Abin da Kwankwaso da Ganduje Suka Fadawa Abba Ana Batun Shigarsa APC

Abin da Kwankwaso da Ganduje Suka Fadawa Abba Ana Batun Shigarsa APC

  • Saƙonnin taya murna na cikar gwamna Abba Kabir Yusuf shekara 63 sun kasance suna ɗauke da bayanan siyasa masu zurfi a wannan karon
  • Abdullahi Umar Ganduje da Rabiu Musa Kwankwaso sun aike da saƙonni masu ma’ana daban-daban, abin da ya tayar da rade-radi kan siyasa
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake rade radin cewa gwamna Abba Kabir Yusuf zai koma jam'iyyar APC daga NNPP mai mulki a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Zagayowar ranar haihuwar Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, karo na 63, ta zama wata dama da ta fito da alamu na sauyin kawance da sabon lissafin siyasa a jihar.

Saƙonnin taya murna da manyan jagorori suka fitar sun ja hankalin masu sa ido kan siyasar Kano da ma Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda Gwamna Abba ya yi alkawarin kin yi wa Kwankwaso butulci

Abba Kabir Yusuf, Abdullahi Ganduje, Rabiu Kwankwaso
Tsohon shugaban APC, Abdulahi Ganduje, gwamna Abba Kabir Yusuf da Rabiu Kwankwaso. Hoto: All Progressive Congress|Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Rahoton Business Day ya nuna cewa abin da ya fara a matsayin taya murna ya rikide zuwa wata alama ta siyasa, inda kalmomin da aka yi amfani da su suka nuna yiwuwar sulhu, daidaitawa, da sauyin alaka.

Saƙon Ganduje ga Abba Kabir Yusuf

Tsohon gwamnan Kano kuma tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, na daga cikin fitattun mutanen da suka taya gwamna Abba Kabir murna.

A saƙonsa, Ganduje ya bayyana ranar a matsayin lokaci na nazari kan jagoranci da ƙara jajircewa wajen yi wa jama’ar Kano hidima.

Rahotanni sun nuna cewa baya ga yi masa fatan samun lafiya da hikima, saƙon Ganduje ya ƙunshi kalmomi da ke ɗauke da ma’anar siyasa.

Ya bayyana maraba da abin da ya kira daidaituwar gwamnan da APC, yana mai bayyana hakan a matsayin nuna hangen nesa da daukar matakin da ya dace.

Ganduje ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa wannan dangantaka za ta haifar da manufofi da suka mayar da hankali kan jama’a, daidai da ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fito da abubuwan alheri da ya yi wa Abba Kabir a baya

Legit Hausa ta kura da yadda na-kusa da gwamnati suka karbi wannan sako, daga ciki har da Shugaban hukumar KASA, Kabir Dakata da ya yabawa Abdullahi Ganduje.

Saƙon Kwankwaso ga Abba Kabir Yusuf

A gefe guda, jagoran Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, shi ma ya taya Abba Kabir Yusuf murna.

Sakon da Sanata Rabiu Kwankwaso ya wallafa a Facebook ya fi karkata ga kira ga shugabanci na bai ɗaya da hidima ga al’umma, ba tare da jaddada batun jam’iyya ba.

Masu nazari sun fassara bayanin a matsayin tunatarwa game da ci gaba da aiki bisa tsarin Kwankwasiyya a Kano da sha’awarsa kan alkiblar mulkin Abba Kabir Yusuf.

Tsohon gwamnan ya yi amfani da damar wajen tunawa Abba irin damammakin da ya ba shi tun yana gwamna har ya zama minista zuwa kuma dawowarsa gwamnati a 2015.

Madugun Kwankwasiyyar ya kare da yin wata addu'a da ke nuna alamun gwamnan yana neman sakin tafarkin da aka san shi a kai na shekara da shekaru.

Rabiu Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf
Rabiu Kwankwaso na tattaunawa da Abba Kabir Yusuf. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Saƙon Tinubu ga Abba Kabir Yusuf

Kara karanta wannan

Bayan shirin barin Kwankwaso, da gaske Abba Kabir zai tarbi Aminu Ado Bayero?

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika da saƙon taya murna, yana yabawa Abba Kabir Yusuf bisa nagarta, tawali’u, da jajircewa.

Shugaban Najeriyan ya ƙarfafa gwamnan da ya ci gaba da isar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar Kano domin inganta rayuwarsu ta yau da kullum.

Tinubu ya bayyana sabuwar shekarar da gwamnan ya shiga a matsayin lokaci na zurfafa haɗin gwiwa domin cimma manufofin ci gaban ƙasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng