Siyasar Kano: Kwankwaso Ya Nemi a Biya Su da Gwamna Abba Ya Karbi Katin Shiga APC
- Sanata Rabiu Kwankwaso ya gargadi Gwamna Abba Kabir Yusuf kan shirin komawa jam'iyyar APC, inda ya bayyana hakan da 'cin amana'
- Kwankwaso ya ce lallai akwai bukatar wadanda ke shirin barin NNPP zuwa APC a Kano su biya 'yan Kwankwasiyya wahalar da suka yi masu
- Majalisar dokokin jihar Kano dai ta amince da sauya shekar gwamnan zuwa APC domin kaucewa fadawa tarkon shari'ar da ta faru a Zamfara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Rikicin siyasa tsakanin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙara ƙamari sakamakon shirin gwamnan na ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Gwamna Abba, wanda ya riga ya karɓi katin zama mamba na jam’iyyar APC a mazaɓarsa, ya shirya gudanar da gagarumin taron sauya sheƙa a ranar Litinin, 12 ga Janairu, 2026.

Kara karanta wannan
"Ni zan masu dariya a karshe," Kwankwaso ya kara tabo batun sauya shekar Gwamna Abba

Source: Twitter
Maganar Kwankwaso kan sauya shekar Abba
Yayin da Kwankwaso ke ganin an ware shi gefe a wajen yanke manyan shawarwari, Gwamna Abba ya dage kan cewa sauya sheƙa haƙƙinsa ne na siyasa bayan tattaunawa da masu zaɓe, in ji rahoton The Nation.
Sanata Kwankwaso ya gargaɗi waɗanda ke shirin bin Gwamna Abba zuwa APC cewa lallai akwai sakamako ga duk wanda ya ci amanar tafiyar da ta gina shi, inda ya bayyana cewa:
“Kalmar ‘maci amana’ ta na bin mutum; shi karan kansa, iyalinsa, har ma da zuriyarsa.”
Kwankwaso ya yi zargin cewa masu barin NNPP zuwa jam'iyyar APC sun karɓi "toshiya" ne kafin su yanke shawarar barin gidansu na asali.
An nemi a biya 'yan kwankwasiyya diyya
Tsohon gwamnan na Kano ya bukaci dukkan mambobin NNPP da ke son sauya sheka zuwa APC da su biya diyya ga tafiyar Kwankwasiyya da ta sadaukar da komai wajen ganin nasararsu.
Da yake zantawa da wasu 'yan a-mutun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu ya ce akwai bukatar 'yan siyasa su yi karatun ta-nutsu, su daina biyewa kyal-kyalin 'banza' da zai iya kai su ya baro.
Jagoran Kwankwasiyyar ya nuna cewa da yawa daga cikin masu shirin sauya shekar za su iya zuwa su yi da-na-sani daga baya, saboda sun dauki gurguwar shawara yanzu.

Source: Original
Majalisar Kano ta goyi bayan Abba
Majalisar Dokokin Jihar Kano dai ta fito fili ta amince da shirin Gwamna Abba na komawa APC kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini, ya bayyana cewa zama a jam’iyyar NNPP babban haɗari ne ga makomar siyasar gwamnan da sauran zaɓaɓɓun wakilai saboda rikicin shugabanci da shari’o’in da suka addabi jam’iyyar.
Hussaini ya bayyana cewa:
“Ba za mu iya ci gaba da zama a jam’iyyar ba muna fuskantar barazanar abin da ya faru a Jihar Zamfara, inda Kotun Ƙoli ta soke dukkan zaɓaɓɓun wakilan jam’iyya saboda rashin sahihancin tsari.”
Majalisar ta nuna tsoron cewa rigingimun gida na NNPP na iya kai wa ga soke nasarar da suka samu a kotu, don haka komawa APC ita ce hanya mafi aminci ta kare wa’adin mulkin Gwamna Abba.
Kwankwaso ya fadi baiwarsa a siyasa
A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon ɗan takarar Shugaban Ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce shi ɗan siyasa ne da ba a saye shi da kuɗi.
Tsohon gwamnan jihar na Kano ya bayyana siyasar Kano a matsayin wadda jama’a ke da wayewa kuma ba sa yarda da cin hanci sai dai ra'ayin kansu.
Yayin da ake batun sauya sheƙar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Kwankwaso ya gargadi ’yan siyasa da masu zaɓe kan amincewa da ribar gajeren lokaci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

