Jerin Kwamishinoni da Hadiman Abba da aka Hango a Taron Gidan Kwankwaso
- Yayin da siyasar Kano ta ɗauki zafi, an hango manyan jagororin Kwankwasiyya da ke gwamnatin Abba a taron gidan Rabi’u Musa Kwankwaso
- Taron ya zo a lokacin da ake ta jita-jitar yiwuwar sauya sheƙar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa APC lamarin da Kwankwaso ya yi tir da shi
- Haka kuma taron na zuwa a lokacin da Kwankwaso ke kalaman na rashin nasara a cin amana da neman a ba wa Gwamnan shawara kan sauya sheka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Masu rike da mukamai gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf sun halarci wani babban taro da tsohon dan takarar Shugaban Ƙasa, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi a gidansa.
Wasu daga cikin jagororin Kwankwasiyya da masu muƙamai da aka gani a taron gidan jagoran NNPP na ƙasa, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, sun haɗa da manyan ’yan siyasa da masu rike da muƙamai a gwamnati da jam’iyya.

Source: Facebook
Arewa Updates ta wallafa sunayen mutane akalla 35 da suke rike da kujeru daban-daban a gwamnatin Abba duk da dambarwar siyasa a Kwankwasiyya a shafin Facebook.
Masu mukaman gwamnatin Kano a taron Kwankwaso
Taron ya jawo ce-ce-ku-ce sosai, musamman ganin lokacin da aka yi shi, wato a yayin da ake ta rade-radin sauya sheƙar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.
Jerin sunayen da aka gani a taron sun hada da:
1. Hon. MB Aliyu, Dan Majalisar Jiha mai wakiltar Nasarawa
2. Abdullahi Musa Shugaban Ma’aikatan Kano
3. Musa Gambo Danzaki Sakataren Hukumar Tallafin Karatu ta Kano
4. Sadiq Muhammad Kura Shugaban gidan Zoo
5. Dr. Mansur Hassan Shugaban Kwankwasiyya Scholars
6. Hamisu Dogonnama MD, Kasuwar Kwari
7. Haj. A’in Jafaru Fagge SSA kan yaɗa ayyukan gwamnati

Source: Facebook
8. Haj. Fatima Amneef Shugabar hukumar KASPA
9. Ibrahim Ma’aji Sumaila SSA kan al'amuran ɗalibai
10. Hon. Isyaku Ali Danja SA kan batutuwan majalisa
11. Hon. Shakoor Yassar Shugaban CRC Kano
12. Balarabe Zawachiki, Shugaban Lafiya Jari
13. Sunusi Surajo Kwankwaso (SA, kan al'amuran siyasa
14. Habib Saleh Mailemo Shugaban Kano Pro-Pa
15. Usman Nura Getso PA a ofishin mataimakin Gwamna
16. Aisha Muhammad Idris SA kan samarda wadatar abinci
17. Sadiya Abdu Bichi, SA kan al'amuran mata, yara da masu buƙata ta musamman
18.Sadiya Umar Bichi, Mamba a KSCPC
19. Abdullahi Namama, mashawarci kan al'amuran gwamnati
20. Hamza Ahmad Telan Mata, PA a kan daukar hoto a ofishin mataimakin Gwamna
21. Shafa’atu Ahmad LondonBe (SSR, Ma'aikatar ci gaban karkara
22. Meenan Kwankwasiyya SSR a ma'aikatar matasa da wasanni
23. Inuwa Kwankwaso SSR, KNUPDA
24. Sulaiman Mainasara SSR, kankare zaizayar ƙasa
25. Yusuf Sulaiman Karkasara SSR, KSIP
26. Dr. Yusuf Kofar Mata,Kwamishinan Kimiyya da Fasaha
27. Adamu Aliyu Kibiya,Kwamishinan Agaji da Jinkai
28. Amina Abdullahi HOD,Kwamishinar Al'amuran Mata
29. Mustapha Kwankwaso,Kwamishinan Matasa da Wasanni

Kara karanta wannan
Dalilanmu na son Kwankwaso ya ja Abba zuwa APC inji Hadimin Gwamna Alhajiji Nagoda
30. AVM Ibrahim Umar,Kwamishinan Tsaron Cikin Gida
31. Hon. Hamza Kachako,Kwamishinan Ma'adinai
32. Sani Adamu Wakili, 'Dan Majalisar Wakilai, Minjibir/Ungogo
33. Abdulhakim Kamil Ado, 'Dan Majalisar Wakilai, Wudil/Garko
34. Datti Yusuf Kura, 'Dan Majalisar Wakilai, Kura/Madobi/Garunmalam
35. Hon. Muntari Yarima, 'Dan Majalisar Wakilai, Tarauni
Ra'ayin jama'a game da siyasar Kano
Jama'a sun bayyana mabambantan ra'ayoyi game da mutanen da suka halarci taron Kwankwaso, inda Isma’ila Abubakar Ahmad ya ce:
“To me ya ruwan ku, wallahi ku munafukai ne.”
Amina Muhd ta bayyana cewa:
“Ba laifi ba ne su je, idan ma Abba ya kira taro gobe za su je.”
Kwankwaso ya faɗi bambancinsa da sauran ƴan siyasa
A baya, mun wallafa cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa shi ba ɗan siyasa ba ne da ke da farashi ko abin da za a iya sayensa da kuɗi ba.
Ya faɗi hakan ne yayin da yake tsokaci kan halin siyasar Najeriya a baya-bayan nan, musamman a daidai lokacin da ake zargin yiwuwar sauya sheƙar Gwamnan Kano.
Kwankwaso ya ce siyasa tana cike da riba da asara, amma ya jaddada cewa cin amana abu ne da ke janyo fushin jama’a da kuma rasa amincewarsu a kowace irin tafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


