Sheikh Ibrahim Khalil Ya Shawarci Gwamna kan Rabuwa da Kwankwaso zuwa APC

Sheikh Ibrahim Khalil Ya Shawarci Gwamna kan Rabuwa da Kwankwaso zuwa APC

  • Sheikh Ibrahim Khalil ya shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC gaba ɗaya
  • Ya ce dangantaka tsakanin Abba Kabir Yusuf da Kwankwasiyya ta riga ta lalace, saboda haka sauya sheka ce ta saura
  • Malamin ya bayyana cewa sauya shekar Abba na ɗauke da alheri ga Kano, Arewa da Najeriya ta fuskoki da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon ɗan takarar Gwamnan Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf dangane da yunƙurinsa na sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Malamin ya bayyana cewa tun bayan da maganganu suka fara yawo kan cewa Gwamnan Kano na shirin sauya sheka, wata babbar baraka ta shiga tsakanin Abba Kabir Yusuf da Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

Garba Kore ya bankado shirin Kwankwasiyya na ƙwace kujerar Abba a Kano

Gwamna ya samu goyon baya kan komawa APC
Gwamna Abba Kabir Yusuf a cikin farin ciki Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da Arewa Updates, wadda aka wallafa a shafin Facebook, Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa daga yanzu babu sauran amincewa ko fahimta tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwankwasiyya.

Shawarar Sheikh Ibrahim Khalil ga Gwamna Abba

A cikin hirar, Sheikh Ibrahim Khalil ya shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya koma jam’iyyar APC gaba ɗaya, saboda a cewarsa babu wani abin da ya rage a tsakaninsa da Kwankwasiyya.

Ya ce ko da Gwamnan ya ce ba zai sauya sheka ba, tuni ya karya alakar siyasa da Kwankwasiyya kuma babu sauran yarda a tsakaninsu.

Sheikh Ibrahim Khalil ya shawarci Abba ya rike damarsa
Sheikh Ibrahim Khalil yayin bayani a wani taro Hoto: Khalil Network
Source: Facebook

A kalamansa, ya ce:

“In ya ce ma ba zai koma ba, to ai ya riga ya karya alaka tsakaninsa da Kwankwasiyya. Kuma ya riga ya zo da abin da su Kwankwasawa zai yi wahala su yarda da shi a zaɓe na gaba, haka kuma zai yi wahala su yarda a ba shi tikiti.”

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda Gwamna Abba ya yi alkawarin kin yi wa Kwankwaso butulci

Ya ƙara da cewa:

“Ba abin da ya rage masa illa ya tafi APC. Ko da daɗi ko ba daɗi, ya tafi kada ya yi wasa da hakan. Kuma yana da muƙami, shi ne zai ɗauki kashi 40 ko 50 cikin 100, ragowar kuma a bar wa mutane.”

Sheikh Ibrahim Khalil ya ce tun da maganganu sun yi ƙarfi kan batun sauya sheka, ya dace Gwamnan ya gaggauta rungumar matsayar da ya ɗauka.

Malami ya gano alheri a sauya shekar Abba

Sheikh Ibrahim Khalil, wanda shi ne Shugaban Zaure na Malamai a Jihar Kano, ya bayyana cewa akwai alheri mai tarin yawa a sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya ce wannan mataki na iya amfanar Kano, Arewa da Najeriya baki ɗaya, da shi kan shi jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

A cewarsa:

“Mu mun san akwai alheri mai yawa ga Kano da Arewa da Najeriya, kuma hakan zai taimaka wa dimokuraɗiyya da siyasa. Zai taimaka wa shi kansa Kwankwaso, zai kuma ƙara masa girma da ƙarfi da ɗaukaka, har da ita kanta Kwankwasiyya.”

Kara karanta wannan

Dalilanmu na son Kwankwaso ya ja Abba zuwa APC inji Hadimin Gwamna Alhajiji Nagoda

Sheikh Ibrahim Khalil ya ƙara da kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya jajirce idan ya koma APC, tare da karɓar ragamar jam’iyyar kamar yadda tsarin jam’iyyar ya tanada.

Ya ce kada ya yi sakaci da haƙƙinsa na shugabanci da jagoranci a APC, kada kuma ya raina matsayinsa.

Malamin ya kammala da cewa yanzu ba lokaci ba ne na sakaci, yana mai cewa idan Gwamnan ya tsaya wasa, zai rasa duka bangarorin biyu.

Ana son raba Abba da kujerar Gwamna

A wani labarin, mun wallafa cewa fitaccen ɗan siyasa a jam’iyyar APC, Garba Kore Dawakin Tofa, ya bayyana cewa wasu manyan Kwankwasiyya na son kwace kujerar Abba.

Garba Kore ya ce mutanen da ke kiran kansu amintattun Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun yiwa Gwaman Abba barazana cewa za su ba Ahmad Garba Bichi takarar gwamna.

Ya ƙara da cewa Kwankwaso bai fito fili ya ƙaryata hakan ko ya tsawatar wa magoya bayansa ba kan ci gab ad furta kalaman ba, wanda ya sa dole Gwamna ya dauki mataki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng