Datti Baba Ahmed Ya Ayyana Tsayawa Takarar Shugaban Kasa, Ya Kara da Tinubu a 2027

Datti Baba Ahmed Ya Ayyana Tsayawa Takarar Shugaban Kasa, Ya Kara da Tinubu a 2027

  • Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed ya bayyana aniyarsa ta tsatawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 karkashin inuwar jam'iyyar LP
  • Baba-Ahmed ya bayyana kudurinsa mako guda bayan tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya fice daga LP zuwa ADC
  • Bayan fadin matsayarsa a taron jam'iyya, tsohon abokin takarar Obi ya bayyana abun da zai hana shi fara yakin neman zabe yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed, wanda shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, ya ayyana tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2027.

Datti ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 7 ga Janairu, 2026, yayin wani gangamin mambobin jam’iyya da aka gudanar a sakatariyar LP ta ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan adawa sun tashi tsaye, PDP za ta gana da manyan jagororin ADC, Atiku da Peter Obi

Datti Baba Ahmed ya ayyana neman kujerar shugaban kasa a 2027
Datti Baba Ahmed, tsohon abokin takarar Peter Obi a 2023 yana jawabi ga manema labarai a Abuja. Hoto: @dattibabaahmed
Source: Twitter

Datti Baba-Ahmed zai nemi takarar shugaban kasa

Bayyana aniyarsa da Datti Baba Ahmed ya yi na zuwa ne mako guda kacal bayan Peter Obi ya fice daga jam’iyyar LP ya koma ADC, in ji rahoton Punch.

Datti ya jaddada cewa burinsa na zama shugaban ƙasa ba ya dogara da matakin Peter Obi ba, kuma ya tunatar da jama'a cewa ya nemi wannan matsayi tun kafin Peter Obi ya shigo jam'iyyar a 2023.

Ya bayyana cewa ya taɓa yin takara a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar PDP a 2018 kafin ya amince ya zama abokin takarar Obi a 2023 don ci gaban ƙasa.

'Dan siyasar ya kuma bayyana cewa kasancewarsa Musulmi kuma Bahaushe bai hana shi takara ba domin kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba shi wannan damar.

Matsayar jam’iyyar LP kan siyasar 2027

Shugaban jam’iyyar LP, Julius Abure, ya yaba wa Datti Baba-Ahmed bisa jajircewarsa na zama a cikin jam’iyyar duk da sauya shekar Obi.

Kara karanta wannan

An fadi shekarun da mulki zai yi a Kudu kafin ya dawo yankin Arewa

Abure ya bayyana cewa LP tana nan daram da karfinta, inda ya bayyana cewa manyan jiga-jigan jam’iyyar kamar Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, duka suna nan a cikinta.

Wannan magana ta kwantar da hankalin mambobin jam'iyyar da ke fargabar rugujewarta saboda sauya shekar Obi, a cewar rahoton jaridar Leadership.

Datti Baba Ahmed ya ce dalilinsa na tsayawa takarar bai shafi ficewar Obi daga jam'iyyar LP ba.
Julisu Abure ya daga hannun Peter Obi da na Datti Baba-Ahmed lokacin da suka samu tikitin takara karkashin LP a 2022. Hoto: @dattibabaahmed
Source: UGC

Datti Baba-Ahmed zai jira umarnin INEC

Datti Baba-Ahmed ya kuma yi bayani cewa ko da yake ya fito da kudurinsa a fili, zai bi dukkan dokokin hukumar INEC da na jam’iyyar LP wajen gudanar da harkokinsa.

Ya bayyana cewa ba zai ƙara cewa uffan kan kudurinsa na yin takara ba har sai lokacin da hukumar INEC ta fitar da jadawalin zaɓen 2027.

A cewarsa, Najeriya tana buƙatar agajin gaggawa, kuma shi ya shirya tsaf domin bayar da tasa gudunmawar wajen ceto ƙasar daga matsalolin da take ciki.

Fasto Odumeje zai fito takarar shugaban kasa

A wani labari, mun ruwaito cewa, Fasto Chukwuemeka Cyril Ohanaemere da aka fi sani da Odumeje ko Indasbosky ya nuna sha'awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.

Odumeje, wanda ya assasa Cocin Mountain of Holy Ghost Intervention da Deliverance Ministry ya bayyana aniyarsa a fili ne a yayin da yake wa'azi ga mabiyansa a cikin majami'ar.

Malamin addinin Kiristan wanda ya saba fadin maganganun da ke jawo ce-ce-ku-ce, ya bayyana cewa Najeriya na bukatar matashi a matsayin shugaban kasa mai jini a jika kamarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com