan fage tsakanin manyan jam’iyyun adawa a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

APC ta dauki zafi da ta ji jita jitar tsohon shugaban jam'iyya ya sauya sheƙa zuwa ADC

Atiku Abubakar, Bola Tinubu da Rabiu Kwankwaso
Manyan 'yan ADC da NNPP tare da Bola Tinubu. Hoto: Saifullahi Hassan|Atiku Abubakar|Bayo Onanuga
Source: Facebook

ADC na son hadaka da PDP da NNPP

AIT ta rahoto cewa sakataren yaɗa labaran jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana maganar hadakar a Abuja, inda ya ce jam’iyyarsa na tattaunawa da NNPP da PDP domin duba yiwuwar kafa wata haɗaka.

A cewarsa, manufar tattaunawar ita ce samar da tsari da zai kawo sauƙi da kyakkyawar rayuwa ga al’ummar Najeriya, musamman duba da halin da ƙasar ke ciki a fannoni da dama.

Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa tattaunawar da ake yi tsakanin ADC, NNPP da PDP na ci gaba, inda kowace jam’iyya ke bayyana matsayinta kan yadda za a gina haɗakar da za ta kasance mai fa’ida ga jama’a.

Ya jaddada cewa abin da jam’iyyun ke dubawa shi ne yadda za a samar da shugabanci nagari, da manufofi masu ma’ana da za su inganta rayuwar talakawa.

Kakakin ADC, Malam Bolaji Abdullahi
Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi yana jawabi. Hoto: ADC Vanguard
Source: Facebook

Bolaji Abdullahi ya kuma bayyana cewa ADC na ƙoƙarin gina jam’iyya mai ƙarfi da tsarin dimokiraɗiyya na gaskiya, inda ra’ayin mambobi zai zama ginshiƙi a yanke manyan shawarwari.

Kara karanta wannan

APC ta bugi kirji, ta fadi adadin kuri'un da Tinubu zai samu a Filato a 2027

Za a duba kundin tsarin mulkin jam'iyyar ADC

A wani ɓangare na shirye-shiryen jam’iyyar, ADC ta kafa Kwamitin Duba Kundin Tsarin Mulki, domin sake fasalin wasu tanade-tanade da ake ganin za su ƙara ƙarfafa jam’iyyar.

Jiga-jigan 'yan siyasa ne ke jagorantar kwamitin, ciki har da tsohon gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, da tsohon shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Enyinnaya Abaribe.

Jam’iyyar ta ce an dora wa kwamitin alhakin gabatar da rahoton farko da shawarwarin gyare-gyare ga kwamitin gudanarwa na ƙasa cikin kwanaki 30.

Kalli bidiyon hirar da aka yi da Bolaji Abdullahi kamar yadda shafin ADC Vanguard ya wallafa a X:

APC ta magantu kan nasarar Bola Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na jihar Kwara, Sunday Fagbemi ya yi magana kan tazarcen shugaba Bola Tinubu.

Fagbemi ya ce zaben 2027 zai zo wa APC da sauki lura da cewa tana da gwamnoni kusan 30 a fadin kasa da za su mata aiki sosai.

Shugaban jam'iyyar ya bayyana haka ne yayin taron kaddamar da rajistar shiga jam'iyyar ADC ta yanar gizo a birnin Ilorin na jihar Kwara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng