Garba Kore Ya Bankado Shirin Kwankwasiyya na Ƙwace Kujerar Abba a Kano
- Garba Kore ya zargi manyan Kwankwasiyya da yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf barazana tun kafin zaɓen 2027
- Fitaccen dan siyasar ya ce Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai fito fili ya tsawatar da magoya bayansa ba
- Garba Kore ya bayyana cewa jiga-jigan Kwankwasiyya sun sanar da cewa za a kwace takara daga hannun Abba a badi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Fitaccen ɗan siyasa a jam’iyyar APC a jihar Kano, Garba Kore Dawakin Kudu, ya bayyana cewa wasu manyan Kwankwasiyya, sun yi wa Gwamna barazana.
A cewarsa, tun yanzu aka fara bayyana shirin kwace kujerar gwamnan a zaɓen shekarar 2027, abin da ya ce ya sa dole Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake tunani.

Source: Facebook
Garba Kore ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi, wadda aka wallafa a shafin Facebook na Express Radio.
Kwankwasiyya na wa Abba barazana – Garba Kore
Garba Kore ya ce mutanen da ke kiran kansu amintattun Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suna yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf barazanar cewa za a miƙa kujerarsa ga Ahmad Garba Bichi.
A kalamansa:
“An yi wa Abba barazana kala-kala cewa Ahmad Garba Bichi za a ba takarar gwamna. Me Abba ya yi? Su da suke wannan magana, Kwankwaso bai fito ya ce wa mutanen nan ba wannan magana, bai tsawatar ba. Ko akwai ta a bar ta sai ta zo, sai a danne Abba.”
Ya ƙara da cewa an riga an faɗa wa gwamnan tun yanzu cewa babu dalilin da zai sa ya ci gaba da zama a inda zai cutu.
Garba Kore ya jaddada cewa waɗanda ke aikata hakan su ne mutanen da ake kallon su a matsayin masoyan Kwankwasiyya na gaskiya, amma a ganinsa “munafukai” ne.

Kara karanta wannan
Dalilanmu na son Kwankwaso ya ja Abba zuwa APC inji Hadimin Gwamna Alhajiji Nagoda
Garba Kore ya ga laifin Abba Gida Gida
Garba Kore ya bayyana cewa bai ji daɗin yadda gwamnan ya ƙi fitowa ya yi wa al’umma cikakken bayani game da halin da ake ciki ba.

Source: Facebook
Jigon a APC ya ce:
“Abba ya yi hankali, amma sakacinsa da kuskurensa ne ya sa ya ƙi yin ƙarin bayani kan yadda abin ya taho. Ya san jam’iyyar da ya taho babu cikakkiyar jam’iyya mai ƙarfi.”
Garba Kore ya ayyana cewa tun a lokacin da Gwamna Abba ya yi maganar manya da yara na cin amana, ya gane cewa da Kwankwaso ya ke.
Garba Kore na son Abba ya koma APC
A baya, mun wallafa cewa Garba Kore Dawakin Kudu, ya bayyana jin dadi game da shirin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na sauya sheka zuwa APC mai mulki.
Ya ce matakan da gwamnan ke ɗauka a halin yanzu sun nuna ƙudurinsa na yi wa al’ummar Kano aiki ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ko ra’ayi ba.
A cewarsa, abubuwan da ke faruwa a fagen siyasar Kano sun nuna cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na ƙoƙarin ɗaukar matakai masu amfani da za su amfani jihar Kano gaba ɗaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

