Siyasar Kano: NNPP Ta Yi Roko na Musamman ga Abba Kabir kan Shirin Shiga APC
- Shugaban NNPP na Kano da aka kora, Hashim Dungurawa, ya shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf ka da ya bar jam’iyyar
- Dungurawa ya jaddada cewa NNPP ita ce jam’iyya mafi cika ka’idojin doka, tana da tsari da ofisoshi a dukkan jihohi 36 da Abuja
- Ya ƙaryata rade-radin cewa Rabiu Kwankwaso na shirin komawa APC, yana mai cewa yana alfahari da NNPP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Shugaban NNPP a Jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya bayyana tsari da jam'iyyar ke da shi a Najeriya.
Dungurawa ya roki Gwamna Abba Kabir Yusuf da kada ya yi tunanin barin jam’iyyar saboda yin hakan babban kuskure ne.

Source: Facebook
NNPP ta roki Abba Kabir kan shiga APC
A wata hira da ya yi da Punch, Dungurawa ya ce ya yi matuƙar mamakin rahotannin da ke nuna cewa Gwamnan Kano na shirin ficewa daga NNPP.

Kara karanta wannan
"Ni zan masu dariya a karshe," Kwankwaso ya kara tabo batun sauya shekar Gwamna Abba
Dungurawa ya bayyana cewa NNPP jam’iyya ce mai karfi a matakin kasa, wadda ke da ofisoshi da cikakken tsari a fadin Najeriya.
Ya roki Gwamna Abba Kabir Yusuf kai tsaye da ya sake tunani kan duk wani shiri na sauya sheka, yana mai bayyana hakan a matsayin babban kuskuren siyasa.
Ya ce:
“Babu wata jam’iyyar siyasa a Najeriya da ta cika dukkan ka’idojin doka da inganci kamar NNPP.
“Muna kira gare shi da kada ya bar jam’iyyar. Wannan zai zama kuskure mafi girma da zai taba yi idan ya yanke shawarar ficewa daga NNPP."
Shugaban na NNPP wanda shugaabannin jiha suka tsige ya kara da cewa, gwargwadon saninsa, babu wani rikici ko matsala da ba a warware ba tsakanin jam’iyyar da gwamnan.

Source: Facebook
Rade-radin barin Kwankwaso jam'iyyar NNPP
Dangane da rade-radin da ke cewa shugaban jam’iyyar a matakin kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso, na shirin komawa jam’iyyar APC, Dungurawa ya yi watsi da batun gaba daya.
“Kwankwaso ba zai sauya sheka ba, yana alfahari da NNPP. Duk lokacin da ka ziyarce shi, za ka ga tutar jam’iyyar a kan teburinsa da kuma ofishinsa.”
- In ji Dungurawa.
Game da dalilin da ya sa yake zargin Gwamna Abba Kabir Yusuf na iya yin tunanin barin jam’iyyar, Dungurawa ya ce hasashensa ya dogara ne kan abubuwa biyu.
“Na yi wannan hasashe ne bisa abubuwa biyu. Na farko, wata kila ana matsa masa lamba daga hukumomi kamar ICPC ko EFCC, shi ya sa yake tunanin komawa APC.
“Amma ko da haka, akwai wasu da suka aikata fiye da abin da ake zargi, idan har ma akwai wani zargi.
“Wata kila saboda yawan kudaden da ake turawa gwamnonin jihohi. Idan haka ne, to abin kunya ne."
- Cewar Dungurawa
Sheikh Khalil ya shawarci Abba Kabir
Kun ji cewa Sheikh Ibrahim Khalil ya shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Ya ce dangantaka tsakanin Abba Kabir Yusuf da Kwankwasiyya ta riga ta lalace, saboda haka sauya sheka ce ta rage.
Malamin ya bayyana cewa sauya shekar Abba na ɗauke da alheri ga Kano, Arewa da Najeriya ta fuskoki da dama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
