Kotun Kano Ta Takawa Shugabannin NNPP Masu Biyayya ga Kwankwaso Birki
- Babbar kotun Kano ta ayyana rusa shugabannin jam'iyyar NNPP a matakin jiha, kananan hukumomi da mazabu a matsayin ba bisa ka’ida ba
- Kotun ta kuma hana kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar daukar wani sabon mataki kan shugabancin NNPP a Kano har sai an yanke hukunci
- Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara rikicin siyasa tsakanin Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso a jam’iyyar NNPP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Babbar kotun jihar Kano ta soke matakin da kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar NNPP ya dauka na rusa shugabannin jam’iyyar a matakin jiha, kananan hukumomi da mazabu a jihar.
Hukuncin ya zo ne a daidai lokacin da ake rade-radin shirin ficewar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, daga NNPP zuwa APC, da kuma rikicinsa da jagoran jam’iyyar na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso.

Source: Twitter
Sanusi Bature D-Tofa ya wallafa a Facebook cewa mai shari’a Nasiru Saminu ne ya bayar da umarnin, inda ya ayyana matakin NWC na rusa shugabannin NNPP a Kano a matsayin maras inganci a doka.
Kotu ta dauki mataki kan NNPP
A cikin umarnin da ya bayar, mai shari’a Nasiru Saminu ya hana NWC na NNPP daukar duk wani karin mataki da ya shafi tsarin shugabancin jam’iyyar a Kano, har sai an yanke hukunci kan bukatar da aka gabatar a gaban kotu.
Kotun ta kuma umurci dukkan bangarori da su ci gaba da bin matakin da aka yanke tun kafin 30, Disamba, 2025, ranar da aka ce an fitar da umarnin rusa shugabannin jam’iyyar.
Mai shari’ar ya jaddada cewa babu wani kwamitin rikon kwarya da NWC zai nada a Kano, a matakin jiha, kananan hukumomi ko mazabu, har sai an kammala shari’ar da ke gaban kotu.
Bayanin karar da jam'iyyar NNPP ta shigar
Shari’ar mai lamba K/06/2026, Abdullahi Zubairu Imam da wasu mutum biyar ne suka shigar da ita a madadin kwamitin zartarwa na NNPP a kananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Masu karar sun shigar da korafi ne kan jam’iyyar NNPP, suna kalubalantar matakin da NWC ta dauka na rusa shugabannin jam’iyyar a jihar.
Lauyoyin masu kara, K.K. Njidda da S.A. Muhammad, sun gabatar da hujjoji a gaban kotu, lamarin da ya sa kotun ta bayar da umarnin wucin-gadi domin kare halin da ake ciki kafin yanke hukunci na karshe.
Rikici tsakanin Abba da Kwankwaso
A baya, NWC na NNPP ya sanar da rusa shugabannin jam’iyyar a dukkan matakai a Kano, bayan dakatar da Hon. Hashim Dungurawa daga matsayin shugaban jam’iyyar na jihar.
Bayan dakatarwar, an yi wani taro, inda aka tabbatar da nada Abdullahi Abiya a matsayin mukaddashin shugaban jam’iyyar a Kano.

Source: Facebook
Rahotanni sun nuna cewa Dungurawa na daga cikin masu biyayya ga Rabiu Musa Kwankwaso, yayin da Abdullahi Abiya ke da kusanci da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kwankwaso ya taya Abba Kabir murna
A wani labarin, kun ji cewa jagoran NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya taya Abba Kabir Yusuf murnar cika shekara 63 a duniya.
Rabiu Kwankwaso ya tuna yadda ya shafe shekaru yana aiki tare da Abba Kabir a matakai daban-daban a kasa da jihar Kano.
A sakon da ya fitar, jagoran NNPP ya roki Allah ya cigaba da ba Abba Kabir Yusuf hikima wajen daukar matakan da suka dace.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


