Shugaban APC Ya Fadi Yadda Yawan Gwamnoni zai Taimaki Tinubu a 2027
- Jam’iyyar APC ta ce karuwar yawan gwamnonin jihohi a cikinta na kara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu karfin tunkarar zaben 2027
- Shugaban APC na Kwara ya bayyana cewa jam’iyyar yanzu tana da iko a kusan jihohi 30, abin da ya saukaka shirin sake zaben shugaban
- An kaddamar da rajista da sabunta rajistar mambobin APC a Kwara a matsayin matakin farko na shirye-shiryen babban zabe mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kwara – Shugaban jam’iyyar APC a Jihar Kwara, Sunday Fagbemi, ya bayyana cewa karuwar yawan gwamnonin jihohi da ke karkashin APC na karfafa shugaba Bola Ahmed Tinubu a shirin lashe zaben shugaban kasa a 2027.
Fagbemi ya bayyana hakan ne a Ilorin yayin taron masu ruwa da tsaki da kuma kaddamar da rajistar intanet da sabunta rajistar mambobin jam’iyyar APC a jihar.

Source: Facebook
A sakon da gwamnatin Kwara ta wallafa a Facebook, ya ce wannan mataki na daga cikin dabarun jam’iyyar na karfafa gwiwar mambobi da kuma tanadin nasara a gaba.
A cewarsa, halin da jam’iyyar ke ciki a yanzu ya nuna karara cewa APC na kara fadada karfinta a fadin kasar, lamarin da ke nuna saukin tafiyar da yakin neman zabe ga shugaban kasa mai ci.
Yawan gwamnonin APC da tasirinsu a 2027
Sunday Fagbemi ya ce a taron Kwamitin Zartarwa na APC da aka gudanar a Disamban 2025, Shugaba Tinubu ya lura cewa jam’iyyar na da gwamnonin jihohi 28 a wancan lokaci.
A bayanin da shugaban APC ya yi, ya kara da cewa a yanzu, wasu karin gwamnonin sun shiga ko kuma suna dab da shiga jam’iyyar.
Ya ce:
“A halin yanzu muna da kusan gwamnonin jihohi 30. Idan aka duba wannan, yana nuna cewa sake zaben Shugaban kasa zai kasance cikin sauki. Abin da ya rage shi ne kowanne daga cikinmu a matakin jiha ya tabbatar da nasarar jam’iyyar a jiharsa.”
Fagbemi ya jaddada cewa karfin da jam’iyyar ke samu zai taimaka wajen hada kai da kuma tabbatar da aiwatar da manufofin APC a kowane mataki na mulki.
Gwamnan Kwara na girmama Tinubu
Shugaban APC a Kwara ya yabawa gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, yana mai cewa gwamnan ya nuna biyayya da kyakkyawar alaka da gwamnatin tarayya.
A cewarsa, wannan fahimta da hadin kai sun haifar da cigaba da dama a Kwara, ciki har da rangwamen haraji da wasu ayyuka na ci gaba da gwamnatin tarayya ta kawo jihar.
Daily Trust ta rahoto ya kara da cewa rajista da sabunta rajistar mambobi da ake yi a yanzu na nufin fara shimfida tubalin nasarar zaben 2027, ta hanyar tattara mambobi da masu kada kuri’a a karkashin jam’iyyar.
Maganar gwamnan AbdulRazaq a taron APC
Gwamna AbdulRazaq, wanda shi ne mutum na farko da ya yi rajista a yayin kaddamar da shirin, ya ce manufar aikin ita ce karfafa jam’iyyar da kuma samun sahihin bayanai domin tsara tsare-tsare yadda ya kamata.
Ya bukaci jami’an da ke kula da rajistar da su kasance masu bude kofa ga kowa, tare da gujewa ware wani mutum. Ya ce ya kamata a ba kowane dan kasa da ke da ke sha’awar shiga APC dama.

Source: Facebook
Gwamnan ya kara da cewa jam’iyyar na bukatar sanin adadin mambobinta domin tsara yakin neman zabe, kare kanta, da kuma karfafa mambobi ba tare da barin kowa a baya ba.
Peter Obi zai yi takarar 2027 a ADC
A wani labarin da ya shafi siyasa, mun kawo muku cewa jagoran magoya bayan Peter Obi, Dr Yunusa Tanko ya yi magana kan takarar 2027.
Yunusa Tanko ya bayyana cewa Peter Obi ya shiga ADC ne domin ya yi takarar shugaban kasa ba wai domin ya zama mataimakin wani ba.
Sai dai ya kara da cewa idan Obi ya samu nasara a 2027, zai dawo da mulki Arewa a zaben 2031 bayan kammala wa'adi daya kacal.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


