Kwankwaso Ya Fadi Baiwarsa da Abin da Ya Bambanta Shi da Sauran Ƴan Siyasa
- Tsohon ɗan takarar Shugaban Ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce shi ɗan siyasa ne da ba a saye shi da kuɗi
- Ya bayyana siyasar Kano a matsayin wadda jama’a ke da wayewa kuma ba sa yarda da cin hanci sai dai ra'ayin kansu
- Yayin da ake batun sauya sheƙar Gwamnan Kano, Kwankwaso ya gargadi ’yan siyasa da masu zaɓe kan amincewa da ribar gajeren lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa shi ba ɗan siyasa ba ne da ke da farashi.
Ya faɗi hakan ne yayin da yake tsokaci kan halin siyasar Najeriya a baya-bayan nan, musamman yadda lamuran ke gudana a Kano na zargin sauya shekar Gwamna.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa Kwankwaso ya ce siyasa tana tattare da riba da asara, amma ya jaddada cewa cin amana abu ne da ke janyo fushin jama’a.
Rabiu Kwankwaso ya yi kan kunne a Kano
Aminiya ta ruwaito Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kara da cewa kowa na da masaniya a kan cewa amana abu ce mai kyau kuma jam'iyyu na rasa goyon baya a yanzu.
Ya ce:
“Rayuwa haka take; wani ya yi riba, wani ya yi asara. Amma mun san cewa cin amana ba abu ne mai kyau ba. Kowa ya san yadda wasu jam’iyyu ke rasa goyon bayan jama’a, musamman game da matsalar tsaro da tattalin arziki."
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa siyasar Kano ta bambanta da ta wasu sassan Najeriya, yana mai cewa al’ummar Kano suna da wayewar kai ta siyasa kuma ba sa yarda a ruɗe su da kuɗi.
Kwankwaso ya yabi siyasar Kano
A cewarsa, ba abu ne mai sauƙi ba a Kano ka zo da jaka cike da kuɗi ka yi tunanin za ka sayi ra’ayin jama’a, amma su baɗa maka kasa a ido.
A kalaman tsohon Gwamnan:
“Siyasar Kano ta daban ce. Idan ba a Kano ba, a ina ne za ka samu ka zo da kuɗi ka shiga taro ka ce za ka ba mutane abubuwa su canja ra’ayinsu?”

Source: Facebook
Kwankwaso ya yi watsi da ra’ayin da wasu ke yadawa cewa duk ’yan siyasa ana iya sayen su. Ya ce duk wanda ke neman ɗan siyasa da ba shi da farashi, to ya dubi Rabiu Musa Kwankwaso.
Ya ce:
“Ana cewa a Najeriya kowa na da farashi. Idan kana neman wanda ba shi da farashi, ka zo wurin Rabiu Kwankwaso."
Tsohon Sanatan ya ƙara da cewa idan burinsa kuɗi ne, da ya iya saka wa kansa farashi tun tuni. Ya kuma gargadi ’yan siyasa da masu kaɗa ƙuri’a da su guji rungumar ribar gajeren lokaci, musamman a lokacin zaɓe.
Kwankwaso ya ce a lokuta da dama ana bai wa jama’a kuɗi ko kayan abinci na ɗan lokaci, amma daga bisani su shafe shekaru huɗu suna fama da wahala.

Kara karanta wannan
Dalilanmu na son Kwankwaso ya ja Abba zuwa APC inji Hadimin Gwamna Alhajiji Nagoda
Ya ce:
“Za ka yi shekara huɗu kana shan wahala, sai rana ɗaya su zo su ba ka kaɗan, daga nan kuma ka sake shafe wata huɗu."
Ya buƙaci shugabanni da masu ruwa da tsaki a siyasa su tsaya kan ƙa’ida, su yi siyasa domin muradun jama’a na dogon lokaci. Ya yi gargaɗin cewa shugabanci da aka gina kan cin hanci da cin amana ba zai kawo ci gaba mai ma’ana ga al’umma ba.
Abin da zai jawo rabuwa da Kwankwasiyya
A baya, mun kawo labarin cewa Mai bai wa Gwamnan Jihar Kano shawara kan harkokin tattalin arzikin zamani, Yusuf Sharada, ya bayyana dalilan da wasu ke son barin Kwankwasiyya.
Yusuf Sharada ya danganta wannan yunƙuri da abin da ya kira neman wasu fa’idoji na siyasa da tattalin arziki, waɗanda a cewarsa wasu ’yan Kwankwasiyya ke ganin a APC za a samu.
Ya ce ana hana Kano wasu abubuwan saboda jam’iyyarsu ba ita ce ke rike da mulkin tarayya ba. Ya ce wannan fahimta ta sa wasu ke kallon sauya sheka a matsayin alheri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

