Sabani Ya Gifta tsakanin Yan Kasuwa da Matatar Dangote kan Yarjejeniyar Sayen Mai da Sauki
- Yarjejeniyar rarraba fetur tsakanin matatar Dangote da manyan ’yan kasuwa 20 ta rushe saboda takaddama kan farashi
- Haka kuma shigo da fetur daga waje ya karu sosai a Nuwamba 2025 bayan ganin farashin duniya ya fi na Dangote sauki
- Matatar Dangote ta fitar da sabon tsarin sayar da man fetur ga kowane ɗan kasuwa daga lita 250,000 zuwa sama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Rahotanni sun nuna cewa yarjejeniyar samar da fetur tsakanin matatar man fetur ta Dangote da manyan ’yan kasuwa 20 ta lalace sakamakon sabani kan farashin sayarwa.
A karkashin wannan shiri, bangarorin sun amince cewa ’yan kasuwan za su rika karɓar kimanin lita miliyan 600 na fetur a kowane wata.

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta ruwaito cewa sai dai rashin jituwa kan daidaita farashi ya kawo karshen shirin bayan kusan wata guda kacal da fara shi.
Shigo da man fetur daga waje ya karu
Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NMDPRA) ta bayyana cewa shigo da fetur daga waje ya karu zuwa lita biliyan 1.563 a watan Nuwamba 2025.
Wannan karin ya zo ne a daidai lokacin da rikicin farashi tsakanin Dangote da ’yan kasuwar man fetur a Najeriya ya kara tsananta.
An dai cimma yarjejeniyar ne a watan Oktoba 2025 a matsayin gwaji, inda aka ware masu ajiya 20 su rika karɓar fetur kai tsaye daga matatar tare sayarwa yan Najeriya.
Sakataren hulɗa da jama’a na IPMAN, Chinedu Ukadike, ya bayyana cewa an kafa tsarin ne domin daidaita samar da fetur a cikin gida da rage tsadarsa daga tushe.
Farashin mai ya rikito a duniya
Majiyoyi daga masana’antar sun bayyana cewa yarjejeniyar ta kunshi duba farashi duk wata bisa canjin kasuwar duniya.
A farkon shirin, Dangote ya sayar da fetur kan N806 kowace lita ga jigilar bakin teku, sannan N828 a gantry.
An kuma dakatar da sayarwa kai tsaye ga kananan ’yan kasuwa, wanda ya tilasta musu saye daga manyan 20 da aka amince da su.

Source: Getty Images
Sai dai a Nuwamba, farashin fetur a kasuwar duniya ya fadi kasa da na Dangote, lamarin da ya sa ’yan kasuwa suka koma shigo da fetur daga waje.
Duk da cewa daga baya Dangote ya rage farashin dauko mai zuwa N699 kowace lita — mafi araha a shekarar 2025 — hakan ya zo ne bayan ’yan kasuwa sun riga sun fuskanci asara.
Bayanan MEMAN da petroleumprice.ng sun nuna cewa matsakaicin kudin sauke fetur daga waje ya sauka zuwa N829.77 a karshen Oktoba, kasa da farashin dauki man Dangote a lokacin.
Rikicin ya kuma kai ga cacar baki tsakanin Dangote da tsohon shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed, kan bayar da lasisin shigo da fetur, wanda daga baya ya kai ga murabus dinsa a Disamba 2025.
A yanzu haka, matatar Dangote ta soke duk wata yarjejeniya ta keɓancewa, ta koma tsarin kasuwa a bude, inda kowane ɗan kasuwa zai iya sayen fetur kai tsaye, ko da kuwa daga lita 250,000 ne kacal.
Wannan mataki, a cewar IPMAN, dabarar kasuwa ce domin ƙara gasa da hana hauhawar farashi ba gaira ba dalili.
A cewarsa, an yanke shawarar takaita masu saye kai tsaye domin rage matsakaici da ke haddasa rikice-rikicen farashi.
Dangote ya ƙaryata batun rufe matatarsa
A baya, mun wallafa cewa matatar man fetur ta Dangote da ke jihar Legas ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ta dakatar da ayyukanta na wani lokaci.
Matatar ta bayyana irin wadannan rahotanni a matsayin ƙarya da yaudara, tana mai jaddada cewa babu wani shiri na rufe ko dakatar da ayyukanta na samar da mai.
Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rukunin kamfanonin Dangote Group ya fitar kan zargin fara gyare-gyare a matatar,.inda ta ce aiki na gudana yadda ya kamata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


