Jigo a PDP Ya Hango Yadda Wike zai Ci Amanar Bola Tinubu da APC
- Jigo a PDP mai hamayya, Emmanuel Ogidi, ya zargi APC da bai wa Nyesom Wike kwangilar rusa jam’iyyar adawa
- Ogidi ya ce amma yana da yakinin Wike zai iya juya wa APC baya nan gaba saboda yadda aka ba shi dama
- Ogidi ya yi wannan batu ne bayan rikici ya ɓarke tsakanin Wike da Sakataren APC na ƙasa, Ajibola Basiru, kan batun Ribas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Wani jigon jam’iyyar PDP, Emmanuel Ogidi, ya zargi jam’iyyar APC da ƙarfafa wa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike gwiwa don rusa yan adawa.
Sai dai Ogidi ya bayyana imanin cewa nan ba da jimawa ba Wike zai iya juyawa jam’iyya mai mulki baya tare da yi mata lahani.

Source: Twitter
Channels TV ta wallafa cewa Ogidi ya bayyana haka ne a ranar inda ya ce zai yi wahala a yi sulhu da mutumin da aikinsa kawai ya rusa jam’iyyarku.
Jagora a PDP ya soki Nyesom Wike
Babban 'dan na PDP ya kara da gargadin cewa babu batun sulhu da Nyesom Wike saboda zargin yana son rusa jam'iyya.
Ya ce:
“Ta ya ya za ka yi sulhu da mutane? Ta yaya za ka yi sulhu da mutumin da ke son rushe gidanka? Ka kalli APC yanzu. Bayan duk hayaniyar da ake yi, su ne suka ba shi ƙarfi domin ya yi ƙoƙarin rusa PDP.”
Ogidi ya ƙara da cewa duk abin da Wike ya yi, zai iya dawowa ya shafi APC ɗin kanta, kuma za ta iya samun matsala saboda haka.
A kalamansa:
“Ya riga ya yi abin da ya yi. Yanzu kuma zai iya juya wa kansu."
Yadda Wike ya dagula jam'iyyar PDP
Idan za a iya tunawa Nyesom Wike ya yi aiki da APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda ya mara wa jam’iyyar baya duk da kasancewarsa ɗan PDP a wancan lokaci.
Tsohon gwamnan Jihar Ribas ya bayyana cewa rashin bin dokokin jam’iyya ne ya sa aka fitar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar PDP a zaɓen.

Source: Facebook
Daga bisani, Wike ya samu naɗin Ministan Abuja, lamarin da ya ƙara rikitar da alaƙarsa da jam’iyyun siyasa.
Wike ya hango karshensa a siyasa
A baya, mun wallafa cewa Nyesom Wike, ya ce duk wani yunƙuri na bai wa Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, wa’adi na biyu a 2027 zai jefa siyasar sa cikin mummunan hali.
Wike ya bayyana cewa irin wannan abu zai iya kawo ƙarshen tasirinsa a siyasar jihar Rivers da ma kasa baki ɗaya Saboda haka ya ja daga da duk yunkurin Fubara na sake neman mulki.

Kara karanta wannan
Dalilanmu na son Kwankwaso ya ja Abba zuwa APC inji Hadimin Gwamna Alhajiji Nagoda
Wike ya fadi hakan ne a ranar Asabar, 3 ga watan Disamban 2025, yayin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki na siyasa a wani taro da aka gudanar a karamar hukumar Okrika, a Jihar Rivers
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

