Atiku ko Obi: Sanatar ADC Ta Fadi Wanda Za Ta Goyi Baya a Zaben Shugaban Kasa na 2027

Atiku ko Obi: Sanatar ADC Ta Fadi Wanda Za Ta Goyi Baya a Zaben Shugaban Kasa na 2027

  • Sanata mai wakiltar Abuja, Ireti Kingibe ta bayyana matsayarta game da tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben 2027
  • Kingibe, wacce ta sauya sheka daga LP zuwa ADC, ta ce babu tabbacin Peter Obi zai samu tikitin jam'iyyar a zabe mai zuwa
  • 'Yar Majalisar dattawan ta ce duk wanda ya samu tikitin takara tsakanin Atiku Abubakar, Obi ko wani daban, za ta mara masa baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sanata Ireti Kingibe, mai wakiltar Babban Birnin Tarayya (FCT) a Majalisar Dattawa, ta bayyana wanda za ta goyi baya a zaben shugaban kasar 2027 a inuwar ADC.

'Yar Majalisar dattawan, wacce ta koma tafiyar hadaka a inuwar ADC, ta ce a shirye take ta yi aiki da duk wanda ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Datti Baba Ahmed ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa, ya kara da Tinubu a 2027

Sanatar Abuja, Ireti Kingibe.
Sanata mai wakiltar Abuja a Majalisar dattawan Najeriya, Ireti Kingibe Hoto: Senator Ireti Kingibe
Source: Twitter

Sanata Kingibe ta bayyana hakan ne yayin wata hira da ta yi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.

Sanatar Abuja ta yi magana kan zaben 2027

Ta bayyana cewa babu wanda ta zaba a yanzu, amma za ta ba da cikakken goyon baya ga duk wanda ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027.

A cewar Sanatar ta Abuja, ita ’yar kishin ƙasa ce kuma ta rungumi ADC ne domin ƙarfafa adawa a Najeriya.

Ireti Kingibe ta ce:

“Ina kishin ƙasa. Gaskiya ita ce, Peter Obi zai iya zama ɗan takarar ADC a 2027, watakila kuma ba zai zama ba. Na shiga ADC ne domin tallafa wa jam’iyyar a matsayin adawa.
"Duk wanda ya samu tikitin takara, za mu yi aiki tare da shi. Idan Peter Obi ne, babu matsala. Idan kuma ba shi ba ne, duk wanda aka zaɓa, za mu mara masa baya.”

Kara karanta wannan

'Yan adawa sun tashi tsaye, PDP za ta gana da manyan jagororin ADC, Atiku da Peter Obi

Sanata Kingibe ta koka kan matsin rayuwa

Ta ƙara da cewa idan ’yan Najeriya suka zaɓi Bola Ahmed Tinubu, to hakan suke so, zai ci gaba da zama shugaban ƙasa, amma ta jaddada cewa ba ta goyon bayan ƙasar koma tsarin jam’iyya ɗaya.

Sanatar ta kuma ce ’yan Najeriya ba sa jin daɗin rayuwa a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu, inda ta bayyana cewa jama’a ba sa walwala kamar yadda ake tsammani.

Tutar ADC.
Tambarin jam'iyyar ADC ta Najeriya Hoto: @ADCParty
Source: Twitter

A cewarta, akwai buƙatar a rage nauyin haraji da ake ɗora wa ’yan ƙasa, tare da kiran shugaban ƙasa da ya sake duba yadda manufofinsa ke shafar rayuwar talakawa, in ji jaridar Guardian.

Dangane da ikirarin Shugaba Tinubu cewa wahalhalun da ake sha za su zama tarihi nan ba da jimawa ba, Sanata Kingibe ta ce ba ta da tabbacin ko ƙarshen yana gabatowa.

ADC ta tsaida dan takara a zaben 2027?

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta musanta jita-jitar cewa ta riga ta zabi wanda za ta ba tikitin takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ko Peter Obi?: ADC ta yi magana kan wanda za ta ba tikitin takara a 2027

ADC ta ce bai kamata a fassara kwararar da ’yan siyasa ke yi zuwa jam’iyyar a halin yanzu a matsayin wata yarjejeniya ta sirri kan wanda zai riƙe tutar jam’iyyar a zabe ba.

Kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ya jaddada cewa kofar jam’iyyar tana buɗe ga kowa, kuma babban burinta shi ne tabbatar da adalci ga dukkan mambobinta

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262