An Kira Sunan Atiku da Aka Lissafa 'Yan Siyasar da Suka 'Ruguza' Jam'iyyar PDP

An Kira Sunan Atiku da Aka Lissafa 'Yan Siyasar da Suka 'Ruguza' Jam'iyyar PDP

  • Ayo Fayose ya zargi su Atiku Abubakar da Aminu Tambuwal da ruguza jam'iyyar PDP sakamakon son rai da rashin adalci a zaben 2023
  • Tsohon gwamnan ya jaddada cewa duk da ya goyi bayan Bola Tinubu a 2023, ba zai taba komawa jam'iyyar APC ba, yana nan a cikin PDP
  • Fayose ya ce sai da ya gargadi Gwamna Simi Fubara da kada ya ci amanar Nyesom Wike duba da irin rikicin dake faruwa a jihar Rivers

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose, ya fito fili ya zargi wasu fitattun 'yan siyasar Najeriya da jawo rugujewar jam'iyyar hamayya ta PDP.

Fayose ya ce PDP ta ruguje ne saboda tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, da kuma tsohon shugaban jam’iyya Iyorchia Ayu.

Kara karanta wannan

Ribas: Gwamna Fubara na tsaka kai wuya, azumi da addu'a kadai za su cece shi

Atiku Abubakar, Aminu Waziri Tambuwal sun shiga jerin 'yan siyasar da ake zargi da ruguza PDP.
Atiku Abubakar tare da Aminu Waziri Tambuwal a gidansa da ke Abuja. Hoto: @atiku
Source: Twitter

An zargi su Atiku da lalata jam'iyyar PDP

Fayose ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 9 ga Janairu, 2026, yayin wata hira ta musamman da gidan talabijin na Channels TV a cikin shirin "Siyasa a yau".

Fayose, wanda aka sani da faɗar gaskiya ba tare da tsoro ba, ya bayyana cewa:

“Atiku ya lalata PDP, Tambuwal ya lalata PDP, haka ma Ayu ya lalata ta. Siyasa ba ta da adalci, kuma rayuwar kanta ba ta kullum take zuwa mana a daidai ba.”

Ya jaddada cewa ko da yake shi har yanzu mamba ne na PDP, amma ya fito fili ya goyi bayan Bola Tinubu na jam’iyyar APC a zaɓen 2023 kuma ba ya nadamar hakan.

Fayose ya ce:

“A fili na goyi bayan Asiwaju Tinubu kuma ban ɓoye ba. Har yanzu ina nan kan bakana, ban sauya ra'ayi ba. Ni ba d'an jam'iyyar APC ba ne, kuma ba zan taba zama ba.”

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Kwankwaso ya nemi a biya su da Gwamna Abba ya karbi katin shiga APC

'Na gargadi Fubara kan cin amanar Wike' - Fayose

Baya ga maganar rikicin PDP, Fayose ya tabo rigimar da ake yi a Jihar Rivers tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Ya bayyana cewa bai taba tunanin za a samu saɓani tsakanin mutanen biyu ba amma Fayose ya ba da labarin cewa a ranar rantsar da Fubara, ya gargaɗe shi a gaban Wike cewa ya kiyaye kada ya ci amanar wanda ya tsaya masa.

Fayose ya ce:

“Ina zaune a babban teburin manyan baki a ranar da aka rantsar da Gwamna Fubara, na gaya masa cewa kada ya ci amanar Wike.”
Ayo Fayose ya yi magana game da rikicin jam'iyyar PDP
Ayo Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti da ya yi magana kan rikicin PDP.
Source: Twitter

Dalilin rikicin PDP da martanin Fayose

Rikicin PDP ya samo asali ne tun lokacin zaɓen fidda gwani na Mayu 2022, inda janyewar Tambuwal domin Atiku ya samu nasara ta fusata ɓangaren Nyesom Wike da gwamnonin "G5".

Wannan ya kai ga neman murabus ɗin Iyorchia Ayu domin samar da daidaito tsakanin shugabancin Arewa da Kudu, buƙatar da Atiku da Ayu suka ƙi amincewa da ita.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta yi zazzafan martani kan jita jitar Gwamna Bala zai koma ADC

Fayose ya kammala da cewa wannan rashin adalcin ne ya jefa jam’iyyar cikin mawuyacin halin da take ciki har zuwa yau.

Abin da ya jawo sabon rikicin Fubara da Wike

A wani labarin, mun ruwaito cewa, sulhun da Shugaba Bola Tinubu ya yi tsakanin manyan ’yan siyasa a Jihar Rivers (Gwamna Sim Fubara da Nyesom Wike) ya sake rushewa.

Wannan kuwa ya faru ne bayan majalisar dokokin jihar ta fara shirin tsige Gwamna Fubara bisa zargin aikata manyan laifuffuka, karya kundin tsarin mulki da kuma almundahana.

Wannan shi ne karo na uku da ake yunkurin tsige Gwamna Fubara cikin ƙasa da shekaru uku, tun bayan ɓarkewar sabani tsakaninsa da magabacinsa, Nyesom Wike.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com