APC Ta Bugi Kirji, Ta Fadi Adadin Kuri'un da Tinubu Zai Samu a Filato a 2027

APC Ta Bugi Kirji, Ta Fadi Adadin Kuri'un da Tinubu Zai Samu a Filato a 2027

  • Farfesa Nentawe Yilwatda ya tabbatar da cewa jihar Filato za ta ba Shugaba Bola Tinubu dubunnan daruruwan kuri'u a zaben 2027
  • A cewar shugaban APC na kasa, sauya shekar Gwamna Caleb Mutfwang daga PDP zuwa jam'iyyarsu babbar nasara ce a gare su
  • Yilwatda ya kuma kawo karshen fargabar da mambobin jam'iyyar suke yi na cewa sababbin zuwa na iya kwace dukkan ikon APC a Filato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa jihar Filato za ta ba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ƙuri’u sama da miliyan ɗaya a zaɓen 2027.

Yilwatda ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 6 ga Janairu, 2026, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na mazaɓar Pankshin, Kanke, da Kanam (PKK) da aka gudanar a Pankshin.

Kara karanta wannan

Babban alkawarin da APC ta yi wa Gwamna Caleb bayan komawarsa jam'iyyar

Jam'iyyar APC ta ce Tinubu zai samu fiye da kuri'u miliyan 1 a Filato a 2027
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin gwamnan Filato, Caleb Mutfwang a Aso Rock, Abuja. Hoto: @CalebMutfwang
Source: Twitter

2027: APC ta hango nasarar Tinubu a Filato

A cewarsa, jam’iyyar APC yanzu ta fi kowane lokaci ƙarfi a jihar duba da yadda dukkan manyan shingayen adawa suka rushe, a cewar rahoton Punch.

Wannan sanarwa tana zuwa ne kwanaki kaɗan bayan babban sauyin siyasa a jihar, inda Gwamna Caleb Mutfwang ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a ranar 2 ga Janairu, 2026.

Farfesa Yilwatda ya jaddada cewa shigowar gwamnan, kwamishinoninsa, da shugabannin ƙananan hukumomi cikin APC ya sa jam’iyyar ta zama "garke guda" ba tare da wata hamayya ba.

Ya bayyana yankin PKK a matsayin tungar APC inda Shugaba Tinubu ya samu gagarumar nasara a 2023, kuma yana sa ran wannan nasarar za ta ninka a 2027.

Sauyin salon siyasar shugaban APC

Farfesa Nentawe Yilwatda, wanda shi ne tsohon ɗan takarar gwamnan Filato na APC a 2023, ya bayyana cewa yanzu salon siyasarsa ya canza.

Kara karanta wannan

Jagora a APC ya hango abin da zai wargaza jam'iyya, ya bada shawara tun wuri

Ya sha alwashin daina sukar Gwamna Mutfwang a bainar jama'a, yana mai cewa tunda yanzu duka suna jam'iyya ɗaya, zai riƙa kiran gwamnan a waya ko ziyartarsa don ba shi shawarwari kan yadda za a inganta mulki.

Wannan mataki na nuna tsantsar haɗin kai da ake fatan zai kawo ƙarshen rarrabuwar kawuna a siyasar jihar Filato, a cewar rahoton Daily Trust.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda
Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda yana jawabi a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Pankshin, jihar Filato. Hoto: @Imranmuhdz
Source: Twitter

An kore fargabar tsofaffin mambobin APC

Game da fargabar wasu tsofaffin 'yan APC cewa sababbin mambobin da ke shiga za su iya ƙwace madafun ikon jam'iyyar, Yilwatda ya kwantar musu da hankali.

Ya bayyana cewa APC tana da isasshen wurin zama ga kowa, kuma dukkan mambobi za su sami daidaiton damarmaki komai daɗewarsu a cikin jam’iyyar.

Ya umarci shugabannin mazaɓu da su karɓi sababbin mambobi da hannu biyu-biyu domin gina dandalin da za ta share fage ga nasarar Shugaba Tinubu a zaɓe mai zuwa.

Tinubu ya fusata kan kashe-kashe a Plateau

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin cewa za a kama ƴan bindigan da suka kashe mutanen wasu ƙauyuka a jihar Filato.

Tinubu ya kuma buƙaci al’ummomin da lamarin ya shafa su haɗa kai da hukumomi da jami’an tsaro ta hanyar ba da bayanai domin a kama masu laifin.

Ya tabbatarwa Gwamna Mutfwang samun cikakken goyon bayansa wajen kawo ƙarshen wannan mummunan kashe-kashe da ke faruwa a Plateau.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com