Siyasar Rivers: Dalilan da Suka Jawo Sabon Rikici tsakanin Fubara da Wike

Siyasar Rivers: Dalilan da Suka Jawo Sabon Rikici tsakanin Fubara da Wike

  • Majalisar Jihar Rivers ta sake kaddamar da shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara, lamarin da ya nuna rushewar sulhun da Bola Ahmed Tinubu ya yi
  • Rahoto ya ce rikicin ya samo asali ne daga sabani kan yarjejeniyoyin baya, kasafin kuɗi da kuma batun wa’adin mulki na biyu da Fubara zai iya nema
  • Hakan na zuwa ne bayan kokarin da shugaban ƙasa ya yi a jihar tun daga 2023, ciki har da ayyana dokar ta-baci da sake dawo da Fubara kan mulkin Rivers

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers – Sulhun da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi tsakanin manyan ’yan siyasa a Jihar Rivers ya sake rushewa, bayan Majalisar Dokokin jihar ta fara shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta dauki zafi, ta yi magana kan shirin tsige Gwamma Fubara daga mulki

Majalisar, ƙarƙashin jagorancin shugabanta Martins Amaewhule, ta fitar da sanarwar tuhuma da zargin aikata manyan laifuffuka, karya kundin tsarin mulki da kuma almundahana, lamarin da ya sake tayar da ƙurar rikicin siyasa a jihar.

Gwamna Simi Fubara da Nyesom Wike
Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara da Ministan Abuja, Nyesom Wike. Hoto: Lere Olayinka|Rivers State Government
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa matakin majalisar ya zo ne duk da kokarin sulhu da shugaban ƙasa ya yi a lokuta daban-daban, abin da ke nuna cewa sabon sulhun da aka cimma bai dawwama ba.

Yadda rikicin siyasar Rivers ya fara

Wannan shi ne karo na uku da ake yunkurin tsige Gwamna Fubara cikin ƙasa da shekaru uku, tun bayan ɓarkewar sabani tsakaninsa da magabacinsa kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

Punch ta wallafa cewa rikicin ya fara ne bayan Fubara ya hau mulki a 2023, inda rikici ya barke tsakanin bangaren zartarwa da majalisa.

A watan Disamba, 2023, Shugaba Tinubu ya shiga tsakani karo na farko bayan ’yan majalisa masu biyayya ga Wike sun fara yunkurin tsige Fubara.

Tsoma bakin ya haifar da wata yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnan, majalisar da ministan FCT. wacce ita ma ta rushe daga baya.

Dokar ta-baci da dawowar Simi Fubara

Kara karanta wannan

Majalisar Rivers ta lissafo zunuban Fubara 11 yayin take shirin tsige shi

Rikicin ya sake tsananta a watan Maris, 2025, lokacin da Majalisar ta sake fara shirin tsige gwamnan, lamarin da ya sa Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers.

A lokacin, an dakatar da gwamnan, mataimakiyarsa da ’yan majalisa, sannan aka naɗa Ibok-Ete Ibas a matsayin mai kula da harkokin jihar.

Kafin karewar wa’adin dokar ta-baci, shugaban ƙasa ya sake sasanta bangarorin siyasar jihar, wanda ya kai ga dawo da Fubara kan kujerarsa. Sai dai sabon matakin da Majalisar ta dauka ya nuna cewa wannan sulhu ma ya sake rushewa.

Dalilan sake rikicin Gwamna Fubara da Wike

Masu bibiyar siyasa sun ce batun tsige Fubara na da alaka da zargin ya karya wasu yarjejeniyoyi da aka cimma a baya, ciki har da batun rashin neman wa’adi na biyu.

Haka kuma, rahotanni sun nuna cewa rikici ya sake ɓarkewa ne bayan gwamnan ya ƙi amincewa da wani ƙarin kasafin kudi da ’yan majalisa masu biyayya ga Wike suka gabatar.

An ce Fubara ya dage cewa kasafin kuɗin Naira tiriliyan 1.48 na shekarar 2025 da aka amince da shi a lokacin dokar ta-baci zai wadatar da jihar.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara shirin tsige gwamna Fubara bayan sabon rikici da Wike

Bayan kin amincewar ƙarin kasafin, an ce Wike ya kira taro da abokan siyasar sa a Port Harcourt, yayin da Fubara ya hanzarta shiga jam’iyyar APC da amincewar Shugaba Tinubu, a yunkurin rage tasirin Wike.

Haka kuma, ana zargin Fubara ya ƙi cika wasu sharuɗa da suka haɗa da mayar da Sergeant Awuse kan kujerar shugaban majalisar sarakunan gargajiya da kuma naɗa sababbin kwamishinoni.

Yadda aka yi zaman sulhu kan siyasar Rivers
Jagororin siyasar Rivers a lokacin zama da shugaba Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

APC ta ki yarda da tsige Fubara

A wani labarin, mun kawo muku cewa jam'iyyar APC ta yi martani kan shirin da majalisar jihar Rivers ta fara na ganin ta tsige gwamna Simi Fubara.

Jam'iyyar APC a jihar Rivers ta yi Allah wadai ta matakin tana mai cewa bata yarda da shi ba, lamarin da ake ganin zai zama kariya ga gwamnan.

Sai dai har yanzu APC a matakin kasa bata fito ta yi magana ba game da lamarin, duk da wasu manyan shugabannin jam'iyya sun fara sabani da Wike.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng