NNPP Ta Yi Watsi da Hukuncin Kotu game da Rushe Shugabancin Jam'iyyar a Kano

NNPP Ta Yi Watsi da Hukuncin Kotu game da Rushe Shugabancin Jam'iyyar a Kano

  • Jam’iyyar NNPP ta bayyana rashin amincewarta da hukuncin kotu da ya shafi shugabancinta a Kano ba da kae takaddama a kai a 'yan kwanakin nan
  • Bangaren jam’iyyar ya ce hukuncin ba ya wakiltar ainihin tsarin da kundin jam’iyyar ya tanada, saboda haka babu wata magana ta rushe shugabancin da ta nada
  • Rikicin shugabanci na kara tsananta yayin da ake jiran matakan shari’a na gaba tun batan da jam'iyya ta kori tsige Hashimu Dungurawa mai kusanci da Rabiu Musa Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – NNPP ta yi watsi da hukuncin wata kotu da ya shafi shugabancin jam’iyyar a Jihar Kano, tana mai jaddada cewa hukuncin bai sauya matsayin shugabancin da jam’iyyar ta amince da shi ba.

Kara karanta wannan

Hadimin Abba ya fadi abin da ke shirin kora 'yan Kwankwasiyya zuwa jam'iyyar APC

Wannan bayani ya zo ne a ranar Laraba, 8 ga watam Janairu, 2026 a yayin da rikicin cikin gida ke ci gaba da daukar hankali, musamman a kan dambarwar sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

NNPP ta yi fatali da hukuncin kotu
Hashimu Dungurawa a gefen hagu, Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Sanata Rabi'u Kwankwaso a gefen dama Hoto: Abba Gwale/Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da jagororin NNPP a Kano suka fitar, jam’iyyar ta ce hukuncin kotun bai bi ka’idojin da kundin tsarin jam’iyyar ya tanada ba.

NNPP ta yi fatali da hukuncin kotu

The Guardian ta ruwaito Kakakin NNPP Ladipo Johnson ya kara da cewa tsarin zaben shugabanci da kuma yanke hukunci a cikin jam’iyya yana karkashin dokokin da aka amince da su tun farko.

Jam’iyyar ta kuma jaddada cewa shugabancin da take da shi a Kano ya samu sahalewar manyan hukumomin jam’iyyar a matakin kasa.

A cewar NNPP, duk wani yunkuri na bayyana wani shugabanci daban a matsayin halastacce ba zai samu karbuwa ba, har sai an bi dukkan hanyoyin doka da tsarin jam’iyyar.

Jam'iyyar NNPP ta ja hankalin 'ya'yanta

Sanarwar ta kara da cewa NNPP ta bukaci ‘yan jam’iyya da magoya baya da su kwantar da hankalinsu tare da kaucewa duk wani abu da zai iya haddasa tashin hankali.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Kotu ta kwace kadarori 57 na Malami a Kano, Abuja da wasu jihohi 2

NNPP ta ce tana da tsarin zabe a jam'iyya
Shugaban jam'iyyar NNPP na Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa Hoto: Mustapha Kakisu Yalwa
Source: Facebook

A halin yanzu, idanu na kan kotuna da manyan shugabannin jam’iyyar domin ganin yadda za a warware rikicin da ke neman jawo wankin hula ya kai NNPP dare.

Wannan mataki ya samo asali ne bayan 'yan jam'iyyar a matakin mazaba sun dakatar, tare da korar shugabansu, Hashimu Dungurawa tare da maye gurbinsa da Abdullahi Abiya, kamar yadda ta sanar a baya,

Rokon NNPP ga Gwamnan Kano

A wani labarin, mun wallafa cewa shugaban jam’iyyar NNPP a jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya bayyana tsare-tsare da karfin da jam’iyyar ke da shi a Najeriya tare da mika roko ga Abba Kabir Yusuf.

Dakta Hashimu Dungurawa ya yi kira kai tsaye ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da kada ya yi tunanin ficewa daga jam’iyyar, inda ya ce duk shiri na barin NNPP zai zama babban kuskuren siyasa ga Gwamnan.

Hashimu Dungurawa ya bayyana mamakinsa kan rahotannin da ke yawo cewa Gwamnan Kano na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, musamman ganin karfin alakarsa da tsarin Kwankwasiyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng