Hadimin Abba Ya Fadi Abin da ke Shirin Kora 'Yan Kwankwasiyya zuwa Jam'iyyar APC
- Mai bai wa Gwamnan Kano shawara kan tattalin arzikin zamani, Yusuf Sharada, ya ce akwai abin da ke sa 'yan Kwankwasiyya zuwa APC
- Yusuf Sharada ya bayyana cewa kasancewar Kano ba ta jam’iyyar da ke mulkin tarayya ba na hana jihar cin gajiyar wasu manyan ayyuka
- Hadimin ya kuma nuna fargaba kan rikice-rikicen shari’a a NNPP yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa, wanda zai iya zama masu barazana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Mai bai wa Gwamnan Kano shawara kan tattalin arzikin zamani, Yusuf Sharada, ya bayyana dalilan da suka sa wasu 'yan Kwankwasiyya ke shirin sauya sheka zuwa APC.
Yusuf Sharada ya danganta wannan mataki da bukatar samun wasu fa’idoji da suke ganin ana hana su saboda ba su cikin jam’iyyar da ke mulkin tarayya.

Source: Facebook
Channels TV ta wallafa cewa hadimin Gwamnan ya fadi haka ne a ranar Laraba yayin wata hira da ya yi a shirinta na "The Morning Brief."
Dalilin wasu 'yan Kwankwasiyya na son komawa APC
A cewarsa, akwai al’amura da dama da suka sa suka fahimci cewa wasu matsaloli na tasowa ne saboda Kano ba ta cikin jam’iyyar da ke rike da iko a matakin tarayya.
Ya ce:
“Akwai abubuwa da dama da suka sa muka yanke shawarar cewa watakila duk wannan yana faruwa ne saboda ba mu cikin jam’iyyar da ke mulkin ƙasa. Akwai ayyuka da dama da suka fi ƙarfin ikon jiha kaɗai.”
Yusuf Sharada ya ƙara da cewa wasu jihohi da ke karkashin jam’iyyar da ke mulki a tarayya na cin gajiyar manyan ayyuka da tallafi, alhali Kano ba ta samun irin wannan dama.
Hadimin Gwamna ya shiga fargabar zaben 2027
Mai ba gwamnan shawarar ya amince cewa Kano na karɓar rabonta daga tarayya, amma ya ce hakan bai wadatar ba wajen kawo gagarumin ci gaba.

Kara karanta wannan
Dalilanmu na son Kwankwaso ya ja Abba zuwa APC inji Hadimin Gwamna Alhajiji Nagoda

Source: Facebook
A kalamansa:
“Muna so mu ƙara wa Kano ayyukan ci gaba, saboda abin da muke samu a yanzu bai isa ba."
Haka kuma, Yusuf Sharada ya bayyana fargaba game da rikice-rikicen shari’a da ke addabar jam’iyyar NNPP, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
Ya ce abin da ya faru a Jihar Zamfara (a zaben 2019) darasi ne da ya kamata a koya, saboda haka wasu ke hararar koma wa APC.
Ya ce:
“Mun ga abin da ya faru a Zamfara, kuma ba ma son ya sake faruwa a Kano. Shi ya sa muke neman wata hanya mafi aminci da za ta ba duk masu rike da muƙaman zaɓe damar sake tsayawa takara, idan jama’a suka ba su dama su ci gaba da mulkin jihar."
“Ba na cewa an hana mu haƙƙinmu gaba ɗaya. Amma idan kana a adawa, ba lallai ba ne ka samu duk abin da kake so."
Abba ya samu goyon-bayan koma wa APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon ɗan takarar gwamnan Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya yi magana kan rade-radin da ke yawo game da sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Malamin ya bayyana cewa tun bayan fara jita-jitar sauya shekar, babbar baraka ta shiga tsakanin gwamnan da tafiyar Kwankwasiyya, saboda haka Gwamna ya tattara kayansa zuwa APC.
A cewarsa, abubuwa sun kai wani matsayi da ba za a iya cewa har yanzu akwai cikakkiyar fahimta ko amincewa tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwankwasiyya ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

