Malami Ya Fadi Manyan Najeriya 3 da Za Su Tilasta wa Atiku Janye wa Jonathan

Malami Ya Fadi Manyan Najeriya 3 da Za Su Tilasta wa Atiku Janye wa Jonathan

  • Fasto Elijah Ayodele ya yi magana kan yadda za a lallashi Atiku Abubakar ya janye neman takararsa ta shugaban kasa a zaben 2027
  • Ya bayyana cewa kungiyoyin kasa da kasa da manyan ‘yan siyasar Najeriya za su mara wa wannan shiri baya domin cire Bola Tinubu
  • Limamin ya gargadi cewa Amurka, karkashin Donald Trump, za ta zama babbar barazana ga mulkin Tinubu idan bai dauki mataki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Fasto Elijah Ayodele, ya bayyana damuwa game da zaben 2027.

Ayodele ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai fuskanci matsin lamba domin ya janye takararsa ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Fasto ya yi hasashe kan zaben 2027 tsakanin Atiku da Jonathan
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Fasto Elijah Ayodele da Atiku Abubakar. Hoto: Goodluck Jonathan, Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Zargin hannun kasashen waje a siyasar 2027

Hakan na cikin wata sanarwa da mataimakinsa na yada labarai, Osho Oluwatosin, ya sanya wa hannu, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun kawo sabon salo a tsarin marawa 'yan takara baya a 2027

Ayodele ya ce kasashen duniya da kungiyoyi irin su Tarayyar Afirka (AU), Tarayyar Turai (EU), Amurka, tare da wasu manyan ‘yan siyasar Najeriya, za su kasance a bayan wannan shiri.

Ya ambaci sunayen TY Danjuma, Abubakar Abdulsalami, da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin wasu daga cikin manyan masu goyon bayan shirin.

Fasto Ayodele ya ce za a shawo kan Goodluck Jonathan ya shiga hadakar ‘yan adawa domin fuskantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

A cewarsa, manufar wannan shiri ita ce Jonathan zai yi wa’adi guda daya ne kacal idan ya samu nasara, sannan a yi amfani da shi wajen kwace mulki daga jam’iyya mai mulki.

Ya ce:

“Ina ganin AU, Birtaniya, Amurka, EU, da wasu ‘yan siyasa na cikin gida kamar TY Danjuma, Abdulsalami da Obasanjo za su nemi Atiku ya janye wa Jonathan kafin zaben 2027, har ma a cikin hadaka.
“Za su tilasta wa Jonathan shiga hadakar tare da tabbatar da cewa shi ne zai samu tikitin takara domin kalubalantar Tinubu. Wannan shiri ne mai wahala, amma tuni na hango ana tsara shi."

Kara karanta wannan

'Babu wani mahaluki': Atiku ya magantu kan janye takarar shugaban kasa a 2027

An gargadi Tinubu kan zaben 2027 da ke tafe
Shugaba Bola Tinubu yana addu'a yayin taro. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

“Tinubu bai san abin da da ake shiryawa ba”

Fasto Ayodele ya kara da cewa tattaunawar wannan shiri ta fara tun karshen watan Disambar 2025, amma Shugaba Tinubu bai da masaniya kan abin da ake kullawa a kansa.

Limamin ya kuma sake jaddada hasashen da ya taba yi cewa Amurka za ta yi wa gwamnatin Tinubu katsalandan, musamman saboda manufofin shugaban Amurka, Donald Trump.

A cewarsa:

“Kamar yadda na fada a baya, Amurka ce za ta zama babbar ‘yar adawa ga Tinubu. Burin Trump shi ne ganin Tinubu ya bar kujerar mulki, sai dai idan shugaban ya dauki mataki mai karfi na siyasa.”

Ya yi gargadin cewa kasashen duniya za su tsoma baki a zaben Najeriya na 2027, yana mai cewa ya zama dole ‘yan siyasa da ‘yan kasa su kasance cikin taka-tsantsan, cewar Daily Post.

Fasto Ayodele ya ce tsoma bakin kasashen waje a harkokin zaben Najeriya na iya haifar da matsala idan ba a yi hattara ba, yana mai jaddada cewa wannan al’amari na bukatar kulawa sosai daga bangaren gwamnati da al’umma gaba daya.

Kara karanta wannan

Bayan barin kujerar minista, Badaru ya magantu kan jita jitar watsar da APC

'Amurka na maka makarkashiya' - Fasto ga Tinubu

Mun ba ku labarin cewa Fasto Elijah Ayodele ya gargadi Shugaba Bola Tinubu game da rashin tsaro da kuma manakisar kasar Amurka a Najeriya.

Ayodele ya bayyana cewa shugaban Amurka, Donald Trump, na shirin ganin an cire Bola Tinubu daga mulki.

Limamin ya ce tallafin tsaro da Amurka ke bai wa Najeriya ba wai don kawo karshen rashin tsaro ba ne, illa wata manufa ta daban.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.